Annabi Yehu Ya Tsauta wa Yehoshafat
1 Yehoshafat Sarkin Yahuza ya koma gidansa a Urushalima lafiya.
2 Sai Yehu maigani, ɗan Hanani, ya fita domin ya tarye shi, ya ce wa sarki Yehoshafat, “Za ka taimaki mugu ka kuma ƙaunaci maƙiyan Ubangiji? Saboda haka hasalar Ubangiji za ta same ka.
3 Duk da haka an sami wani abin kirki a wurinka, gama ka kawar da gumakan Ashtarot daga ƙasar, ka sa zuciyarka ga neman Allah.”
Yehoshafat Ya Zaɓi Alƙalai
4 Yehoshafat ya yi zamansa a Urushalima, ya sāke shiga jama’a, tun daga Biyer-sheba har zuwa ƙasar tuddai ta Ifraimu, ya komar da su zuwa wurin Ubangiji, Allah na kakanninsu.
5 Sai ya naɗa alƙalai a ƙasar, a dukan biranen Yahuza masu kagara, birni birni.
6 Sai ya ce wa alƙalan, “Ku lura da abin da kuke yi, gama shari’ar da kuke yi ba ta mutum ba ce, amma ta Ubangiji ce, yana tare da ku sa’ad da kuke yanke shari’a.
7 Yanzu fa ku yi tsoron Ubangiji. Ku lura da abin da kuke yi, gama Ubangiji Allahnmu bai yarda da rashin yin adalci ba, ko son zuciya, ko karɓar rashawa.”
8 Yehoshafat kuma ya naɗa waɗansu Lawiyawa, da firistoci, da waɗansu shugabannin iyalan Isra’ilawa, saboda su yi shari’a tsakani da Ubangiji, su daidaita tsakanin masu jayayya. A Urushalima za su zauna.
9 Sai ya umarce su ya ce, “Haka za ku yi saboda tsoron Ubangiji, ku yi aminci, ku yi da zuciya ɗaya kuma.
10 A duk lokacin da ‘yan’uwanku daga birane suka kawo muku maganar wata shari’a, wadda ta shafi zub da jini, ko karya shari’a, ko umarni, ko dokoki, ko farillai, sai ku koya musu, don kada su aikata laifi a gaban Ubangiji, don kada hasala ta same ku, ku da ‘yan’uwanku. Abin da za ku yi ke nan, don kada ku yi laifi.
11 Amariya, babban firist, shi ne zai shugabance ku a kan dukan al’amuran da suke na wajen Ubangiji. Zabadiya, ɗan Isma’ilu mai mulkin gidan Yahuza, shi ne shugabanku a kan dukan al’amuran da suke na wajen sarki. Lawiyawa kuwa su zama muhimman ma’aikatanku. Kada ku ji tsoro a cikin aikinku, Ubangiji kuwa ya kasance tare da masu gaskiya.”