Bildad Ya Ƙarfafa Hukuncin Allah Daidai Ne
1 Sai Bildad ya yi magana.
2 “Ka gama maganganunka marasa kan gado duka?
3 Allah bai taɓa yin danniya ba,
Bai kuma taɓa fāsa aikata abin da yake daidai ba.
4 Lalle ‘ya’yanka sun yi wa Allah zunubi,
Don haka ya hukunta su yadda ya cancanta.
5 Amma sai ka juyo ka yi roƙo ga Allah Maɗaukaki.
6 Idan kana da tsarki da aminci, Allah zai taimake ka,
Ya maido da iyalin gidanka, ya yi maka sakayya.
7 Duk hasarar dukiyan nan da ka yi, ba kome ba ne
In aka gwada da abin da Allah zai ba ka nan gaba.
8 “Ka tsai da zuciyarka a kan hikima irin ta zamanin dā.
Ka kuma yi ta yin tunani a kan gaskiyar da kakanninmu suka koya.
9 Kwanakinmu ‘yan kaɗan ne kawai,
Ba mu san kome ba,
Mu inuwa ne kawai a fuskar duniya.
10 Amma ka yarda masu hikima na zamanin dā su koya maka,
Ka kasa kunne ga abin da za su faɗa.
11 “Iwa ba ta tsirowa inda ba ruwa,
Ba a taɓa samunta a ko’ina ba sai a fadama.
12 In ruwan ta ƙafe, ita ce za ta fara bushewa,
Tun tana ƙanƙana ba ta isa a yanke a yi amfani da ita ba.
13 Marasa tsoron Allah kamar iwan nan suke,
Ba su da sa zuciya muddin sun rabu da Allah.
14 Suna dogara ga silin zare, murjin gizo-gizo.
15 Idan suka jingina ga saƙar gizo-gizo, za ta iya tokare su?
Idan sun kama ta, za ta taimake su tsayawa?
16 “Mugaye sukan tsiro kamar ciyayi a hasken rana,
Ciyayin da sukan yaɗu su cinye gona duka.
17 Saiwoyinsu sukan nannaɗe duwatsu,
Su riƙe kowane dutse da ƙarfi.
18 Amma idan aka tumɓuke su,
Ba wanda zai taɓa cewa sun kasance a wurin.
19 Hakika matuƙar murnar da mugaye suke da ita ke nan,
Yanzu waɗansu ne za su zo su gāje wurarensu.
20 “Amma daɗai Allah ba zai rabu da amintattu ba,
Ba kuwa zai taɓa taimakon mugun mutum ba.
21 Zai sāke barinka ka yi dariya ka ƙyalƙyata kamar dā,
Ka kuma yi sowa da murna matuƙa.
22 Amma zai sa maƙiyanka su sha kunya,
Za a shafe gidajen mugaye.”