Elifaz Ya Tsauta wa Ayuba
1 Elifaz ya yi magana.
2 “Surutai, Ayuba! Surutai!
3 Ba wani mai hikima wanda zai yi magana irin taka,
Ko kuma ya kāre kansa da irin maganganun da ba su da ma’ana.
4 Kana karya jama’a, kana hana su jin tsoron Allah,
Kana hana su yin addu’a gare shi.
5 Mugun lamirinka shi ne yake magana yanzu,
Kana ƙoƙari ka ɓuya a bayan maganganunka na wayo.
6 Ba na bukata in kā da kai,
Kowace kalma da ka hurta ta kā da ka.
7 “Kana tsammani kai ne mutumin da aka haifa na farko?
Sa’ad da Allah ya yi duwatsu kana nan?
8 Ko ka taɓa jin shirye-shiryen da Allah ya yi?
Ko kai kaɗai kake da hikima a cikin mutane?
9 Ba wani abu da ka sani da mu ba mu sani ba.
10 Daga wurin mutanen da suka yi furfura muka koyi hikimarmu.
Mun koyi hikimarmu daga mutane waɗanda aka haife su
Tun kafin a haifi mahaifinka.
11 “Allah yana ta’azantar da kai,
Me ya sa har yanzu ka ƙi kulawa da shi?
Mun yi magana a madadinsa a natse da lafazi mai daɗi.
12 Amma ka ta da hankalinka,
Kana ta zazzare mana ido da fushi.
13 Fushi kake yi da Allah, kana ƙinsa.
14 Akwai mutumin da yake tsarkakakke sarai?
Akwai mutumin da yake cikakke a wurin Allah?
15 Me ya sa Allah bai sakar wa mala’ikunsa kome ba?
Har su ma ba tsarkaka suke a gare shi ba.
16 Mutum yakan sha mugunta kamar yadda yake shan ruwa,
Hakika mutum ya lalace, ya zama mai rainako.
17 “Yanzu ka saurara, ya Ayuba, ga abin da na sani.
18 Mutane masu hikima sun koya mini gaskiya
Wadda suka koya daga wurin kakanninsu,
Ba su kuwa ɓoye mini asirin kome ba.
19 Ƙasaru ‘yantacciya ce daga baƙi
Ba wanda zai raba su da Allah.
20 “Mugun mutum mai zaluntar sauran mutane
Zai kasance da wahala muddin ransa.
21 Zai ji ƙarar muryoyi masu firgitarwa a kunnuwansa.
‘Yan fashi za su fāɗa masa
Sa’ad da yake tsammani ba abin da zai same shi.
22 Bai sa zuciya zai kuɓuta daga duhu ba,
Gama takobi yana jiransa a wani wuri don ya kashe shi.
23 Yana ta yawon neman abinci, yana ta cewa, ‘Ina yake?’
Ya sani baƙin ciki ne yake jiransa a nan gaba. Kamar sarki mai iko,
24 Haka masifa take shirin fāɗa masa.
25 “Wannan shi ne ƙaddarar mutum,
Wanda ya nuna wa Allah yatsa,
Ya kuwa raina Mai Iko Dukka.
26 Wannan mutum mai girmankai ne, ɗan tawaye.
27 Ya ɗauki garkuwarsa kamar ɗan yaƙi,
Ya ruga don ya yi yaƙi da Allah.
28 Shi ne mutumin da ya ci birane da yaƙi,
Ya ƙwace gidajen waɗanda suka tsere,
Amma yaƙi ne zai hallaka birane da gidaje.
29 Arzikinsa ba zai daɗe ba,
Duk abin da ya mallaka ba zai daɗe ba.
Har inuwarsa ma za ta shuɗe,
30 Ba kuwa zai kuɓuta daga duhu ba.
Zai zama kamar itacen da wuta ta ƙone rassansa,
Kamar itace kuma da iska ta kaɗe furensa.
31 Idan wauta tasa ta kai shi ga dogara ga mugunta,
To, mugunta ce kaɗai zai samu.
32 Kafin kwanakinsa su cika zai bushe,
Zai bushe kamar reshe, ba zai ƙara yin ganye ba.
33 Zai ama kamar itacen inabi
Wanda ‘ya’yansa suka kakkaɓe tun kafin su nuna,
Kamar itacen zaitun wanda bai taɓa yin ‘ya’ya ba.
34 Marasa tsoron Allah ba za su sami zuriya ba,
Wuta za ta cinye gidajen da aka gina da dukiyar rashawa.
35 Waɗannan su ne irin mutanen da suke shirya tarzoma, su aikata mugunta.
Kullum zuciyarsu cike take da ruɗarwa.”