Zofar Ya Nuna Rabon Mugu
1 Zofar ya amsa.
2 “Ayuba, ka ɓata mini rai,
Ba zan yi haƙuri ba, sai na ba ka amsa.
3 Abin da ka faɗa raini ne,
Amma na san yadda zan ba ka amsa.
4 “Hakika ka sani tun daga zamanin dā,
Sa’ad da aka fara sa mutum a duniya,
5 Ba wani mugun mutum wanda ya taɓa daɗewa da farin ciki.
6 Mai yiwuwa ne ya ƙasaita, ya zama kamar hasumiya a sararin sama.
Ya ƙasaita har kansa ya taɓa gizagizai.
7 Amma zai shuɗe kamar ƙura.
Waɗanda dā suka san shi,
Za su yi mamaki saboda rashin sanin inda ya tafi.
8 Zai ɓace kamar mafarki, kamar wahayi da dad dare,
Ba kuwa za a ƙara ganinsa ba.
9 Ba za a ƙara ganinsa a wurin zamansa ba.
10 Tilas ‘ya’yansa maza su biya zambar da ya yi wa matalauta,
Tilas hannuwansa su biya dukiyar da ya ƙwace.
11 Ko da yake gagau yake, ma’aikaci ne kuma sa’ad da yake yaro,
Duk da haka ba da jimawa ba, zai zama ƙura.
12-13 Ɗanɗana mugunta yana da daɗi a gare shi ƙwarai,
Yakan sa wata a bakinsa don ya riƙa jin daɗin tsotsanta.
14 Amma a cikinsa wannan abinci yakan zama da ɗaci,
Ɗacinsa kamar na kowane irin dafi mai ɗaci ne.
15 Mugun mutum yakan harar da dukiyar da ya samu ta hanyar zamba,
Allah zai karɓe ta har da wadda ya ci a cikin cikinsa.
16 Abin da mugu ya haɗiye kamar dafi yake,
Yakan kashe shi kamar saran maciji mai mugu dafi.
17 Zai mutu bai ga kogunan man zaitun ba,
Ba kuwa zai ga rafuffukan da suke da yalwar albarka ba.
18 Tilas ya rabu da dukan abin da ya yi wahalarsa.
Ba dama ya mori dukiyarsa,
19 Saboda zalunci da rashin kula da matalauta,
Da ƙwace gidajen da waɗansu suka gina.
20 “Har abada ba zai kai ga samun abin da yake wahala ba.
21 Sa’ad da ya ci ba zai yi saura ba,
Gama yanzu dukiyarsa ta ƙare.
22 A lokacin da yake gaɓar samunsa,
Baƙin ciki mai nauyin gaske zai ragargaza shi.
23 Bari ya ci duk irin abin da yake so!
Allah zai hukunta shi da hasala da fushi.
24 Lokacin da yake ƙoƙari ya kuɓuta daga takobin baƙin ƙarfe,
Za a harbe shi da bakan tagulla ya fāɗi warwar.
25 Kibiya za ta kafe a jikinsa
Tsininta zai yi ta ɗiɗɗiga da jini,
Razana ta kama zuciyarsa.
26 Aka hallaka dukan abin da ya tattara,
Wutar da ba hannun mutum ya kunna ba
Ta ƙone shi, shi da iyalinsa duka.
27 Samaniya ta bayyana zunubin wannan mutum,
Duniya kuma ta ba da shaida gāba da shi.
28 Dukan dukiyarsa za a hallaka ta a rigyawar fushin Allah.
29 “Wannan ita ce ƙaddarar mugaye,
Wadda Allah ya ƙayyade musu.”