Ayuba Ya Tuba aka kuma Karɓe Shi
1 Ayuba ya amsa wa Ubangiji.
2 “Na sani kai kake da ikon yin dukan abu,
Ba wanda ya isa ya hana ka yin abin da ka nufa.
3 Wane ne wannan marar ilimi da zai ɓoye shawara?
Saboda haka na hurta abin da ban gane ba,
Abubuwa waɗanda ban gane ba suna banmamaki ƙwarai.
4 Ka ce, ‘Kasa kunne, zan yi magana da kai,
Zan yi maka tambaya, ka ba ni amsa.’
5 Dā jin labarinka nake,
Amma yanzu na gan ka ido da ido.
6 Saboda haka na ga ni ba kome ba ne,
Na tuba, ina hurwa da ƙura da toka.”
Ƙarshen Magana
7 Bayan da Ubangiji ya gama faɗa wa Ayuba waɗannan magana, sai ya ce wa Elifaz, mutumin Teman, “Ina fushi da kai da abokan nan naka biyu, gama ba ku faɗi gaskiya game da ni ba, kamar yadda bawana Ayuba ya yi.
8 Yanzu fa, sai ku kama bijimai bakwai da raguna bakwai, ku kai wa Ayuba, ku miƙa su hadaya ta ƙonawa domin kanku. Ayuba zai yi addu’a dominku, ni kuwa zan amsa addu’arsa don kada in sāka muku bisa ga wautarku. Gama ba ku faɗi gaskiya game da ni ba, kamar yadda bawana Ayuba ya yi.”
9 Sai Elifaz mutumin Teman, da Bildad mutumin Shuwa, da Zofar mutumin Na’ama suka tafi suka yi kamar yadda Ubangiji ya faɗa musu, Ubangiji kuwa ya karɓi addu’ar Ayuba.
Allah Ya Mayar wa Ayuba da Wadatarsa
10 Ubangiji kuwa ya mayar wa Ayuba da dukiyarsa, sa’ad da ya yi addu’a domin abokansa, sai Ubangiji ya mayar masa da riɓin abin da yake da shi dā.
11 Sa’an nan dukan ‘yan’uwan Ayuba mata da maza da dukan waɗanda suka san shi a dā, suka zo gidansa suka ci abinci tare da shi, suka yi juyayin abin da ya same shi, suka ta’azantar da shi,saboda dukan wahalar da Ubangiji ya aukar masa. Kowannensu ya ba shi ‘yan kuɗi da zoben zinariya.
12 Ubangiji ya sa wa wannan zamani na Ayuba albarka, har fiye da na farko. An ba shi tumaki dubu goma sha huɗu (14,000), da raƙuma dubu shida (6,000), da takarkari dubu biyu (2,000), da jakai mata dubu ɗaya (1,000).
13 Ya kuma haifi ‘ya’ya maza bakwai, mata uku.
14 Ya raɗa wa ta farin suna Yemima, da ta biyun Keziya,da ta ukun Keren-Haffuk.
15 Duk ƙasar ba ‘yan mata kyawawa kamar ‘ya’yan Ayuba. Mahaifinsu kuwa ya ba su gādo tare da ‘yan’uwansu maza.
16 Ayuba ya rayu shekara ɗari da arba’in bayan wannan, ya ga ‘ya’yansa, ya ga jikokin jikokinsa har tsara ta huɗu.
17 Sa’an nan Ayuba ya rasu da kyakkyawan tsufa.