Haman Ya Fāɗa a Ramin da Ya Haƙa
1 Sarki da Haman kuwa suka tafi wurin Esta, gun liyafa.
2 A rana ta biyu, sa’ad da suke shan ruwan inabi, sai sarki ya sāke ce wa Esta, “Mece ce bukatarki, sarauniya Esta? Za a yi miki. Mene ne roƙonki? Za a ba ki, ko da rabin mulkina ne.”
3 Sai Esta ta ce, “Ya sarki, idan na sami tagomashi a wurinka, idan kuma sarki ya yarda, bukatata ita ce a bar ni da raina, roƙona kuma shi ne a bar mutanena.
4 Gama an sayar da mu, ni da mutanena, don a hallaka mu, a karkashe, a ƙarasa mu. Da a ce an sayar da mu mu zama bayi, mata da maza, da na yi shiru, gama ba za a kwatanta wahalarmu da hasarar da sarki zai sha ba.”
5 Sarki Ahasurus ya ce wa sarauniya Esta, “Wane ne shi, ina yake, wanda zai yi karambanin yin wannan?”
6 Esta ta ce, “Haman ne, magabci, maƙiyi, mugu!”
Sai tsoro ya kama Haman a gaban sarki da sarauniya.
7 Sarki kuwa ya tashi da fushi, ya tafi lambun fāda. Amma Haman ya tsaya don ya roƙi sarauniya Esta ta ceci ransa, gama ya ga sarki yana niyyar hukunta shi.
8 Da sarki ya koma daga lambun fāda zuwa inda suke shan ruwan inabi, sai ga Haman ya fāɗi a kan shimfiɗar da Esta take zaune. Sai sarki ya ce, “Har ma zai ci mutuncin sarauniya a gabana, a gidana?”
Da dai sarki ya faɗi haka, sai bābāni suka cafe Haman.
9 Sa’an nan Harbona, ɗaya daga cikin bābānin da yake yi wa sarki hidima ya ce, “Ga shi ma, Haman ya riga ya shirya gungumen itace a gidansa, mai tsayi kamu hamsin, inda zai rataye Mordekai wanda ya ceci sarki ta wurin maganarsa.”
Sai sarki ya ce, “A rataye Haman a gungumen.”
10 Aka kuwa rataye Haman a gungumen itace da ya shirya zai rataye Mordekai. Sa’an nan sarki ya huce.