1 Ubangiji ya yi wa Ayuba magana.
2 “Mai neman sa wa wani laifi ya jā da Mai Iko Dukka?
Wanda yake gardama da Allah, bari ya ba da amsa.”
3 Ayuba ya amsa wa Ubangiji ya ce,
4 “Ai, ni ba a bakin kome nake ba,
Wace amsa zan ba ka?
Na rufe bakina na yi gam.
5 Ai, na riga na yi magana sau ɗaya, har ma sau biyu,
Ba zan amsa ba, ba zan ƙara cewa kome ba.”
Bayyanuwar Ikon Allah
6 Sa’an nan Ubangiji ya amsa wa Ayuba daga cikin guguwa, ya ce,
7 “Tashi tsaye ka sha ɗamara kamar namiji,
Zan yi maka tambaya, kai kuwa ka ba ni amsa.
8 Kai kanka za ka sa mini laifi?
Za ka kā da ni don kai ka barata?
9 Kana da ƙarfi kamar na Allah?
Kana iya tsawa da murya kamar tasa?
10 “Ka caɓa ado da kwarjini da ɗaukaka,
Ka yafa daraja da maƙami.
11 Ka kwararar da rigyawar fushinka,
Ka dubi dukan wanda yake alfarma, a wulakance.
12 Ka dubi dukan wanda yake alfarma ka ƙasƙantar da shi,
Ka tattake mugaye a inda suke.
13 Dukansu ka binne su a ƙasa,
Ka ɗaure fuskokinsu, ka jefa su a lahira.
14 Sa’an nan ni kaina kuma zan sanar da kai,
Cewa da hannun damanka za ka yi nasara.
15 “Ga dorina wanda ni na halicce ta,
Kamar yadda na halicce ka,
Tana cin ciyawa kamar sa.
16 Ga shi, ƙarfinta yana cikin ƙugunta,
Ikonta yana cikin tsakar cikinta.
17 Na yi mata wutsiya miƙaƙƙiya, mai ƙarfi kamar itacen al’ul,
Jijiyoyin cinyoyinta suna haɗe wuri ɗaya
18 Ƙasusuwanta bututun tagulla ne,
Gaɓoɓinta kamar sandunan ƙarfe ne.
19 “Ita ce ta farko cikin ayyukan Allah,
Sai Mahaliccinta kaɗai yake iya tunkararta da takobi!
20 Gama duwatsu suke ba ta abinci,
A inda dukan namomin jeji suke wasa.
21 Takan kwanta a inuwar ƙaddaji,
Ta ɓuya a cikin iwa, da a fadama.
22 Gama inuwar da take rufe ta ta ƙaddaji ce,
Itatuwan wardi na rafi, sun kewaye ta.
23 Ga shi, ba ta jin tsoron tumbatsar kogi,
A natse take, ko da ta bakinta rigyawar Urdun take wucewa.
24 Akwai wanda zai iya kama ta da ƙugiya,
Ko ya sa mata asirka?”