Elihu ya ga Allah ya yi Daidai
1 Elihu ya ci gaba.
2 “Ku mutane masu hikima, ku ji maganata,
Ku kasa kunne ga abin da zan faɗa, ku masana.
3 Kunne yake rarrabewa da magana,
Kamar yadda harshe yake rarrabewa da ɗanɗanar abinci.
4 Bari mu zaɓi abin da yake daidai,
Bari kuma mu daidaita abin da yake mai kyau tsakanin junanmu.
5 Gama Ayuba ya ce, ‘Ni marar laifi ne,
Amma Allah ya ƙwace mini halaliyata.
6 Duk da rashin laifina an ɗauke ni a maƙaryaci,
Raunina ba ya warkuwa ko da yake ba ni da laifin kome.’
7 “Wane irin mutum ne kai, Ayuba,
Da kake shan raini kamar yadda kake shan ruwa,
8 Wanda yake cuɗanya da ƙungiyar masu aikata laifi,
Kana yawo tare da mugaye?
9 Gama ka ce, ‘Bai amfana wa mutum kome ba
Ya yi murna da Allah.’
10 “Saboda haka ku kasa kunne gare ni, ku da kuke haziƙai,
Sam, Allah ba mai aikata mugunta ba ne,
A wurin Mai Iko Dukka ba kuskure,
11 Gama bisa ga aikin mutum yake sāka masa,
Yana sa aniyarsa ta bi shi.
12 Gaskiya ce, Allah ba zai aikata mugunta ba,
Mai Iko Dukka ba zai kauce wa adalci ba.
13 Wa ya shugabantar da shi a kan duniya?
Wa ya mallakar masa da duniya duka?
14 Da zai amshe ruhu da numfashin da ya hura wa mutum,
15 Da duk mai rai ya halaka,
Mutum kuma ya koma ƙura.
16 “Idan kai haziƙi ne, to, ji wannan,
Kasa kunne ga abin da zan faɗa.
17 Da Allah maƙiyin adalci ne, da ya yi mallaka?
Ka iya sa wa Adali, Mai Iko Dukka laifi?
18 Ka iya sa wa Allah laifi,
Shi da ya ce, ‘Sarki marar amfani ne,
Hakimai kuma mugaye’?
19 Ba ya nuna sonkai ga sarakuna,
Ko kuma ya fi kulawa da attajira fiye da matalauta,
Gama shi ya halicce su duka.
20 Sukan mutu nan da nan,
Da tsakar dare manya da ƙanana sukan shuɗe farat ɗaya,
An kawar da su ba da hannun mutum ba.
21 “Gama yana ganin al’amuran mutum,
Yana kuma ganin dukan manufarsa.
22 Ba wani duhu, ko duhu baƙi ƙirin
Inda masu aikata mugunta za su ɓuya.
23 Ba ajiyayyen lokacin da ya ajiye wa kowane mutum
Da zai je shari’a a gaban Allah.
24 Yakan ragargaza ƙarfafa ba tare da wani bincike ba,
Ya sa waɗansu a madadinsu.
25 Saboda sanin ayyukansu,
Yakan kaɓantar da su da dare ya ragargaza su,
26 Yakan buge su a gaban mutane saboda muguntarsu,
27 Don sun daina binsa, ba su kula da ko ɗaya
Daga cikin umarnansa ba.
28 Suka sa matalauta su yi kuka ga Allah,
Ya kuwa ji kukan waɗanda ake tsananta wa.
29 Idan Allah zai yi shiru, da wa zai sa wa wani laifi?
Idan ya ɓoye fuskarsa, wa zai iya ganinsa,
Ko aka yi wa al’umma ko ga mutum?
30 Bai kamata marar tsoron Allah ya yi mulki ba,
Don kada ya tura jama’a cikin tarko.
31 “Akwai wanda zai ce wa Allah, ‘Ni horarre ne,
Ba zan ƙara yin laifi ba?
32 Ka koya mini abin da ban sani ba,
Idan na yi laifi, ba zan ƙara yi ba.’
33 Zai kuɓutar domin ya gamshe ka saboda ka ƙi yarda?
Tilas kai za ka zaɓa, ba ni ba,
Saboda haka sai ka hurta abin da ka sani.
34 “Haziƙan mutane da mutum mai hikima da suka ji ni za su ce,
35 ‘Ayuba yakan yi magana ne ba tare da sanin abin da yake yi ba,
Maganarsa ba ta mai hangen nesa ba ce.
36 Da ma a gwada Ayuba har ƙarshe,
Saboda amsar da yake bayarwa ta mugaye.
37 Gama ya ƙara zunubinsa da tayarwa,
Yana tafa hannunsa a tsakaninmu,
Yana yawaita maganganunsa gāba da Allah.’ ”