1 Amma Elisha ya ce, “Kasa kunne ga abin da Ubangiji ya ce! Gobe war haka za a sayar da mudu na lallausan gari a bakin shekel guda, da mudu biyu na sha’ir a bakin shekel guda a ƙofar garin Samariya.”
2 Amma dogarin da yake tare da sarki ya ce wa Elisha, “Ko da Ubangiji kansa zai buɗe tagogin sama, wannan abu ba zai yiwu ba.”
Elisha kuwa ya ce, “Za ka gani da idanunka, zai faru, amma ba za ka ci ba.”
Sojan Suriyawa sun Tafi
3 Akwai mutum huɗu, kutare, waɗanda suke zaune a bakin ƙofar gari, sai suka ce wa junansu, “Me ya sa muke zaune nan har mu mutu?
4 Idan mun ce, ‘Bari mu shiga birni,’ yunwa tana birnin, za mu mutu a wurin. Idan kuma mun zauna a nan za mu mutu. Saboda haka bari mu tafi sansanin Suriyawa, idan sun bar mu da rai, za mu rayu, idan kuwa sun kashe mu, za mu mutu.”
5 Sai suka tashi da magariba, suka tafi sansanin Suriyawa. Da suka isa gefen sansanin Suriyawa, sai suka tarar ba kowa a wurin,
6 gama Ubangiji ya sa sojojin Suriyawa suka ji amon karusai, da na dawakai, da na babbar rundunar soja. Sai suka ce wa junansu, “Ai, Sarkin Isra’ila, ya yi ijara da sarakunan Hittiyawa, da na Masarawa, su zo su fāɗa mana.”
7 Saboda haka suka gudu da almuru, suka bar alfarwansu, da dawakansu, da jakunansu, suka bar sansanin yadda yake, suka tsira da rayukansu.
8 Sa’ad da kutaren nan suka zo sansanin, sai suka shiga wata alfarwa, suka ci suka sha. Suka kwashe azurfa, da zinariya, da tufafi, suka tafi suka ɓoye. Suka koma suka shiga wata alfarwa kuma, suka kwashe abubuwan da suke cikinta. Suka tafi suka ɓoye su.
9 Sa’an nan suka ce wa junansu, “Ba mu kyauta ba. Yau ranar albishir ce, idan mun yi shiru, mun jira har safe, wani mugun abu zai same mu. Domin haka bari mu tafi mu faɗa a gidan sarki.”
10 Sai suka tafi wurin masu gadin ƙofar birnin, suka ce musu, “Mun tafi sansanin Suriyawa ba mu ga kowa ba, ba mu kuma ji motsin kowa a wurin ba, ba kowa a wurin sai dawakai da jakai, a ɗaure, alfarwai kuma suna nan yadda suke.”
11 Sa’an nan masu tsaron ƙofar birnin suka aika a faɗa a gidan sarki.
12 Sai sarki ya tashi da dare ya ce wa fādawansa, “Bari in faɗa muku irin shirin da Suriyawa suka yi a kanmu. Sun sani muna fama da yunwa, domin haka suka fita daga sansanin suka ɓuya a karkara, suna nufin sa’ad da muka fita daga birnin, sai su kama mu da rai, sa’an nan su shiga birnin.”
13 Ɗaya daga cikin fādawan sarki ya ce, “A sa waɗansu mutane su ɗauki dawakai biyar da suka ragu cikin birnin, idan ba su tsira ba, za su zama kamar sauran Isra’ilawan da suka riga suka mutu. Bari mu aika, mu gani.”
14 Aka ɗibi mahayan dawakai biyu, sarki kuwa ya aike su, su bi bayan sojojin Suriyawa, ya ce musu, “Ku tafi, ku gani.”
15 Sai suka bi bayansu har zuwa Kogin Urdun, suka ga tufafi da makamai barjat ko’ina a hanya, waɗanda Suriyawa suka zubar lokacin da suke gudu. Sai manzannin suka komo suka faɗa wa sarki.
16 Sa’an nan mutane suka fita, suka washe sansanin Suriyawa. Aka kuwa sayar da mudu na lallausan gari da mudu biyu na sha’ir a bakin shekel ɗaya ɗaya kamar dai yadda Ubangiji ya faɗa.
17 Sarki kuwa ya sa dogari wanda ya raka shi wajen Elisha ya tsare ƙofar birnin. Sai mutane suka tattake shi a ƙofar har ya mutu, kamar yadda annabi Elisha ya faɗa sa’ad da sarki ya tafi wurinsa.
18 Ya faru daidai yadda annabi Elisha ya ce wa sarki, “Za a sayar da mudu biyu na sha’ir, da mudu na lallausan gari a bakin shekel ɗaya ɗaya gobe war haka a ƙofar birnin Samariya.”
19 Dogarin ya ce wa Elisha, “Ko da Ubangiji da kansa zai buɗe tagogin sama, wannan abu zai yiwu ke nan?”
Elisha kuwa ya ce, “Za ka gani da idanunka amma ba za ka ci ba.”
20 Haka kuwa ya zama gama mutane suka tattake shi a ƙofar har ya mutu.