Ayuba Ya Yi Tunani a kan Rashin Tsawon Rai
1 “Mutum duka kwanakin ransa gajere ne, kwanakin wahala kuwa.
2 Sukan yi girma su bushe nan da nan kamar furanni,
Sukan shuɗe kamar inuwa.
3 Na ma isa ka dube ni ne, ya Allah?
Ko ka gabatar da ni a gabanka,
Ka yi mini shari’a?
4 Ba wani abu tsarkakakke
Da zai fito daga cikin kowane marar tsarki, kamar mutum.
5 Tsawon kwanakin ransa, an ƙayyade su tun can,
An ƙayyade yawan watannin da zai yi,
Ka riga ka yanke haka ya Allah, ba su sākuwa.
6 Ka kawar da fuska daga gare shi, ka rabu da shi,
Ka bar shi ya ji daɗin kwanakinsa na fama da aiki idan zai iya.
7 “Akwai sa zuciya ga itacen da aka sare,
Yana iya sāke rayuwa ya yi toho.
8 Ko da yake saiwoyinsa sun tsufa,
Kututturensa kuma ya ruɓe a ƙasa,
9 In aka zuba ruwa, sai ya toho kamar sabon tsiro.
10 Amma ɗan mutum ya mutu, ƙarshensa ke nan,
Ya mutu, a ina yake a lokacin nan?
11 “Mai yiwuwa ne koguna za su daina gudu,
Har tekuna kuma su ƙafe.
12 Amma matattu ba za su tashi ba daɗai,
Ba za su ƙara tashi ba sam, muddin sararin sama na nan.
Sam, ba za a dame su cikin barcinsu ba.
13 “Ya Allah, da ma a ce ka ɓoye ni a lahira,
Ka bar ni a ɓoye, har fushinka ya huce,
Sa’an nan ka sa lokacin da za ka tuna da ni!
14 Idan mutum ya mutu, zai sāke rayuwa kuma?
Amma zan jira lokaci mafi kyau,
In jira sai lokacin wahala ya wuce.
15 Sa’an nan za ka yi kira, ni kuwa zan amsa,
Za ka yi murna da ni, ni talikinka.
16 Sa’an nan za ka lura da kowace takawata
Amma ba za ka bi diddigin zunubaina ba.
17 Za ka soke zunubaina ka kawar da su,
Za ka shafe dukan kurakuran da na taɓa yi.
18 “Lokaci na zuwa sa’ad da duwatsu za su fāɗi,
Har ma za a kawar da duwatsun bakin teku.
19 Ruwa zai zozaye duwatsu, su ragu,
Ruwan sama mai ƙarfi zai kwashe jigawa,
Kai ma ka bar mutane, ba su da sauran sa zuciya ko kaɗan.
20 Ka fi ƙarfin mutum, ka kore shi har abada,
Fuskarsa ta rikiɗe sa’ad da ya mutu.
21 ‘Ya’yansa maza za su sami girma,
amma sam, ba zai sani ba,
Sam, ba wanda zai faɗa masa sa’ad da aka kunyatar da su.
22 Ciwon jikinsa da ɓacin zuciyarsa kaɗai yake ji.”