Asa ya Haɗa Kai da Ben-hadad
1 A shekara ta talatin da shida ta mulkin Asa, sai Ba’asha, Sarkin Isra’ila, ya haura ya fāɗa wa Yahuza da yaƙi, ya gina Rama don ya hana kowa fita, ko shiga wurin Asa, Sarkin Yahuza.
2 Sa’an nan Asa ya ɗebo azurfa da zinariya daga dukiyar da take cikin Haikalin, da na fādar sarki, ya aika wa Ben-hadad da su, wato Sarkin Suriya, wanda yake zaune a Dimashƙu, yana cewa,
3 “Bari mu haɗa kai, da ni da kai kamar yadda ubana da naka suka yi. Ga shi, na aika maka da azurfa da zinariya. Ka tafi ka warware haɗa kan da yake tsakaninka da Ba’asha, Sarkin Isra’ila, don ya janye ya rabu da ni.”
4 Ben-hadad kuwa ya kasa kunne ga sarki Asa, ya aika da shugabannin rundunan sojojinsa suka yi yaƙi da biranen Isra’ila. Suka ci Iyon, da Dan, da Abel-bet-ma’aka, da dukan biranen ajiya na Naftali.
5 Da Ba’asha ya ji haka, sai ya daina gina Rama, ya bar aikin da yake yi.
6 Sa’an nan sarki Asa ya kawo dukan mutanen Yahuza, suka kwashe duwatsun da katakan da Ba’asha yake gina Rama da su, ya gina Geba da Mizfa da su.
Annabi Hanani
7 A lokacin nan sai Hanani, maigani, ya zo wurin Asa, Sarkin Yahuza, ya ce masa, “Da yake ka dogara ga Sarkin Suriya, maimakon ka dogara ga Ubangiji Allahnka, shi ya sa rundunar sojojin Sarkin Suriya ta kuɓuta daga hannunka.
8 Ai, Habashawa da Libiyawa rundunar sojoji ne masu yawan gaske, suna kuma da karusai da mahayan dawakai masu yawa ƙwarai. Amma duk da haka, saboda ka dogara ga Ubangiji, sai ya bashe su a hannunka.
9 Idon Ubangiji fa, yana kai da komowa ko’ina a duniya don ya nuna ikonsa ga dukan waɗanda suka dogara gare shi da zuciya ɗaya. Ka yi wauta a cikin wannan al’amari. Tun daga yanzu har zuwa nan gaba za ka yi ta fama da yaƙoƙi.”
10 Sai Asa ya yi fushi da maiganin, ya sa shi a kurkuku saboda maganar da ya yi masa, gama ya husata da shi ƙwarai. A wannan lokaci kuma sai Asa ya ƙuntata wa waɗansu daga cikin jama’a.
Ƙarshen Mulkin Asa
11 Ayyukan Asa, daga farko har zuwa ƙarshe, an rubuta su a littafin sarakunan Yahuza da na Isra’ila.
12 A shekara ta talatin da tara ta mulkin Asa, sai wani ciwo ya kama shi a ƙafa. Ciwon kuwa ya tsananta ƙwarai, duk da haka Asa bai nemi taimakon Ubangiji ba, sai na magori.
13 Asa fa ya rasu bayan shekara biyu da ciwon, a shekara ta arba’in da ɗaya ta mulkinsa.
14 Aka binne shi a kabarin da shi da kansa ya haƙa a birnin Dawuda. Aka sa shi a makara wadda aka cika da kayan ƙanshi da na turare yadda gwanayen aikin turare suka shirya, suka hura babbar wuta don su darajanta shi.