1 Sulemanu ya kammala dukan aikin Haikalin Ubangiji. Sa’an nan ya kawo kayayyakin da tsohonsa Dawuda ya riga ya keɓe, wato azurfa da zinariya, da dukan kayan girke-girke, da tasoshi, ya ajiye su a taskokin Haikalin Allah.
Sulemanu Ya Kawo Akwatin Alkawari a Haikali
2 Sulemanu kuwa ya tattara dattawan Isra’ila, da shugabannin kabilai, da shugabannin gidajen kakannin jama’ar Isra’ila, a Urushalima, domin a yi bikin fito da akwatin alkawari na Ubangiji da yake a alfarwa a birnin Dawuda, wato Sihiyona.
3 Sai dukan mutanen Isra’ila suka hallara a gaban sarki, a wurin bikin, a wata na bakwai ke nan.
4 Sa’an nan dukan dattawan Isra’ila suka zo, Lawiyawa kuwa suka ɗauko akwatin.
5 Suka kuma kawo akwatin, da alfarwa ta taruwa, da dukan tsarkakakkun kayayyakin da suke cikin alfarwar. Lawiyawa da firistoci ne suka kawo su.
6 Sarki Sulemanu da dukan taron mutanen Isra’ila waɗanda suka hallara a gaban akwatin suka yi ta miƙa hadayun tumaki da bijimai masu yawan gaske, har ba su ƙidayuwa.
7 Sa’an nan firistoci suka shigar da akwatin alkawari na Ubangiji a wurinsa, wato a Wuri Mafi Tsarki na cikin Haikalin, a ƙarƙashin fikafikan kerubobi.
8 Gama kerubobin sun miƙe fikafikansu bisa a daidai wurin da akwatin yake, wato kerubobin sun yi wa akwatin da sandunansa kamar rumfa ke nan.
9 Sandunan akwatin dogaye ne ƙwarai, har ana ganin kawunansu a gaban Wuri Mafi Tsarki na can ciki. Amma daga waje ba a iya ganinsu. Suna a wannan wuri har yau.
10 Ba kome cikin akwatin sai alluna biyu waɗanda Musa ya sa a ciki sa’ad da suke a Horeb. A Horeb ne Ubangiji ya ƙulla alkawarin da mutanen Isra’ila, sa’ad da suka fito daga Masar.
Ɗaukakar Ubangiji
11 Firistocin suka fito daga Wuri Mai Tsarki na Haikalin Allah, gama dukan firistocin da suka hallara, sun tsarkake kansu ba tare da kula da bambancin matsayi ba.
12 Dukan Lawiyawa mawaƙa, wato su Asaf, da Heman, da Yedutun tare da ‘ya’yansu maza da ‘yan’uwansu, aka sa su su tsaya a gabashin bagade, suna sāye da lilin mai kyau, suna ta kaɗa kuge, da molaye da garayu, ga kuma firistoci ɗari da ashirin masu busa ƙaho tare da su.
13 Ya zama aikin mabusan ƙaho ne, da mawaƙa duka, su haɗa kai, har a ji su suna yabon Ubangiji, suna godiya, sa’ad da suka ɗaga waƙa daidai da muryar ƙaho da ta kuge, da dukan kayan bushe-bushe suka yi ta raira waƙa cewa,
“Yabo ya tabbata ga Ubangiji
Gama shi nagari ne,
Ƙaunarsa kuwa madawwamiya ce.”
Gidan kuwa, wato Haikalin Ubangiji, ya cika da girgije,
14 har ma firistoci ba su iya tsayawa su ci gaba da hidima ba saboda girgijen, gama ɗaukakar Ubangiji ta cika Haikalin Allah.