Ayuba Ya Tabbatar da Mutuncinsa
1 “Na yi alkawari da idanuna,
Me zai sa in ƙyafaci budurwa?
2 Wane rabo zan samu daga wurin Allah a Sama?
Wane gādo kuma zan samu daga wurin Mai Iko Dukka a can samaniya?
3 Yakan aika da masifa da lalacewa
Ga waɗanda suke aikata abin da ba daidai ba.
4 Allah ya san dukan abin da nake yi,
Yana ƙididdige dukan takawata.
5 “Idan ina tafiya da rashin gaskiya,
Ina hanzari don in aikata yaudara,
6 Bari Allah ya auna ni da ma’aunin da yake daidai,
Zai kuwa san mutuncina.
7 Idan dai na kauce daga hanya,
Ko kuwa zuciyata ta bi sha’awar idanuna,
Idan akwai ko ɗan sofane a hannuna,
8 To, bari in shuka, wani ya ci amfanin,
Bari a tumɓuke amfanin gonata.
9 “Idan na yi sha’awar wata mace,
Har na je na laɓe a ƙofar maƙwabcina,
10 To, bari matata ta yi wa wani abinci,
Bari waɗansu su kwana da ita.
11 Gama wannan mugun laifi ne ƙwarai,
Wanda alƙalai ne za su hukunta.
12 Za ta zama wuta mai ci har ta hallaka,
Za ta cinye saiwar abin da na shuka ƙurmus.
13 “Idan a ce ban kasa kunne ga kukan barorina mata da maza ba,
Sa’ad da suka kawo koke-kokensu a kaina,
14 To, wace amsa zan ba Allah sa’ad da ya tashi don ya hukuntar?
Me zan iya faɗa sa’ad da Allah ya zo yi mini shari’a?
15 Ashe, shi wanda ya halicce ni a cikin mahaifa,
Ba shi ne ya halicce su ba?
Shi wanda ya siffata mu a cikin mahaifa?
16 “Ban taɓa ƙin taimakon matalauta ba,
Ban kuma taɓa sa gwauruwar da mijinta ya mutu ta yi kuka ba,
17 Ko kuwa in bar marayu da yunwa sa’ad da nake cin abincina,
18 Tun suna yara nake goyonsu,
Ina lura da su kamar ‘ya’yan cikina.
19 “Amma idan na ga wani yana lalacewa saboda rashin sutura,
Ko wani matalauci marar abin rufa,
20 Idan a zuciyarsa bai sa mini albarka ba,
Ko bai ji ɗumi da ulun tumakina ba,
21 Ko na ɗaga hannuna don in cuci maraya,
Don na ga ina da kafar kuɓuta,
22 To, ka sa kafaɗuna su ɓaɓɓalle daga inda suke.
Ka kakkarya gwiwoyin hannuna.
23 Gama bala’i daga wurin Allah ya razanar da ni,
Saboda ɗaukakarsa ba zan iya yin kome ba.
24 “Idan na ce ga zinariya na dogara, ko zinariya tsantsa ita ce jigona,
25 Idan kuma saboda yawan dukiyata nake fariya,
Ko saboda abin da na mallaka ne,
26 Idan ga hasken rana nake zuba ido,
Ko ga hasken farin wata ne,
27 Zuciyata ta jarabtu ke nan a asirce,
Ni da kaina ina sumbatar hannuna,
28 Wannan ma zai zama laifi ne wanda alƙalai za su hukunta,
Gama na zama munafukin Allah Mai Iko Dukka ke nan.
29 “Idan na yi murna saboda wahala ta sami maƙiyana,
Ko na yi fariya saboda mugun abu ya same shi,
30 Ban yi zunubi da bakina ba,
Ban nemi ran wani ta wurin la’anta shi ba.
31 Ko mutanen da suke cikin alfarwata ba wanda zai ce,
Ga wani can da bai ƙoshi da nama ba.
32 Ban bar baƙi su kwana a titi ba,
Ƙofar gidana a buɗe take ga matafiya.
33 Idan na ɓoye laifofina a zuciyata,
34 Ko na tsaya shiru saboda tsoron taron jama’a,
Saboda kuma baƙar maganar mutane ta razanar da ni,
35 Da a ce ina da wanda zai kasa kunne gare ni,
Da sai in sa hannu a kan abin da na faɗa,
Allah kuwa Mai Iko Dukka ya amsa mini.
“Da ƙarar da maƙiyana suke kai ni, a rubuce ne,
36 Hakika da sai in ɗauke ta a kafaɗata,
In kuwa naɗa ta a kaina kamar rawani.
37 Da na ba Allah dukan lissafin abin da na taɓa yi,
In tinƙare shi kamar ni basarauce ne.
38 “Idan ƙasata tana kuka da ni,
Ita da kunyoyinta,
39 Ko na ci amfaninta ban biya ba,
Ko na yi sanadin mutuwar mai ita,
40 Ka sa ƙayayuwa su tsiro maimakon alkama,
Tsire-tsire marasa amfani kuma maimakon sha’ir.”
Maganar Ayuba ta ƙare.