Gyare-gyaren da Asa Ya Yi
1 Ruhun Allah kuwa ya sauko a kan Azariya ɗan Oded,
2 sai ya fita ya taryi Asa, ya ce masa, “Ka ji ni, ya Asa, kai da dukan Yahuza da Biliyaminu, Ubangiji yana tare da ku idan kuna tare da shi. Idan kuwa kun neme shi, za ku same shi, amma idan kun rabu da shi, shi ma zai rabu da ku.
3 Isra’ila kuwa ta daɗe ba ta bin Allah na gaskiya, ba ta da firist mai koya mata, ba ta kuma bin shari’a.
4 Amma lokacin da suke shan wahala suka juyo ga Ubangiji Allah na Isra’ila, suka neme shi, suka same shi.
5 A waɗancan lokatai, ba salama ga mai fita ko ga mai shiga, gama babban hargitsi ya wahalar da dukan mazaunan ƙasashe.
6 An kacancana su, al’umma tana gāba da al’umma, birni kuma gāba da birni, gama Allah ya yi ta wahalshe su da kowace irin wahala.
7 Amma ku sai ku yi ƙarfin hali, kada ku firgita, gama za a ba ku ladan aikinku.”
8 Da Asa ya ji irin kalmomin da annabi Azariya ɗan Oded ya hurta, sai ya yi ƙarfin zuciya, ya kawar da gumakan nan masu banƙyama daga dukan ƙasar Yahuza da ta Biliyaminu, daga kuma biranen da ya ci a ƙasar tuddai na Ifraimu. Sa’an nan ya gyara bagaden Ubangiji wanda yake a ƙofar shirayin Haikalin Ubangiji.
9 Sai ya tattara dukan mutanen Yahuza da na Biliyaminu, da kuma na Ifraimu, da na Manassa, da na Saminu, waɗanda suke zaman baƙunci tare da su. Da yawa daga cikin Isra’ilawa suka yi ƙaura zuwa wurinsa, sa’ad da suka ga Ubangiji Allahnsa yana tare da shi.
10 Suka taru a Urushalima a wata na uku na shekara ta goma sha biyar ta sarautar Asa.
11 A ran nan suka miƙa wa Ubangiji hadayun bijimai ɗari bakwai, da tumaki dubu bakwai (7,000) daga cikin ganimar da suka kwaso.
12 Sai suka ƙulla alkawari, cewa za su nemi Ubangiji Allah na kakanninsu da dukan zuciyarsu da ransu.
13 Duk wanda kuma bai nemi Ubangiji, Allah na Isra’ila ba, za a kashe shi, ko yaro ko babba, ko mace ko namiji.
14 Sai suka rantse wa Ubangiji da murya mai ƙarfi, suna sowa, suna busa kakaki da ƙaho.
15 Dukan Yahuza ta yi murna saboda rantsuwar, gama da zuciya ɗaya suka rantse, suka kuwa neme shi da iyakar aniya, sun kuwa same shi. Don haka Allah ya hutasshe su a kowane al’amari.
16 Asa kuma ya tuɓe tsohuwarsa, Ma’aka, daga matsayinta na sarauniya don ta ƙera wata siffa mai banƙyama ta Ashtoret. Sai Asa ya sare siffar nan, ya niƙe ta, ya ƙone a rafin Kidron.
17 Amma ba a kawar da masujadan da yake Isra’ila ba, duk da haka zuciyar Asa sarai take, ba wani aibi duk kwanakinsa.
18 Sai ya shigar da sadakar da shi da tsohonsa suka keɓe don Haikalin Ubangiji, wato azurfa, da zinariya, da kwanoni da tasoshi, da finjalai iri iri.
19 Ba a kuma ƙara yin wani yaƙi ba har shekara ta talatin da biyar ta mulkinsa Asa.