Alkawarin da yake Tsakanin Allah da Abram
1 Bayan waɗannan al’amura, maganar Ubangiji ta zo ga Abram cikin wahayi cewa, “Abram, kada ka ji tsoro, ni ne garkuwarka, kana da lada mai yawa.”
2 Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, me za ka ba ni, ga shi kuwa, ba ni da ɗa? Ko kuwa Eliyezer na Dimashƙu ne zai gāje ni?”
3 Abram kuma ya ce, “Ga shi, ba ka ba ni zuriya ba, ga shi ma wani yaron gidana ne zai gāje ni.”
4 Sai ga maganar Ubangiji ta zo gare shi cewa, “Mutumin nan, ba shi zai gāje ka ba, ɗan cikinka shi zai gāje ka.”
5 Sai Ubangiji ya fito da shi waje ya ce, “Ina so ka dubi sararin sama, ka kuma ƙidaya taurari, in kana iya ƙidaya su.” Sai kuma ya ce masa, “Haka zuriyarka za ta zama.”
6 Ya amince da Ubangiji, Ubangiji kuwa ya lasafta wannan adalci ne a gare shi.
7 Ubangiji kuma ya ce masa, “Ni ne Ubangiji wanda ya fisshe ka daga Ur ta Kaldiyawa, don in ba ka wannan ƙasa ka gāje ta.”
8 Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, yaya zan mallake ta?”
9 Ya ce masa, “Kawo mini karsana bana uku, da burguma bana uku, da rago bana uku, da hazbiya da ɗan tattabara.”
10 Ya kawo masa waɗannan abu duka, ya yanyanka su ya tsattsaga su a tsaka, ya ajiye su gab da juna, amma bai tsaga tsuntsayen a tsaka ba.
11 Sa’ad da tsuntsaye masu cin nama suke sauka bisansu sai Abram ya kore su.
12 Sa’ad da rana take faɗuwa, barci mai nauyi ya kwashe Abram, sai ga babban duhu mai bantsoro ya rufe shi.
13 Ubangiji ya ce wa Abram, “Ka sani lalle ne zuriyarka za ta yi baƙunci cikin ƙasar da ba tata ba ce, za ta kuwa yi bauta, za a kuma tsananta mata har shekara arbaminya,
14 amma zan hukunta al’ummar da suka bauta wa, daga baya kuma da dukiya mai yawa za ta fita.
15 Kai kuwa, cikin salama za ka koma ga iyayenka, da kyakkyawan tsufa za a binne ka.
16 A tsara ta huɗu kuma, zuriyar za ta komo nan, domin adadin muguntar Amoriyawa bai cika ya kai iyaka ba tukuna.”
17 Sa’ad da rana ta fāɗi aka kuwa yi duhu, sai ga tanderun wuta mai hayaƙi da jiniya mai harshen wuta suka ratsa tsakanin abubuwan nan da aka tsattsaga a tsaka.
18 A wannan rana Ubangiji ya yi wa Abram alkawari ya ce, “Ga zuriyarka na ba da wannan ƙasa, daga Kogin Masar zuwa babban kogi, wato Kogin Yufiretis ke nan,
19 ƙasar Keniyawa, da Kenizziyawa, da Kadmoniyawa,
20 da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Refayawa,
21 da Amoriyawa, da Kan’aniyawa, da Girgashiyawa, da kuma Yebusiyawa.”