Ubangiji Ya Tabbatar da Jahilcin Ayuba
1 Ubangiji ya yi magana da Ayuba ta cikin guguwa.
2 “Wane ne wannan da yake ɓāta shawara
Da maganganu marasa ma’ana?
3 Ka tashi tsaye ka sha ɗamara kamar namiji,
Zan yi maka tambaya, kai kuwa ka ba ni amsa.
4 A ina kake sa’ad da na aza harsashin gina duniya?
Faɗa mini idan ka sani.
5 Wane ne ya zayyana kusurwoyinta?
Hakika ka sani.
Wane ne kuma ya auna ta?
6 A kan me aka kafa tushenta?
Wa ya aza dutsen kan kusurwarta?
7 Sa’ad da taurarin asuba suka raira waƙa tare,
Sai mala’iku duka suka yi sowa saboda murna.
8 “Wa ya yi wa teku iyaka
Sa’ad da ta tumbatso daga zurfafa?
9 Sa’ad da na suturta ta da gizagizai,
Na yi mata maɗauri da duhu ƙirin.
10 Na sa mata iyakoki,
Na sa mata ƙyamare da ƙofofi,
11 Na ce mata, ‘Iyakar inda za ki tsaya ke nan,
Ba za ki wuce ba.
Nan raƙuman ruwanki masu tumbatsa za su tsaya.’
12 “Ayuba, a dukan kwanakinka
Ka taɓa umartar wayewar gari,
Ko ka sa alfijir ya keto?
13 Da gari ya waye,
Ka kawar da muguntar da ake yi da dare?
14 Yakan sāke kamar lakar da take ƙarƙashin hatimi,
Yakan rine kamar riga.
15 Akan hana wa mugaye haske,
Sa’ad da sukan ɗaga hannuwansu sama akan kakkarya su.
16 “Ko ka taɓa shiga cikin maɓuɓɓugan teku?
Ka taɓa yin tafiya a cikin zurfin lallokin teku?
17 An taɓa nuna maka ƙofofin mutuwa?
Ko kuwa ka taɓa ganin ƙofofin duhu ƙirin?
18 Ko ka san iyakar fāɗin duniya?
Ka amsa mini in ka san dukan waɗannan.
19 “Ina hanya zuwa wurin da haske yake?
A ina kuma duhu yake?
20 Ka san iyakarsa ko mafarinsa?
21 Ka sani, gama a lokacin nan an haife ka,
Shekarunka kuwa suna da yawa.
22 “Ka taɓa shiga rumbunan dusar ƙanƙara?
Ko kuwa ka taɓa shiga rumbunan ajiyar ƙanƙara?
23 Na adana su ne don lokacin wahala,
Domin ranar faɗa da ta yaƙi.
24 Ina hanya zuwa inda rana take fitowa,
Ko kuma ta inda iskar gabas take hurowa ta māmaye ko’ina?
25 “Wa ya haƙa hanyar da ruwan sama mai kwararowa zai bi?
Da kuma hanyar da gatarin aradu zai bi?
26 Wa ya kuma kawo ruwan sama a ƙasar da ba mutane,
Da a cikin hamada inda ba kowa,
27 Don a shayar da zozayar ƙasa inda ba kowa,
Har ta tsiro da ciyayi?
28 “Ruwan sama yana da mahaifi?
Wa ya haifi ɗiɗɗigar raɓa?
29 Wace ce mahaifiyar ƙanƙara?
Wace ce kuma ta haifi jaura?
30 Ruwa ya daskare ya yi ƙarfi kamar dutse,
Teku ta daskare.
31 “Za ka iya ɗaure sarƙoƙin kaza-da-‘ya’yanta?
Ko ka iya kwance igiyoyin mafarauci-da-kare-da-zomo?
32 Za ka iya bi da yaneyanen sararin sama bisa ga fasalinsu?
33 Ka san ka’idodin sammai?
Ko ka iya faɗar yadda suka danganta da duniya?
34 “Kana iya yi wa gizagizai tsawa,
Don su kwararo ruwan sama, ya rufe ka?
35 Ka iya aikar walƙiyoyi su tafi,
Sa’an nan su ce maka, ‘Ga mu mun zo?’
36 Wa ya sa hikima a gizagizai,
Ko kuma wa ya ba da ganewa ga kāsashi?
37 Akwai mai hikimar da zai iya ƙidaya gizagizai?
Ko kuwa wa zai iya karkato da salkunan ruwan sammai,
38 Sa’ad da ƙura ta murtuke ta taru jingim, ta game kam?
39 “Ka iya farauto wa zakoki abinci?
Ko ka ƙosar da yunwar sagarun zakoki,
40 Sa’ad da suke fako a kogwanninsu,
Ko suna kwance suna jira a maɓoyarsu?
41 Wa yake tanada wa hankaka abincinsa,
Sa’ad da ‘ya’yansa suke kuka ga Allah,
Suna kai da kawowa saboda rashin abinci?”