An Mayar da Gonakin Mata daga Shunem
1 Elisha kuwa ya ce wa matar da ya ta da ɗanta daga matattu, “Ki tashi, ke da gidanki, ki zauna duk inda kika samu, gama Ubangiji ya sa a yi yunwa a ƙasar har shekara bakwai.”
2 Sai matar ta tashi, ta yi kamar yadda annabi Elisha ya faɗa mata. Ta tafi, ita da iyalinta suka zauna a ƙasar Filistiyawa har shekara bakwai.
3 A ƙarshen shekara bakwai ɗin, matar ta komo daga ƙasar Filistiyawa, ta tafi wurin sarki, ta roƙe shi a mayar mata da gidanta da gonarta.
4 A lokacin kuwa sarki yana tare da Gehazi, wato baran annabi Elisha, ya ce, “Ka faɗa mini dukan mu’ujizan da Elisha ya yi.”
5 A sa’ad da yake faɗa wa sarki yadda Elisha ya ta da matacce, sai ga matar da ya ta da ɗanta daga matattu, ta zo ta roƙi sarki ya mayar mata da gidanta da gonarta. Sai Gehazi ya ce, “Ran sarki ya daɗe, ai, ga matar, ga kuma yaronta wanda Elisha ya tashe shi daga matattu.”
6 Da sarki ya tambayi matar sai ta faɗa masa dukan labarin. Sarki kuwa ya sa wani bafade ya mayar mata da dukan abin da yake nata da dukan amfanin gonakin, tun daga ran da ta bar ƙasar har ranar da ta komo.
Hazayel Ya Ci Sarautar Suriya
7 Elisha kuwa ya tafi Dimashƙu. A lokacin kuwa Ben-hadad, Sarkin Suriya, yana ciwo. Aka faɗa masa cewa, annabi Elisha ya zo, yana nan,
8 sai sarki ya ce wa Hazayel, ɗaya daga cikin fādawansa, “Ka ɗauki kyauta, ka tafi wurin annabin Allah ka sa ya roƙar mini Ubangiji ko zan warke daga wannan cuta.”
9 Hazayel kuwa ya tafi wurin Elisha tare da kyauta iri iri na kayan Dimashƙu. Raƙuma arba’in ne suka ɗauko kayan. Da ya tafi ya tsaya a gabansa, ya ce, “Danka, Ben-hadad Sarkin Suriyawa, ya aiko ni wurinka don yana so ya ji ko zai warke daga wannan cuta.”
10 Elisha kuwa ya ce masa, “Tafi ka faɗa masa zai warke, amma Ubangiji ya nuna mini lalle zai mutu.”
11 Sai Elisha ya kafa wa Hazayel ido, yana kallonsa, har Hazayel ya ji kunya. Elisha kuwa ya fashe da kuka.
12 Hazayel ya ce, “Me ya sa shugabana yake kuka?”
Elisha ya amsa ya ce, “Domin na san irin muguntar da za ka yi wa jama’ar Isra’ila. Za ka ƙone kagaransu da wuta, ka karkashe samarinsu da takobi, za ka kuma fyaffyaɗe ƙananansu a ƙasa, ka tsattsage matansu masu ciki.”
13 Hazayel kuwa ya ce, “Ni wane ne? Ina na sami wannan iko? Ni ba kome ba ne.”
Elisha ya amsa ya ce, “Ubangiji ya nuna mini za ka zama Sarkin Suriya.”
14 Sa’an nan Hazayel ya tashi daga wurin Elisha ya koma wurin Ben-hadad. Ben-hadad ya tambaye shi, “Me Elisha ya faɗa maka?”
Sai ya ce, “Ya faɗa mini, cewa lalle za ka warke.”
15 Amma kashegari sai Hazayel ya ɗauki bargo, ya tsoma a ruwa, sa’an nan ya rufe fuskar sarki da shi har ya mutu.
Sai ya hau gadon sarautarsa.
Sarki Yehoram na Yahuza
16 A shekara ta biyar ta sarautar Yehoram ɗan Ahab Sarkin Isra’ila, Yoram ɗan Yehoshafat Sarkin Yahuza, ya ci sarauta.
17 Yana da shekara talatin da biyu da haihuwa sa’ad da ya ci sarautar. Ya yi shekara takwas yana sarauta a Urushalima.
18 Ya bi halin sarakunan Isra’ila, kamar yadda gidan Ahab ya yi, gama ya auri ‘yar Ahab. Ya aikata mugun abu a gaban Ubangiji.
19 Duk da haka Ubangiji bai hallaka Yahuza ba, saboda bawansa Dawuda, tun da yake ya alkawarta zai ba shi haske, shi da ‘ya’yansa har abada.
20 A zamanin Yoram, Edomawa suka tayar wa Yahuza, suka naɗa wa kansu sarki.
21 Sa’an nan Yoram ya haye zuwa Zayar tare da dukan karusansa. Sai ya tashi da dare da shugabannin karusansa, ya bugi Edomawan da suka kewaye shi, amma sojojinsa suka gudu zuwa alfarwansu.
22 Haka kuwa Edom ta tayar wa Yahuza har wa yau. A lokacin kuma Libna ta tayar wa Yahuza.
23 Sauran ayyukan Yoram da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
24 Yoram kuwa ya mutu, aka binne shi a makabartar kakanninsa a birnin Dawuda. Ahaziya ɗansa ya gāji sarautarsa.
Sarki Ahaziya na Yahuza
25 A shekara ta goma sha biyu ta sarautar Yehoram ɗan Ahab Sarkin Isra’ila, Ahaziya ɗan Yoram Sarkin Yahuza, ya ci sarauta.
26 Ya ci sarauta yana da shekara ashirin da biyu da haihuwa, ya kuwa yi mulki shekara guda a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Ataliya jikanyar Omri, Sarkin Isra’ila.
27 Ya ɗauki halin gidan Ahab. Ya aikata mugun abu a gaban Ubangiji kamar yadda gidan Ahab ya yi, gama shi surukin gidan Ahab ne.
28 Sarki Ahaziya kuwa ya tafi tare da Yehoram ɗan Ahab don su yi yaƙi da Hazayel, Sarkin Suriya, a Ramot cikin Gileyad. Suriyawa suka yi wa Yehoram rauni.
29 Sai sarki Yehoram ya koma zuwa Yezreyel don ya yi jiyyar raunukan da Suriyawa suka yi masa sa’ad da yake yaƙi da Hazayel Sarkin Suriya. Sai Ahaziya, ɗan Yoram, Sarkin Yahuza ya tafi ya ziyarci Yehoram ɗan Ahab cikin Yezreyel saboda yana ciwo.