Elifaz Ya Tsauta wa Ayuba
1 Elifaz ya yi magana.
2 “Ayuba, za ka ji haushi in na yi magana?
Ba zan iya kannewa, in yi shiru ba.
3 Ka koya wa mutane da yawa,
Ka kuma ƙarfafa hannuwan marasa ƙarfi.
4 Idan wani ya yi tuntuɓe,
Ya gaji, ya rasa ƙarfi,
Kalmominka suka ƙarfafa zuciyarsa,
Har ya iya tsayawa kyam.
5 Yanzu naka lokacin wahala ya zo,
Kai kuwa ka rikice, ka kasa ɗaurewa,
6 Kana yi wa Allah sujada,
Ba wani laifi a zamanka,
Ya kamata ka amince ka sa zuciya.
7 “Yanzu fa sai ka yi tunani.
Ka faɗi bala’i ɗaya wanda ya taɓa fāɗa wa adalin mutum.
8 Na taɓa ganin mutane suna huɗe gonar mugunta,
Suna shuka mugunta,
Suka kuwa girbe mugunta.
9 A cikin fushinsa Allah yakan hallaka su kamar hadiri.
10 Mugaye sukan yi ruri suna gurnani kamar zakoki,
Amma Allah yakan sa su yi tsit,
Ya kakkarya haƙoransu.
11 Kamar zakoki da ba su da abin da za su kashe su ci,
Haka nan za su mutu, ‘ya’yansu kuwa su warwatse duka.
12 “Wata rana wani saƙo ya zo a hankali,
Har da ƙyar nake iya ji,
13 Kamar wani irin mafarki mai razanarwa yake,
Wanda ya hana ni jin daɗin barcina.
14 Na yi rawar jiki ina makyarkyata,
Duk jikina yana ta ɓare-ɓare don tsoro.
15 Wata iska marar ƙarfi ta taɓa fuskata,
Sai fatar jikina ta yanƙwane saboda fargaba.
16 Na ga wani abu can yana tsaye,
Na zura ido, amma ban san kowane irin abu ba ne,
Ina cikin wannan hali sai na ji murya,
17 Ta ce, ‘Mutum yana iya zama adali a gaban Allah?
Akwai kuma wanda yake mai tsarki a gaban Mahaliccinsa?
18 Allah ba ya amince wa barorinsa na cikin sammai,
Yakan sami laifi a wurin mala’ikunsa.
19 Ta ƙaƙa zai amince da talikinsa wanda aka yi da ƙasa,
Abin da yake na ƙura, ana kuwa iya murƙushe shi kamar asu.
20 Mai yiwuwa ne mutum yana raye da safe
Amma ya mutu ba a sani ba kafin maraice.
21 Duk abin da ya mallaka an ɗauke,
Duk da haka ya mutu cikin rashin hikima.’ ”