Esta Ta Yi wa Sarki da Haman Liyafa
1 A kan rana ta uku sai Esta ta sa rigunan sarautarta, ta tafi, ta tsaya a shirayi na ciki na fādar sarki, kusa da ɗakin sarki. Sarki kuwa yana zaune a gadon sarautarsa, a gidan sarautarsa, daura da ƙofar shiga fāda.
2 Sa’ad da ya ga Esta tana tsaye a shirayin, sai ya miƙa mata sandan zinariya na sarauta, gama ta sami kwarjini a wurinsa. Sai Esta ta matsa kusa ta taɓa kan sandan.
3 Sarki ya ce mata, “Mene ne, sarauniya Esta? Me kike so? Za a ba ki, ko rabin mulkina ma.”
4 Sai Esta ta ce, “Idan sarki ya yarda, bari sarki ya zo tare da Haman yau wurin liyafa da na shirya wa sarki.”
5 Sarki kuwa ya ce, “A zo da Haman maza, mu yi abin da Esta take so.” Sai sarki da Haman suka tafi liyafar da Esta ta shirya.
6 Sa’ad da suke shan ruwan inabi, sai sarki ya tambayi Esta, “Mece ce bukatarki? Za a biya miki ko da rabin mulkina ne.”
7 Sai Esta ta ce, “Bukatata, da roƙona ke nan,
8 idan na sami tagomashi a wurin sarki, idan kuma sarki ya yarda ya biya bukatata da roƙona, to, bari sarki da Haman su zo liyafar da zan yi musu, gobe kuwa zan yi abin da sarki ya faɗa.”
Haman Ya Yi Shirin Kashe Mordekai
9 Ran nan Haman ya fita da murna da farin ciki, amma da ya ga Mordekai a ƙofar sarki, Mordekai kuwa bai tashi ba, bai kuma yi rawar jiki a gabansa ba, sai ya husata ƙwarai.
10 Duk da haka Haman ya cije, ya tafi gida. Ya aika a kirawo abokansa da matarsa, Zeresh.
11 Ya faɗa musu darajar wadatarsa, da yawan ‘ya’yansa, da yawan matsayin da sarki ya girmama shi da su, da yadda sarki ya ciyar da shi gaba fiye da sarakuna da barorin sarki.
12 Ya ƙara da cewa, “Har ma sarauniya Esta ma ba ta yarda kowa ya tafi tare da sarki wurin liyafar da ta shirya ba, sai ni. Gobe ma ta gayyace ni tare da sarki.
13 Duk da haka wannan bai yi mini daɗi ba, muddin Mordekai, Bayahuden nan, yana zaune a ƙofar sarki.”
14 Matarsa, Zeresh kuwa, da abokansa duka suka ce, “Ka sa a shirya gungumen itace mai tsayi kamu hamsin, sa’an nan da safe ka faɗa wa sarki a rataye Mordekai a kai, sa’an nan ka tafi wurin liyafar tare da sarki da murna.”
Haman kuwa ya ji daɗin wannan shawara, sai ya sa aka shirya gungumen itacen.