AYU 9

Ayuba Ya Kasa Amsa wa Allah

1 Ayuba ya amsa.

2 “Ai, na taɓa jin waɗannan duka,

Amma ta ƙaƙa mutum zai yi jayayya da Allah har ya yi nasara?

3 Ta ƙaƙa za ka iya jayayya da shi?

Yana yiwuwa ya yi maka tambayoyi guda dubu

Waɗanda ba wanda zai iya ba da amsarsu.

4 Allah mai hikima ne, mai iko,

Ba wanda zai iya ja in ja da shi.

5 Yakan kawar da manyan duwatsu farat ɗaya,

Ya hallaka su da fushinsa,

6 Allah yakan aiko da girgizar ƙasa, ya girgiza duniya,

Yakan jijjiga ginshiƙan da duniya take zaune a kansu.

7 Allah yana da iko ya hana rana fitowa,

Ko kuma ya hana taurari haskakawa da dare.

8 Ba wanda ya taimaki Allah shimfiɗa sammai,

Wanda yake taka raƙuman ruwan teku, ya kuma kwantar da su.

9 Allah ya rataye taurari a sararin sama,

Wato su mafarauci da kare da zomo,

Da kaza da ‘ya’yanta da taurarin kudu.

10 Ba shi yiwuwa mu gane manyan abubuwa da yake yi.

Ayyukan al’ajabansa ba su da iyaka.

11 “Allah yana wucewa kusa da ni,

Amma ba na ganinsa.

12 Yakan ɗauki abin da yake so, ba wanda yake hana shi,

Ba wanda yake tambayarsa cewa,

‘Me kake yi?’

13 “Allah ba zai huce fushinsa ba.

Ya murƙushe maƙiyansa waɗanda suka taimaki dodon ruwan nan da ake kira Rahab, wanda ya tayar masa.

14 To, ƙaƙa zan yi in samo kalmomin da zan amsa wa Allah?

15 Ko da yake ba ni da laifi,

Duk da haka iyakar abin da zan iya yi ke nan,

In roƙi Allah ya yi mini jinƙai,

Shi da yake alƙalina.

16 Amma duk da haka ko ya yardar mini in yi magana ma,

Ban yi tsammani zai saurare ni ba.

17 Shi ya aiko da hadura, suka yi kacakaca da ni,

Suka ƙuƙƙuje ni, ga shi kuwa, ba wani dalilin da ya sa ya yi mini rauni.

18 Ya hana ni in ko shaƙata,

Ina jin haushin dukan abin da yake yi mini.

19 In gwada ƙarfi ne?

To, a iya gwada wa Allah ƙarfi?

In kai shi ƙara ne?

Wa zai sa shi ya je?

20 Ni ba ni da laifin kome, amintacce ne ni,

A kunne sai a ji kalmomina kamar na marar gaskiya ne.

Kowane abu da na fāɗa, kā da ni yake yi.

21 Ba ni da laifin kome, amma ba na ƙara damuwa.

Na gaji da rayuwa.

22 Don haka ban damu da kome ba.

Da marar laifin da mai laifin duk, Allah zai hallaka mu.

23 Sa’ad da marar laifi ya mutu farat ɗaya,

Allah yakan yi dariya.

24 Allah ya ba da duniya ga mugaye,

Ya makantar da dukan alƙalai,

Idan ba Allah ne ya yi haka nan ba, to, wa ya yi?

25 “Kwanakina suna shuɗewa da sauri, ba mai kyau ko ɗaya.

26 Raina na wucewa kamar jirgin ruwa mafi sauri,

Da sauri ƙwarai kamar juhurma ya kai wa zomo sura.

27 Idan an yi murmushi,

Ina ƙoƙari in manta da azabata,

28 Sai dukan wahalar da nake sha ta yi ta firgita ni,

Na sani Allah ya ɗauke ni mai laifi.

29 Tun da yake Allah ya ɗauka, ni mai laifi ne,

To, me zai sa in damu?

30 Ba sabulun da zai iya wanke zunubaina.

31 Allah ya jefa ni a kwatami,

Har tufafina ma suna jin kunyata.

32 Da a ce Allah mutum ne,

Da sai in mayar masa da magana,

Da sai mun je ɗakin shari’a a yanka mana shari’a.

33 Amma ga shi, ba wanda zai shiga tsakaninmu,

Ba wanda zai shara’anta tsakanina da Allah.

34 Ka daina hukunta ni, ya Allah!

Ka daina razanar da ni.

35 Ba na jin tsoro,

Zan yi magana, domin na san zuciyata.”