Shirin Hezekiya domin Firistoci da Lawiyawa
1 Sa’ad da aka gama duka, sai dukan Isra’ilawa da suka hallara, suka bi cikin biranen Yahuza, suka farfashe al’amudan, suka ragargaza Ashtarot, suka farfashe masujadai da bagadai duka da suke a Yahuza da Biliyaminu, da na Ifraimu da Manassa har suka hallakar da su duka. Sa’an nan dukan jama’ar Isra’ila suka koma garuruwansu, ko wanne zuwa mahallinsa.
2 Hezekiya kuma ya raba firistoci da Lawiyawa kashi kashi, ko wanne da hidimarsa, firistoci da Lawiyawa, don hadayu na ƙonawa da na salama, su yi hidima a ƙofofin Ubangiji, don su yi godiya da yabo.
3 Daga dukiyarsa kuma ya ba da taimako na abin yin hadayun ƙonawa, wato hadayun ƙonawa na safe da na maraice, da hadayun ƙonawa na ranakun Asabar, da na amaryar wata, da na ƙayyadaddun idodi, kamar yadda aka rubuta a Attaura ta Ubangiji.
4 Hezekiya ya kuma umarci jama’ar da suke zaune a Urushalima su riƙa ba da rabon firistoci da na Lawiyawa, domin su mai da hankali ga dokar Ubangiji.
5 Nan da nan da aka baza labarin umarnin ko’ina, sai jama’ar Isra’ila suka ba da nunan fari na hatsinsu, da ruwan inabi, da mai, da zuma, da amfanin gona duka, suka kuma kawo zaka mai yawa ta kowane irin abu.
6 Jama’ar Isra’ila da na Yahuza waɗanda suke zaune a garuruwan Yahuza, su ma sun kawo tasu zaka ta shanu, da ta tumaki, da ta abubuwan da aka keɓe aka kuma tsarkake domin Ubangiji Allahnsu, suka tara su tsibi tsibi.
7 A wata na uku ne suka fara tattara tsibi tsibin, suka gama a wata na bakwai.
8 Sa’ad da Hezekiya da sarakuna suka zo suka ga tsibi tsibin, sai suka yabi Ubangiji da jama’arsa Isra’ila.
9 Hezekiya kuma ya yi wa firistoci da Lawiyawa tambaya a kan tsibi tsibin.
10 Sai Azariya, babban firist na gidan Zadok, ya amsa masa, ya ce, “Tun lokacin da suka fara kawo sadakarsu a Haikalin Ubangiji, mun ci mun ƙoshi, abin da ya ragu kuwa yana da yawa, gama Ubangiji ya sa wa jama’arsa albarka, saboda haka abin da ya ragu a rumbu yana da yawa.”
11 Sai Hezekiya ya umarce su su shirya ɗakuna a Haikalin Ubangiji, suka kuwa shirya.
12 Da aminci suka kawo sadakokinsu, ta zaka da ta keɓaɓɓun abubuwa. Babban shugaban da yake lura da su kuwa, shi ne Konaniya, Balawe, da Shimai ɗan’uwansa, shi ne na biyu,
13 sa’an nan da Yehiyel, da Azaziya, da Nahat, da Asahel, da Yerimot, da Yozabad, da Eliyel, da Ismakiya, da Mahat, da Benaiya su ne shugabanni, mataimakan Konaniya da Shimai waɗanda sarki Hezekiya da Azariya babban shugaban Haikalin Allah suka naɗa.
14 Kore kuwa ɗan Imna Balawe, mai tsaron ƙofar gabas, yake lura da hadayu na yardar rai ga Allah, don ya karkasa bayarwar da aka keɓe domin Ubangiji da hadayu mafi tsarki.
15 Eden, da Miniyamin, da Yeshuwa, da Shemaiya, da Amariya, da Shekaniya suna taimakonsa da zuciya ɗaya a biranen firistoci, don su rarraba wa ‘yan’uwansu rabonsu, tsofaffi da yara, duka ɗaya ne, bisa ga ƙungiyoyinsu,
16 da su kuma waɗanda aka rubuta bisa ga asali, ‘yan samari masu shekara uku zuwa sama, duk dai waɗanda za su shiga Haikalin Ubangiji don yin hidima, kamar yadda aka tsara, bisa ga matsayinsu yadda aka karkasa su.
17 Aka kuma rubuta firistoci bisa ga gidajen kakanninsu, na wajen Lawiyawa kuwa, tun daga mai shekara ashirin zuwa sama, bisa ga matsayinsu, ta yadda aka karkasa su.
18 Aka rubuta firistoci tare da dukan ƙananan ‘ya’yansu, da matansu, da ‘ya’yansu mata da maza, dukansu gaba ɗaya, gama da zuciya ɗaya suka tsarkake kansu.
19 Akwai mutane a garuruwa da yawa waɗanda aka sa don su rarraba wa ‘ya’yan Haruna, firist, maza kuwa, waɗanda suke zaune a gonaki na ƙasar garuruwansu su ba kowane namiji da aka rubuta na Lawiyawa, nasa rabo.
20 Haka kuwa Hezekiya ya yi a dukan Yahuza, ya aikata abin da yake daidai, da aminci, a gaban Ubangiji Allahnsa.
21 Kowane irin aiki da ya kama na hidimar Haikalin Allah, wanda yake kuma bisa ga doka da umarni, na neman Allahnsa, ya yi su da zuciya ɗaya, ya kuwa arzuta.