Haihuwar Ishaku
1 Ubangiji ya yi wa Saratu alheri kamar yadda ya alkawarta.
2 Saratu kuwa ta yi ciki, ta haifa wa Ibrahim ɗa cikin tsufansa a lokacin nan da Allah ya faɗa masa.
3 Sai Ibrahim ya raɗa wa ɗansa wanda Saratu ta haifa masa, suna, Ishaku.
4 Ibrahim ya yi wa Ishaku ɗansa kaciya yana da kwana takwas, kamar yadda Allah ya umarce shi.
5 Ibrahim kuwa yana da shekara ɗari sa’ad da aka haifa masa ɗansa Ishaku.
6 Saratu ta ce, “Allah ya sa na yi dariya, har dukan wanda ya ji zai yi dariya tare da ni.”
7 Ta kuma ce, “Dā wa zai iya ce wa Ibrahim Saratu za ta bai wa ‘ya’ya mama? Duk da haka cikin tsufansa na haifa masa ɗa.”
8 Yaron ya yi girma, aka yaye shi, Ibrahim kuwa ya yi babban biki a ranar da aka yaye Ishaku.
Korar Hajaratu da Isma’ilu
9 Amma Saratu ta ga ɗan Hajaratu Bamasariya wanda ta haifa wa Ibrahim yana wasa da ɗanta Ishaku.
10 Sai ta ce wa Ibrahim, “Ka kori wannan baiwa da ɗanta, gama ɗan baiwan nan ba zai zama magaji tare da ɗana Ishaku ba.”
11 Abin ya ɓata wa Ibrahim zuciya ƙwarai sabili da ɗansa.
12 Amma Allah ya ce wa Ibrahim, “Kada zuciyarka ta ɓaci saboda yaron da kuma baiwarka. Kome Saratu ta faɗa maka, ka yi yadda ta ce, gama ta wurin Ishaku za a riƙa kiran zuriyarka.
13 Zan kuma yi al’umma daga ɗan baiwar, domin shi ma zuriyarka ne.”
14 Ibrahim ya tashi da sassafe, ya kuma ɗauki gurasa da salkar ruwa, ya bai wa Hajaratu, ya ɗora kafaɗarta. Sai ya ba ta ɗanta, ya sallame ta. Ta tafi ta yi ta yawo cikin jejin Biyer-sheba.
15 Sa’ad da ruwan salkar ya ƙare, sai ta yar da yaron a ƙarƙashin wani ƙaramin itace.
16 Sai ta tafi, ta zauna ɗaura da shi da ‘yar rata, misalin nisan harbin baka, gama ta ce, “Don kada in ga mutuwar yaron.” Da ta zauna can daura da shi, sai yaron ya ta da muryarsa ya yi ta kuka.
17 Allah kuwa ya ji muryar yaron, mala’ikan Allah kuma ya kira Hajaratu daga sama, ya ce mata, “Me yake damunki, Hajaratu? Kada ki ji tsoro gama Allah ya ji muryar yaron a inda yake.
18 Tashi, ki ɗauki yaron, ki rungume shi da hannunki gama zan maishe shi babbar al’umma.”
19 Sai Allah ya buɗe idanunta, ta ga rijiyar ruwa, ta kuwa tafi, ta cika salkar da ruwa ta ba yaron ya sha.
20 Allah kuwa yana tare da yaron, ya kuwa yi girma, ya zauna a jeji, ya zama riƙaƙƙen maharbi.
21 Ya zauna a jejin Faran. Sai mahaifiyarsa ta auro masa mata daga ƙasar Masar.
Ibrahim da Abimelek suka Ƙulla Yarjejeniya
22 A lokacin nan fa, ya zamana Abimelek, da Fikol shugaban sojojinsa ya zo ya ce wa Ibrahim, “Allah yana tare da kai cikin sha’aninka duka,
23 don haka, yanzu sai ka rantse mini da Allah, cewa ba za ka ci amanata, ko ta ‘ya’yana, ko ta zuriyata ba, amma kamar yadda na riƙe ka cikin mutunci, haka za ka yi da ni da ƙasar da ka yi baƙunta a ciki.”
24 Sai Ibrahim ya amsa, “I, zan rantse.”
25 Sa’ad da Ibrahim ya kawo kuka ga Abimelek a kan rijiyar ruwa wadda barorin Abimelek suka ƙwace,
26 Abimelek ya ce, “Ban san wanda ya yi wannan abu ba, ba ka faɗa mini ba, ban kuwa taɓa ji ba sai yau.”
27 Ibrahim ya ɗibi tumaki da takarkarai ya bai wa Abimelek, su biyu ɗin kuwa suka yi alkawari.
28 Ibrahim ya ware ‘yan raguna bakwai daga cikin garke.
29 Abimelek ya ce wa Ibrahim, “Ina ma’anar waɗannan ‘yan raguna bakwai da ka keɓe?”
30 Ya ce, “Waɗannan ‘yan raguna bakwai za ka karɓe su daga hannuna domin su zama shaida a gare ni, cewa ni na haƙa rijiyan nan.”
31 Don haka aka kira wannan wuri Biyer-sheba, domin a can ne su duka suka yi rantsuwa.
32 Saboda haka suka yi alkawari a Biyer-sheba. Sai Abimelek, tare da Fikol shugaban sojojinsa, ya tashi ya koma ƙasar Filistiyawa.
33 Ibrahim kuma ya dasa itacen tsamiya a Biyer-sheba, a can ya yi kira bisa sunan Ubangiji, Allah Madawwami.
34 Ibrahim kuwa ya daɗe yana baƙunci a ƙasar Filistiyawa.