Ayuba Ya Bayyana Rabon Mugaye
1 Ayuba ya amsa.
2 “Na rantse da Allah Mai Iko Dukka,
Wanda ya ƙwace mini halaliyata,
Wanda ya ɓata mini rai.
3 Muddin ina numfashi,
Ruhun Allah kuma yana cikin hancina
4 Bakina ba zai faɗi ƙarya ba,
Harshena kuma ba zai hurta maganganun yaudara ba.
5 Allah ya sawwaƙa in ce kun yi daidai,
Har in mutu ba zan daina tsare mutuncina ba.
6 Ina riƙe da adalci kam, ba kuwa zan sake shi ba,
Zuciyata ba ta zarge ko ɗaya daga cikin kwanakin raina ba.
7 “Bari maƙiyina ya zama kamar mugun mutum,
Wanda ya tashi gāba da ni ya zama kamar marar adalci.
8 Wace sa zuciya take ga marar tsoron Allah?
Sa’ad da Allah ya datse shi, ya ɗauke ransa?
9 Allah kuwa zai ji kukansa sa’ad da wahala ta same shi?
10 Ko Mai Iko Dukka zai zama abin farin ciki a gare shi?
Ko zai yi kira ga Allah a kowane lokaci?
11 “Zan koya muku zancen ikon Allah,
Abin da yake na wajen Mai Iko Dukka ba zan ɓoye ba.
12 Ga shi kuwa, dukanku kun gani da kanku,
Me ya sa kuka zama wawaye?
13 “Wannan shi ne rabon mugaye daga wurin Allah,
Gādo ne kuma wanda azzalumai za su karɓa daga wurin Mai Iko Dukka.
14 Idan ‘ya’yansu sun riɓaɓɓanya za su zama rabon takobi,
Zuriyarsu kuwa ba za su sami isasshen abinci ba.
15 Waɗanda suka tsira, annoba za ta kashe su,
Matansu ba za su yi makokin mutuwarsu ba.
16 Ko da yake sun tsibe azurfa kamar turɓaya,
Sun tara tufafi kamar ƙasa,
17 Za su tara, amma adalai za su sa,
Marasa laifi ne za su raba azurfar.
18 Sun gina gidajensu kamar saƙar gizo-gizo,
Kamar bukkar mai tsaro.
19 Attajirai za su kwanta, amma daga wannan shi ke nan,
Za su buɗe ido su ga dukiyan nan ba ta.
20 Razana za ta auka musu kamar rigyawa.
Da dare iska za ta tafi da su.
21 Iskar gabas za ta fauce su su tafi,
Ta share su ta raba su da wurin zamansu.
22 Za ta murɗe su ba tausayi,
Hakika za su yi ƙoƙari su tsere daga ikonsa,
Sai su yi ƙundumbala.
23 Kowa zai tafa hannu yă yi musu tsaki har su tashi daga wurin da suke.”