Elihu Ya Tsauta wa Ayuba
1 “Amma yanzu, kai Ayuba, ka yarda ka ji maganata,
Ka kasa kunne ga dukan abin da zan faɗa.
2 Ga shi, na buɗe baki in yi magana.
3 Maganar da zan hurta ainihin gaskiyar da take a zuciyata ce,
Abin da zan faɗa kuma dahir ne.
4 Ruhun Allah ne ya yi ni, Mai Iko Dukka ya hura mini rai.
5 “Ka amsa mini, in ka iya,
Ka shirya abubuwan da za ka faɗa mini, ka yi tsaye a kansu.
6 Duba, ni da kai ɗaya muke a wajen Allah,
Dukanmu biyu kuma daga yumɓu aka siffata mu.
7 Don haka kada ka razana saboda ni,
Abin da zan faɗa maka, ba abin da zai fi ƙarfinka.
8 “Hakika na ji maganar da ka yi,
Na kuwa ji amon maganganunka,
9 Ka ce kai tsattsarka ne, ba ka da laifi,
Kai tsabtatacce ne, ba ka da wata ƙazanta.
10 Ka ce Allah ya zarge ka ya ɗauke ka tankar maƙiyansa,
11 Ya saka ka a turu,
Yana duban dukan al’amuranka.
12 “Amma a kan wannan, Ayuba, ka yi kuskure, zan ba ka amsa,
Gama Allah ya fi kowane mutum girma.
13 Me ya sa kake yi wa Allah gunaguni,
Cewa ba ya karɓar maganarka ko ɗaya?
14 Gama Allah yakan yi magana sau ɗaya ne,
I, har sau biyu, duk da haka mutum ba ya lura.
15 Yakan sanar a mafarkai ko a wahayi
Sa’ad da barci mai nauyi ya ɗauke su,
A sa’ad da suke barci a gadajensu.
16 Yakan buɗe kunnuwan mutane,
Ya tsorata su da faɗakarwarsa,
17 Domin ya kawar da su daga aikin da suke yi,
Ya kuma kawar musu da girmankai.
18 Yakan hana su zuwa kabari,
Ya hana ransu halaka da takobi.
19 “Akan hori mutum da cuta mai zafi a gadonsa,
Ya yi ta fama da azaba a cikin ƙasusuwansa,
20 Ransa yana ƙyamar abinci,
Yana ƙyamarsa kome daɗinsa kuwa.
21 Yakan rame ƙangayau, ƙasusuwansa duk a waje.
22 Yana gab da shiga kabari,
Ransa yana hannun mala’ikun mutuwa.
23 “Da a ce akwai wani mala’ika mai sulhuntawa a tsakani,
Ko da ɗaya daga cikin dubu ne wanda zai faɗa wa mutum,
24 Mala’ikan da zai yi masa alheri ya ce,
‘Ka cece shi daga gangarawa zuwa cikin kabari,
Na sami abin da zai fanshe shi!’
25 Naman jikinsa zai koma kamar na saurayi,
Zai komo kamar lokacin da yake gaɓar ƙarfinsa.
26 Sa’an nan ne mutum zai yi addu’a ga Allah, ya karɓe shi,
Ya zo gabansa da murna,
Allah zai komar wa mutum da adalcinsa.
27 Zai raira waƙa a gaban jama’a, ya ce, ‘Na yi zunubi. Ban yi daidai ba,
Amma ba a sa ni in biya ba.
28 Allah ya fanshe ni daga gangarawa zuwa kabari,
Raina kuwa zai ga haske.’
29 “Ga shi kuwa, Allah ya yi dukan waɗannan abubuwa sau biyu, har ma sau uku ga mutum,
30 Don ya komo da ran mutum daga kabari,
Domin a haskaka shi da hasken rai.
31 “Haba Ayuba, ka kula fa, ka kasa kunne,
Ga abin da nake faɗa,
Ka yi shiru, zan yi magana.
32 Amma idan kana da ta cewa, to, amsa,
Yi magana, gama ina so in kuɓutar da kai.
33 In kuwa ba haka ba, sai ka yi shiru,
Ka kasa kunne gare ni,
Zan kuwa koya maka hikima.”