Sarki Yowash na Yahuza
1 Yowash yana da shekara bakwai sa’ad da ya ci sarauta, ya kuwa yi shekara arba’in yana mulki a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Zibiya, daga Biyer-sheba.
2 Yowash ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji a dukan zamanin Yehoyada firist.
3 Sai Yehoyada ya auro masa mata biyu, ya haifi ‘ya’ya mata da maza.
4 Bayan wannan sai Yowash ya yi niyya ya gyara Haikalin Ubangiji.
5 Sai ya tattara firistoci da Lawiyawa, ya ce musu, “Ku shiga biranen Yahuza, ku tattara kuɗi daga dukan Isra’ilawa domin a riƙa gyaran Haikalin Ubangijinku kowace shekara. Ku hanzarta al’amarin fa.” Amma Lawiyawa ba su hanzarta ba.
6 Sai sarki ya kira Yehoyada babban firist, ya ce masa, “Don me ba ka sa Lawiyawa su tafi Yahuza, da Urushalima, su karɓo kuɗin da Musa, bawan Ubangiji, ya aza wa taron jama’ar Isra’ila su kawo domin alfarwar sujada ba?”
7 Gama ‘ya’ya maza na Ataliya, muguwar matan nan, sun kutsa kai a cikin Haikalin Ubangiji, suka yi amfani da dukan tsarkakan kayayyakin Haikalin Ubangiji domin gumaka.
8 Don haka sai sarki ya ba da umarni, a yi babban akwati, a ajiye shi a waje a ƙofar Haikalin Ubangiji.
9 Sai aka yi shela a Yahuza da Urushalima, a kawo wa Ubangiji kuɗin da Musa, bawan Allah, ya aza wa Isra’ila sa’ad da suke cikin jeji.
10 Sai dukan sarakuna, da dukan jama’a, suka yi farin ciki, suka kawo kuɗin da aka aza musu, suka zuba a babban akwatin, har ya cika.
11 Duk lokacin da Lawiyawa suka kawo wa ‘yan majalisar sarki babban akwatin sa’ad da suka gan shi cike da kuɗi, sai magatakardan sarki, da na’ibin babban firist, su zo su juye kuɗin da suke cikin babban akwatin, sa’an nan su mayar da shi a inda yake. Haka suka yi ta yi kullum, har suka tara kuɗi masu yawan gaske.
12 Sarki kuwa da Yehoyada suka ba da kuɗin ga waɗanda suke lura da aikin Haikalin Ubangiji. Suka sa magina, da masassaƙa su gyara Haikalin Ubangiji, suka kuma sa masu aikin baƙin ƙarfe da na tagulla su gyara Haikalin Ubangiji.
13 Sai ma’aikatan da aka sa su yi aikin, suka yi aiki sosai, suka tafiyar da gyaran, suka gyara Haikalin Ubangiji, ƙarfinsa ya koma kamar yadda yake dā.
14 Da suka gama aikin, sai suka kawo wa sarki da Yehoyada sauran kuɗin. Da waɗannan kuɗin aka yi tasoshi, da kayan girke-girke na Haikalin Ubangiji, da kuma kayan hidima da miƙa hadayu na ƙonawa, da tasoshi domin turare, da kwanoni na zinariya da na azurfa.
An sāke Shirin Yehoyada
Suka yi ta miƙa hadayu na ƙonawa a cikin Haikalin Ubangiji, dukan kwanakin Yehoyada.
15 Yehoyada kuwa ya tsufa ƙwarai, ya yi tsawon rai, ya rasu. Ya rasu yana da shekara ɗari da talatin da haihuwa.
16 Suka binne shi a birnin Dawuda a inda ake binne sarakuna, saboda ya aikata nagarta a Isra’ila, da kuma a gaban Allah da Haikalin Allah.
17 Bayan rasuwar Yehoyada, sai sarakunan Yahuza suka zo suka yi mubaya’a a gaban sarki, sarki kuwa ya karɓa.
18 Sai suka ƙyale Haikalin Ubangiji Allah na kakanninsu, suka bauta wa Ashtarot da gumaka. Hasala kuwa ta auko a kan Yahuza da Urushalima, saboda wannan mugunta da suka yi.
19 Duk da haka Allah ya aika musu da annabawa don su komo da su wurinsa. Ko da yake sun shaida musu kuskurensu, duk da haka ba su kula ba.
20 Sai Ruhun Allah ya sauko wa Zakariya, ɗan Yehoyada, firist, ya tsaya a gaban jama’a ya yi magana da su, ya ce, “Ga abin da Allah ya ce, ‘Don me kuke ƙetare umarnan Ubangiji, har da za ku rasa albarka? Saboda kun rabu da bin Ubangiji, shi ma ya rabu da ku.’ ”
21 Amma suka yi masa maƙarƙashiya, sarki kuma ya ba da umarni, suka jejjefi annabin da duwatsu har ya mutu a farfajiyar Haikalin Ubangiji.
22 Sarki Yowash bai tuna da irin alherin da Yehoyada mahaifin Zakariya ya yi masa ba, amma ya kashe ɗansa. Sa’ad da Zakariya yake bakin mutuwa, sai ya ce, “Bari Ubangiji ya gani ya kuma sāka.”
23 A ƙarshen shekara sai sojojin Suriyawa suka kawo wa Yowash yaƙi suka je Yahuza da Urushalima, suka hallaka dukan shugabannin jama’a, suka kwashi ganima mai yawa, suka aika wa Sarkin Dimashƙu.
24 Ko da yake mutanen Suriya kima ne, duk da haka Ubangiji ya sa suka ci nasara a kan babbar rundunar Yowash, saboda sun rabu da Ubangiji Allah na kakanninsu. Ta haka suka hukunta wa Yowash.
25 Sa’ad da suka tafi, sun bar shi da rauni mai tsanani ƙwarai, sai barorinsa suka yi masa maƙarƙashiya suka kashe shi a gadonsa, saboda ya kashe ɗan Yehoyada firist. Ya mutu, aka binne shi a birnin Dawuda, amma ba su binne shi a kabarin sarakuna ba.
26 Waɗannan su ne waɗanda suka yi masa maƙarƙashiyar, Yozakar ɗan Shimeyat wata Ba’ammoniya, da Yehozabad ɗan Shimrit wata mutuniyar Mowab.
27 Labarin ‘ya’yansa maza da annabcin da aka kawo a kansa da labarin sāke ginin Haikalin Allah, an rubuta su a sharhin littafin sarakunan. Sai Amaziya ɗan Yowash ya gāji gadon sarautarsa.