1 Sa’ad da Rahila ta ga ba ta haihuwa, sai ta ji kishin ‘yar’uwarta, ta kuma ce wa Yakubu, “Ka ba ni ‘ya’ya, in kuwa ba haka ba, zan mutu!”
2 Fushin Yakubu ya yi ƙuna a kan Rahila, ya ce, “Ina daidai da Allah ne, wanda ya hana ki haihuwa?.”
3 Sai ta ce, “Ga kuyangata Bilha, ka shiga wurinta, domin ta haihu bisa gwiwoyina, domin ni ma in sami ‘ya’ya ta wurinta.”
4 Don haka ta ba shi Bilha ta zama matarsa. Yakubu kuwa ya shiga wurinta.
5 Bilha kuwa ta yi ciki, ta haifa wa Yakubu ɗa.
6 Rahila ta ce, “Allah ya baratar da ni, ya ji muryata, ya kuwa ba ni ɗa.” Saboda haka ta raɗa masa suna Dan.
7 Bilha, kuyangar Rahila, ta sāke yin ciki, ta haifa wa Yakubu ɗa na biyu.
8 Sai Rahila ta ce, “Da gawurtacciyar kokawa na yi kokawa da ‘yar’uwata, har na yi rinjaye,” sai ta raɗa masa suna Naftali.
9 Sa’ad da Lai’atu ta ga ta daina haihuwa, sai ta ɗauki kuyangarta Zilfa, ta ba Yakubu ta zama matarsa.
10 Kuyangar Lai’atu, Zilfa, ta haifa wa Yakubu ɗa.
11 Lai’atu kuma ta ce, “Sa’a!” Saboda haka ta sa masa suna Gad.
12 Kuyangar Lai’atu ta sāke haifa wa Yakubu ɗa na biyu.
13 Lai’atu ta ce, “Ni mai farin ciki ce! Gama mata za su ce da ni mai farin ciki,” saboda haka ta raɗa masa suna Ashiru.
14 A kwanakin kakar alkama, Ra’ubainu ya fita ya samo manta uwa a saura, ya kawo wa mahaifiyarsa Lai’atu. Sai Rahila ta ce wa Lai’atu, “Ina roƙonki, ɗiba mini daga cikin manta uwar da ɗanki ya samo.”
15 Amma ta ce mata, “Kanƙanen abu ne da kika ƙwace mini mijina? Za ki kuma ƙwace manta uwar da ɗana ya samo kuma?”
Rahila ta ce, “To, in haka ne, bari ya kwana tare da ke a daren yau a maimakon manta uwar da ɗanki ya samo.”
16 Sa’ad da Yakubu ya komo daga saura da maraice, Lai’atu ta fita ta tarye shi, ta ce, “Sai ka shigo wurina, gama na riga na ijarar da kai da manta uwar da ɗana ya samo.” Saboda haka ya kwana tare da ita a daren nan.
17 Allah ya saurari Lai’atu, ta kuwa yi ciki ta haifa wa Yakubu ɗa na biyar.
18 Lai’atu ta ce, “Allah ya yi mini sakamako domin na ba da kuyangata ga mijina,” saboda haka ta raɗa masa suna Issaka.
19 Lai’atu ta sāke yin ciki ta kuwa haifa wa Yakubu ɗa na shida.
20 Sai Lai’atu ta ce, “Allah ya wadata ni da kyakkyawar baiwa, yanzu mijina zai darajanta ni, domin na haifa masa ‘ya’ya maza shida,” ta raɗa masa suna Zabaluna.
21 Daga baya ta haifi ‘ya mace, ta kuwa raɗa mata suna Dinatu.
22 Allah kuwa ya tuna da Rahila, ya saurare ta, ya buɗe mahaifarta.
23 Ta yi ciki ta haifa ɗa, ta ce, “Allah ya kawar da zargina,”
24 ta sa masa suna Yusufu, tana cewa, “Da ma a ce Ubangiji ya ƙara mini wani ɗa!”
Yakubu Ya Yi Jinga da Laban
25 Bayan da Rahila ta haifi Yusufu, Yakubu ya ce wa Laban, “Ka sallame mu, domin mu tafi gidanmu a ƙasarmu.
26 Ka ba ni matana da ‘ya’yana waɗanda na yi maka barantaka saboda su, ka bar mu mu tafi, ka dai san ɗawainiyar da na yi maka.”
27 Amma Laban ya ce masa, “Da za ka yarda mini, sai in ce, na fahimta bisa ga istihara, cewa Ubangiji ya sa mini albarka saboda kai.
28 Ka faɗa mini ladanka in ba ka.”
29 Yakubu ya ce masa, “Kai da kanka ka san barantakar da na yi maka, yadda bisashenka suka yawaita a hannuna.
30 Gama kafin in zo, kana da ‘yan kima ne, ga shi, sun ƙaru da yawa, Ubangiji kuwa ya sa maka albarka duk inda na juya. Amma yanzu, sai yaushe zan hidimta wa nawa gidan?”
31 Ya ce, “Me zan ba ka?”
Yakubu ya ce, “Ba za ka ba ni kome ba, in da za ka yi mini wannan, sai in sāke kiwon garkenka in lura da shi,
32 bar ni, in ratsa garkenka duka yau, in keɓe dukan masu dabbare-dabbare da tumaki babare-babare, da kowane ɗan rago baƙi, da dabbare-dabbare da babare-babare na awaki, waɗannan ne za su zama ladana.
33 Ta haka amincina zai shaide ni a gabanka a sa’ad da ka zo bincike hakkina. Duk wanda aka iske ba dabbare-dabbare ba ne, kuma ba babare-babare ba ne cikin awaki, ba kuma baƙi ba ne a cikin raguna, in aka samu a wurina, sai a ɗauka, na sata ne.”
34 Laban ya ce, “Madalla! Bari ya kasance kamar yadda ka faɗa.”
35 Amma a ran nan Laban ya ware bunsuran da suke dabbare-dabbare da masu sofane, da dukan awakin da suke dabbare-dabbare da kyalloli, da dukan baƙaƙen tumaki, ya danƙa su a hannun ‘ya’yansa maza,
36 ya sa nisan tafiya ta kwana uku tsakaninsu da Yakubu, Yakubu kuma ya ci gaba da kiwon sauran garken Laban.
37 Yakubu ya samo ɗanyun tsabgogin aduruku, da na katambiri, da na durumi, ya ɓare ya bayyanar da fararen zane-zanensu a fili.
38 Ya kafa tsabgogin da ya ɓare a gaban garkuna a magudana, wato kwamame na banruwa, don sukan yi barbara a wurin sa’ad da suka zo shan ruwa.
39 Garkunan suka yi barbara a gaban tsabgogin, don haka garkunan sukan haifi masu zāne, dabbare-dabbare da masu sofane.
40 Yakubu kuwa ya keɓe ‘yan raguna, ya sa garkuna su fuskanci tsabgogin da ya shasshauta, da dukan baƙaƙen da suke cikin garken Laban. Sai ya ware waɗanda suke nasa, bai kuwa haɗa su da garken Laban ba.
41 A kowane lokacin da ƙarfafan yake barbara Yakubu yakan sa tsabgogin a magudana a gaban idanun garken, domin su yi barbara a tsakanin tsabgogin.
42 Amma ga marasa ƙarfi na garken, ba ya sa musu. Don haka marasa ƙarfin ne na Laban, ƙarfafan kuwa na Yakubu.
43 Ta haka mutumin ya zama riƙaƙƙen mai arziki, yana da manya manyan garkuna da barori mata da maza, da raƙuma, da jakuna.