Yaƙi da Mowab, da Ammon, da Edom
1 Bayan wannan sai mutanen Mowab, da mutanen Ammon, tare da waɗansu daga cikin Me’uniyawa, suka zo su yi yaƙi da Yehoshafat.
2 Sai waɗansu mutane suka zo suka faɗa wa Yehoshafat cewa, “Mutane masu yawan gaske suna zuwa su yi yaƙi da kai daga Edom, da kuma teku, har sun iso Hazazon-tamar,” wato En-gedi.
3 Sai Yehoshafat ya ji tsoro ya himmatu ga neman Ubangiji, ya kuma sa a yi shela, a yi azumi a dukan Yahuza.
4 Yahuza suka tattaru don su nemi taimako daga wurin Ubangiji. Daga cikin dukan biranen Yahuza, mutane suka zo don su nemi Ubangiji.
5 Sai Yehoshafat ya tsaya a gaban taron jama’ar Yahuza da na Urushalima, a Haikalin Ubangiji, a gaban sabuwar farfajiya,
6 ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na kakanninmu, kai ne Allah na cikin Sama, kai ne kuma kake mulkin dukan al’umman duniya. A gare ka iko da ƙarfi suke, don haka ba wanda ya isa ya jā da kai.
7 Ya Allahnmu, kai ne ka kori jama’ar ƙasan nan a gaban jama’arka Isra’ila, ka kuma ba da ita har abada ga zuriya masoyinka Ibrahim.
8 Suka kuwa zauna a cikinta, suka gina Wuri Mai Tsarki saboda sunanka cewa,
9 ‘Idan wani mugun abu ya same mu, kamar takobi, ko hukunci, ko annoba, ko yunwa, to, za mu tsaya a gaban wannan gida, a gabanka kuma, gama sunanka yana cikin gidan nan, idan mun yi maka kuka saboda wahalarmu, kai kuwa za ka ji, ka cece mu.’
10 “Yanzu kuma ga mutanen Ammon, da na Mowab, da na Dutsen Seyir, waɗanda ka hana Isra’ilawa su kai musu yaƙi sa’ad da suka fito daga ƙasar Masar, su ne mutanen da Isra’ila suka ƙyale, ba su hallaka su ba.
11 Dubi irin sakayyar da suka zo su yi mana, so suke su kore mu daga mallakarka, wanda ka gādar mana.
12 Ya Allahnmu, ba za ka hukunta su ba? Ba mu da ƙarfin da za mu yi yaƙi da wannan babban taro da suke zuwa su yi yaƙi da mu. Mun rasa abin da za mu yi, amma a gare ka muke zuba ido.”
13 A sa’an nan kuwa mutanen Yahuza suna tsaye a gaban Ubangiji, su da ƙananansu, da matansu, da ‘ya’yansu.
14 A tsakiyar taron sai Ruhun Ubangiji ya sauka a kan Yahaziyel ɗan Zakariya, ɗan Benaiya, ɗan Yehiyel, ɗan Mattaniya, Balawe, na ‘ya’yan Asaf, maza.
15 Sai Yahaziyel ya ce, “Ku ji, ku dukanku, mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima, da sarki Yehoshafat, ga abin da Ubangiji yake faɗa muku, ‘Kada ku ji tsoro, ko ku razana saboda wannan babban taro, gama wannan yaƙi ba naku ba ne, amma na Allah ne.
16 Ku gangara ku fāɗa musu gobe. Ga shi kuwa, za su haura ta hawan Ziz, za ku tarar da su a ƙarshen kwarin a gabashin jejin Yeruyel.
17 Ba ku za ku yi wannan yaƙi ba, ku dai, ku jā dāga, ku tsaya kurum ku ga nasarar da Ubangiji zai ciwo muku, ya Yahuza da Urushalima. Kada ku ji tsoro ko ku razana, gobe ku fita ku tsaya gāba da su, gama Ubangiji yana tare da ku.’ ”
18 Yehoshafat fa ya sunkuyar da kansa ƙasa, dukan Yahuza da mazaunan Urushalima kuma suka fāɗi ƙasa a gaban Ubangiji, suna masa sujada.
19 Sai Lawiyawa daga Kohatawa da Koratiyawa suka tashi tsaye suka yabi Ubangiji Allah na Isra’ila da babbar murya.
20 Sai suka tashi da sassafe suka tafi jejin Tekowa. Sa’ad da suka fita sai Yehoshafat ya tsaya, ya ce, “Ku saurara gare ni, ku mutanen Yahuza da mazaunan Urushalima. Ku gaskata da Ubangiji Allahnku, za ku kahu. Ku gaskata annabawansa, za ku ci nasara.”
21 Sa’ad da ya yi shawara da jama’a, sai ya zaɓi waɗanda za su raira waƙa ga Ubangiji, su yabe shi a natse sa’ad da suke tafe a gaban runduna, su ce,
“Ku yi godiya ga Ubangiji,
Saboda madawwamiyar ƙaunarsa
Tabbatacciya ce har abada.”
22 Sa’ad da suka fara raira waƙa, suna yabo, sai Ubangiji ya sa wa mutanen Ammon, da na Mowab, da na Dutsen Seyir, ‘yan kwanto, ‘yan kwanton kuwa suka fatattake su.
23 Gama mutanen Ammon da na Mowab suka tasar wa mazaunan Dutsen Seyir, suka hallaka su ƙaƙaf. Sa’ad da suka karkashe mazaunan Seyir sai suka fāɗa wa juna, suka yi ta hallaka kansu da kansu.
24 Da mutanen Yahuza suka zo hasumiyar tsaro ta jeji, suka duba sai suka ga gawawwaki kawai a kwance, ba wanda ya tsira.
25 Sa’ad da Yehoshafat da jama’arsa suka je kwasar ganima, sai suka sami shanu masu yawan gaske, da kayayyaki, da tufafi, da abubuwa masu daraja, waɗanda suka yi ta kwasa har suka gaji. Kwana uku suka yi suna ta kwasar ganimar saboda yawanta.
26 Sai suka taru a kwarin Beraka, wato albarka, a rana ta huɗu, a nan suka yabi Ubangiji. Don haka har wa yau ake kiran wurin, “Kwarin Beraka.”
27 Sai kowane mutumin Yahuza da na Urushalima, tare da Yehoshafat shugabansu, suka koma Urushalima suna murna, gama Ubangiji ya sa su yi farin ciki saboda maƙiyansu.
28 Suka shigo Urushalima da molaye da garayu, da ƙaho zuwa Haikalin Ubangiji.
29 Tsoron Ubangiji kuwa ya kama dukan mulkokin ƙasashe sa’ad da suka ji Ubangiji ya yi yaƙi da maƙiyan Isra’ilawa.
30 Mulkin Yehoshafat kuwa ya sami salama, gama Allahnsa ya ba shi hutawa a kowane gefe.
Ƙarshen Mulkin Yehoshafat
31 Yehoshafat ya yi mulkin Yahuza. Yana da shekara talatin da biyar sa’ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki a Urushalima shekara ashirin da biyar. Sunan tsohuwarsa Azuba, ‘yar Shilhi.
32 Ya bi tafarkin tsohonsa, Asa, bai kuwa kauce ba, ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji.
33 Duk da haka ba a kawar da masujadai ba, domin har yanzu mutanen ba su tsayar da zukatansu ga Allahn kakanninsu ba.
34 Sauran ayyukan Yehoshafat, daga farko zuwa ƙarshe, an rubuta su a littafin tarihin Yehu ɗan Hanani, wanda aka rubuta a littafin sarakunan Isra’ila.
35 Bayan haka sai Yehoshafat, Sarkin Yahuza, ya haɗa kai da Ahaziya Sarkin Isra’ila, wanda ya aikata mugunta.
36 Ya haɗa kai da shi, suka gina jiragen ruwa don su riƙa zuwa Tarshish. A Eziyon-geber suka gina jiragen ruwan.
37 Sai Eliyezer ɗan Dodawahu mutumin Maresha, ya yi annabci gāba da Yehoshafat, ya ce, “Saboda ka haɗa kanka da Ahaziya, Ubangiji zai hallaka abin da ka yi.” Don haka jiragen ruwa suka farfashe, suka kāsa tafiya Tarshish.