Sauran Zuriyar Ibrahim
1 Ibrahim ya auro wata mace kuma, sunanta Ketura.
2 Ta haifa masa Zimran, da Yokshan, da Medan, da Madayana, da Yisbak, da Shuwa.
3 Yokshan ya haifi Sheba da Dedan. ‘Ya’yan Dedan su ne Asshurim, da Letushim, da Le’umomim.
4 ‘Ya’yan Madayana su ne Efa, da Efer, da Hanok, da Abida, da Eldaya. Waɗannan duka ‘ya’yan Ketura ne.
5 Ibrahim ya ba Ishaku dukan abin da yake da shi.
6 Amma ga ‘ya’yan ƙwaraƙwarai Ibrahim ya ba da kyautai, ya sallame su tun yana da rai, su tafi nesa da Ishaku zuwa can cikin ƙasar gabas.
Rasuwar Ibrahim da Jana’izarsa
7 Waɗannan su ne kwanakin shekarun Ibrahim a duniya, shekara ɗari da saba’in da biyar.
8 Ibrahim ya ja numfashinsa na ƙarshe ya kuwa rasu cikin kyakkyawan tsufa, tsoho ne mai shekaru masu yawa, aka kai shi ga jama’arsa, waɗanda suka riga shi.
9 Ishaku da Isma’ilu ‘ya’yansa suka binne shi a kogon Makfela a saurar Efron ɗan Zohar Bahitte, gabashin Mamre,
10 wato saurar da Ibrahim ya saya a wurin Hittiyawa. Can ne aka binne Ibrahim gab da Saratu matarsa.
11 Bayan rasuwa Ibrahim, Allah ya sa wa Ishaku ɗansa albarka. Ishaku kuwa ya zauna a Biyer-lahai-royi.
Zuriyar Isma’ilu
12 Waɗannan su ne zuriyar Isma’ilu ɗan Ibrahim, wanda Hajaratu Bamasariya, baranyar Saratu, ta haifa wa Ibrahim.
13 Waɗannan su ne sunayen ‘ya’yan Isma’ilu, maza, bisa ga haihuwarsu. Nebayot ɗan farin Isma’ilu, da Kedar, da Adbeyel, da Mibsam,
14 da Mishma, da Duma, da Massa,
15 da Hadad, da Tema, da Yetur, da Nafish, da Kedema.
16 Waɗannan su ne sunayen ‘ya’yan Isma’ilu, bisa ga ƙauyukansu da zangonsu, hakimai goma sha biyu, bisa ga kabilansu.
17 Waɗannan su ne shekarun Isma’ilu a duniya, shekara ɗari da talatin da bakwai, ya ja numfashinsa na ƙarshe ya rasu, aka kai shi ga jama’arsa waɗanda suka riga shi.
18 Mazauninsa a tsakanin Hawila ne da Shur, wanda yake ɗaura da Masar wajen Assuriya. Suka ware daga danginsu suka yi zamansu.
Haihuwar Isuwa da Yakubu
19 Waɗannan su ne zuriyar Ishaku ɗan Ibrahim, Ibrahim ya haifi Ishaku.
20 Ishaku yana da shekara arba’in sa’ad da ya auri Rifkatu, ‘yar Betuwel Ba’aramiye daga Fadan-aram ‘yar’uwar Laban Ba’aramiye.
21 Ishaku kuwa ya yi addu’a sai matarsa Rifkatu ta yi ciki.
22 ‘Ya’yan kuwa suka kama kokawa da juna a cikinta, har ta ce, “In haka ne don me zan rayu?” Sai ta je ta tambayi Ubangiji.
23 Sai Ubangiji ya ce mata, “Al’umma biyu suke a cikin mahaifarki, mutum biyu da za ki haifa, za su rabu da juna, ɗayan zai fi ɗayan ƙarfi, babban zai bauta wa ƙaramin.”
24 Sa’ad da kwanakin haihuwarta suka cika, sai ga shi, ashe, tagwaye ne suke a cikin mahaifarta.
25 Na farin ya fito ja wur kamar riga mai gashi, saboda haka suka raɗa masa suna Isuwa.
26 Daga baya kuma ɗan’uwansa ya fito, hannunsa na riƙe da diddigen Isuwa, saboda haka aka raɗa masa suna Yakubu. Ishaku yana da shekara sittin sa’ad da ya haife su.
Isuwa ya Sayar da Matsayinsa na Ɗan Fari
27 Sa’ad da yaran suka yi girma, Isuwa ya zama ƙwararren maharbi, ya zama mutumin jeji, Yakubu kuwa kintsattse ne mai son zaman gida.
28 Ishaku ya ƙaunaci Isuwa saboda yakan ci naman da ya farauto, amma Rifkatu ta ƙaunaci Yakubu.
29 Wata rana, sa’ad da Yakubu yake dafa fate, Isuwa ya komo daga jeji, yana jin yunwa ƙwarai.
30 Sai Isuwa ya ce wa Yakubu, “Ka ɗibar mini jan fatenka in sha, gama ina fama da yunwa!” Saboda haka aka kira sunansa Edom.
31 Yakubu ya ce, “Sai dai ko in yau za ka sayar mini da matsayinka na ɗan fari.”
32 Sai Isuwa ya ce, “Ni da nake bakin mutuwa, wane amfani matsayina na ɗan fari zai yi mini?”
33 Yakubu ya ce, “Yau sai ka rantse mini.” Sai ya rantse masa ya kuwa sayar wa Yakubu da matsayinsa na ɗan fari.
34 Sa’an nan Yakubu ya ba Isuwa gurasa da faten wake, ya ci ya sha, ya tashi ya yi tafiyarsa. Ta haka Isuwa ya banzatar da matsayinsa na ɗan fari.