AYU 1

Shaiɗan Ya Jarraba Ayuba

1 Akwai wani mutum a ƙasar Uz, mai suna Ayuba, amintacce ne, mai tsoron Allah. Shi mutumin kirki ne, natsattse, yana ƙin aikata kowace irin mugunta.

2 Yana da ‘ya’ya bakwai maza, uku mata.

3 Yana da tumaki dubu bakwai (7,000), da raƙuma dubu uku (3,000), da shanu dubu guda (1,000), da jakuna ɗari biyar. Yana kuma da barori masu yawan gaske, don haka ya fi kowa a ƙasar gabas arziki nesa.

4 ‘Ya’yansa maza sukan yi liyafa bi da bi a gidajen junansu, inda su duka sukan taru koyaushe, sukan gayyaci ‘yan’uwan nan nasu mata su halarci liyafar.

5 A kowane lokacin da aka gama da liyafar, Ayuba yakan tashi da sassafe, kashegarin liyafar, yă miƙa hadayu don yă tsarkake ‘ya’yansa. Haka yake yi kullum, don yana zaton mai yiwuwa ne ɗaya daga cikin ‘ya’yan ya yi zunubi, ya saɓi Allah a ɓoye.

6 Sa’ad da ranar da talikan sama masu rai sukan hallara gaban Ubangiji ta yi, Shaiɗan ma ya zo tare da su.

7 Sai Ubangiji ya tambaye shi, ya ce, “Kai fa me kake yi?”

Shaiɗan ya amsa, ya ce, “Ina ta kaiwa da kawowa ne, a ko’ina a duniya.”

8 Ubangiji ya ce masa, “Ko ka lura da bawana Ayuba? Ba wani mutumin kirki, mai aminci, kamarsa a duniya. Yana yi mini sujada, natsattse ne, yana ƙin aikata kowace irin mugunta.”

9 Shaiɗan ya amsa, ya ce, “A banza Ayuba yake yi maka sujada?

10 Ai, don ka kiyaye shi ne, shi da iyalinsa, da dukan abin da yake da shi. Ka kuma sa wa duk abin da yake yi albarka, ka kuwa ba shi shanun da suka isa su cika dukan ƙasan nan.

11 Amma da a ce za ka raba shi da dukan abin hannunsa, to, da zai fito fili yă zage ka ƙiri ƙiri.”

12 Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “To, shi ke nan, dukan abin hannunsa yana cikin ikonka, amma shi kansa kada ka cuce shi.” Sai Shaiɗan ya tafi.

An Hallaka ‘Ya’yan Ayuba da Dukiyarsa

13 Wata rana ‘ya’yan Ayuba suna shagali a gidan wansu,

14 sai ga jakada ya zo wurin Ayuba a guje, ya ce, “Muna huɗar gona da shanu, jakuna suna kiwo a makiyayar da suke kusa da wurin,

15 sai Sabiyawa suka auka musu farat ɗaya, suka sace su duka, suka kuma karkashe duk barorinka, sai ni kaɗai na tsira, na zo in faɗa maka.”

16 Kafin yă gama magana, sai wani bara ya zo, ya ce, “Tsawa ta kashe tumaki da makiyayansu duka, ni kaɗai na tsira, na zo in faɗa maka.”

17 Kafin yă gama magana, sai wani bara ya zo, ya ce, “Ƙungiyoyin mahara uku na Kaldiyawa suka auka mana, suka kwashe raƙuma duka, suka kuma karkashe barorinka duka, sai ni kaɗai na tsira, na zo in faɗa maka.”

18 Kafin yă gama magana, sai wani bara ya zo, ya ce, “Sa’ad da ‘ya’yanka suke liyafa a gidan wansu,

19 sai hadiri ya taso daga hamada, ya rushe gidan, ya kashe ‘ya’yanka duka, ni kaɗai na tsira na zo in faɗa maka.”

20 Sai Ayuba ya tashi, ya kyakkece tufafinsa don baƙin ciki. Ya aske kansa, ya fāɗi ƙasa,

21 ya ce, “Ban shigo duniya da kome ba, ba kuma zan fita cikinta da kome ba. Ubangiji ya bayar, shi ne kuma ya karɓe, yabo ya tabbata ga sunansa.”

22 Ko da yake waɗannan al’amura duka sun faru, duk da haka Ayuba bai sa wa Allah laifi ba.