1 “Ƙarshen raina ya gabato, da ƙyar nake numfashi,
Ba abin da ya rage mini sai kabari.
2 Na lura da yadda mutane suke yi mini mummunar ba’a.
3 Ni amintacce ne, ya Allah, ka yarda da maganata.
Ba wanda zai goyi bayan abin da nake faɗa.
4 Ka baƙantar da hankalinsu, ya Allah,
Kada ka bar su su yi mini duban wulakanci yanzu.
5 A karin maganar mutanen dā an ce,
‘Kowa ya ci amanar abokinsa saboda kuɗi,
‘Ya’yansa sā sha wahala!’
6 Yanzu kuwa sun mai da wannan karin magana a kaina.
Da mutane suka ji,
Suka zo suka yi ta tofa mini yau a fuska.
7 Baƙin cikina ya kusa makantar da ni,
Hannuwana da ƙafafuna sun rame,
sun zama kamar kyauro.
8 Duk waɗanda suka zaci su adalai ne sun razana.
Dukansu sun kāshe ni, cewa ni ba mai tsoron Allah ba ne.
9 Har su ma da suke cewa su mutanen kirki ne
Suna ƙara tabbatarwa ba su yi kuskure ba.
10 Amma da a ce dukansu za su zo su tsaya a gabana,
Da ba zan sami mai hikima ko ɗaya daga cikinsu ba.
11 “Kwanakina sun ƙare, shirye-shiryena sun kāsa,
Ba ni da sauran sa zuciya.
12 Amma abokaina sun ce dare shi ne hasken rana,
Sun kuma ce haske yana kusa,
Ko da yake ina cikin duhu.
13 Ba ni da sauran sa zuciya,
Gidana yana lahira,
Inda zan kwanta in yi ta barci cikin duhu.
14 Zan ce kabari shi ne mahaifina,
Tsutsotsin da suke cinye ni su ne mahaifiyata, da ‘yan’uwana mata.
15 Ina ne zan sa zuciyata?
Wane ne ya ga inda zan sa ta?
16 Akwai wanda ya yi shiri a binne shi tare da ni,
Mu tafi tare da shi zuwa lahira?”