Allah ya Sa wa Yakubu Albarka a Betel
1 Allah ya ce wa Yakubu, “Tashi, ka hau zuwa Betel, ka zauna can. Can za ka gina bagade ga Allah wanda ya bayyana gare ka sa’ad da kake guje wa ɗan’uwanka Isuwa.”
2 Sai Yakubu ya ce wa iyalin gidansa da dukan waɗanda suke tare da shi, “Ku kawar da gumakan da suke wurinku, ku tsarkake kanku, ku sāke rigunanku,
3 sa’an nan mu tashi mu haura zuwa Betel, domin in kafa bagade ga Allah wanda ya taimake ni a kwanakin ƙuncina, wanda kuwa yake tare da ni duk inda na tafi.”
4 Saboda haka, suka bai wa Yakubu dukan gumakan da suke da su, da zobban kunnuwansu. Sai Yakubu ya ɓoye su a ƙarƙashin itacen oak wanda suke kusa da Shekem.
5 Da suna cikin tafiya, razana daga Allah ta fāɗa wa biranen da suke kewaye da su, har ba wanda ya iya bin ‘ya’yan Yakubu.
6 Sai Yakubu ya zo Luz, wato Betel, wadda take cikin Kan’ana, shi da dukan mutanen da suke tare da shi.
7 A nan ya gina bagade, ya sa wa wurin suna El-betel, domin a nan Allah ya bayyana kansa gare shi sa’ad da yake guje wa ɗan’uwansa.
8 Can Debora, ungozomar Rifkatu ta rasu, aka kuwa binne ta a gangaren Betel, a ƙarƙashin itacen oak, don haka ana kiran wurin, Allon-bakut.
9 Allah kuma ya sāke bayyana ga Yakubu a lokacin da ya komo daga Fadan-aram, ya sa masa albarka.
10 Allah kuwa ya ce masa, “Sunanka Yakubu ne, amma nan gaba ba za a ƙara kiran sunanka Yakubu ba, sai Isra’ila.” Don haka aka kira sunansa Isra’ila.
11 Allah ya ce masa, “Ni ne Allah Maɗaukaki, ka hayayyafa ka riɓaɓɓanya, al’umma da tattaruwar al’ummai za su bumbunto daga gare ka, sarakuna kuma za su fito daga cikinka.
12 Na ba ka ƙasar da na ba Ibrahim da Ishaku, zan kuma ba da ita ga zuriyarka a bayanka.”
13 Sa’an nan Allah ya tashi Sama ya bar shi a wurin da ya yi masa magana.
14 Sai Yakubu ya kafa al’amudin dutse a inda Allah ya yi masa magana, ya zuba masa sadaka ta sha, ya kuma zuba mai a bisansa.
15 Yakubu ya kira sunan wurin da Allah ya yi magana da shi, Betel.
Rasuwar Rahila
16 Da suka tashi daga Betel, tun suna da ‘yar rata da Efrata, sai lokaci ya yi da Rahila za ta haihu, amma ta sha wahala kafin ta haihu.
17 Sa’ad da take cikin naƙudarta, sai ungozoma ta ce mata, “Kada ki ji tsoro, gama yanzu kin sami wani ɗa.”
18 Da tana suma, sai ta sa masa suna Ben-oni, amma mahaifinsa ya sa masa suna Biliyaminu.
19 Ta haka fa Rahila ta rasu, aka kuwa binne ta a bakin hanya zuwa Efrata, wato Baitalami.
20 Yakubu ya kafa al’amudi bisa kabarinta, al’amudin kabarin Rahila ke nan, wanda yake can har wa yau.
21 Isra’ila ya ci gaba da tafiyarsa, ya kuwa kafa alfarwarsa daura da hasumiyar Eder.
‘Ya’yan Yakubu Maza
22 A lokacin da Isra’ila yake zaune a ƙasar, Ra’ubainu ya je ya kwana da Bilha kwarkwarar mahaifinsa, Isra’ila kuwa ya sami labari.
‘Ya’yan Isra’ila, maza, su goma sha biyu ne.
23 ‘Ya’yan Lai’atu, su ne Ra’ubainu ɗan farin Yakubu, da Saminu, da Lawi, da Yahuza, da Issaka, da Zabaluna.
24 ‘Ya’yan Rahila, su ne Yusufu da Biliyaminu.
25 ‘Ya’yan Bilha, kuyangar Rahila, su ne Dan da Naftali.
26 ‘Ya’yan Zilfa, kuyangar Lai’atu, su ne Gad da Ashiru. Waɗannan su ne ‘ya’yan Yakubu da aka haifa masa a Fadan-aram.
Rasuwar Ishaku
27 Yakubu kuma ya zo wurin mahaifinsa a Mamre, a Kiriyat-arba, wato Hebron ke nan, inda Ibrahim da Ishaku suka yi baƙunci.
28 Yanzu kuwa kwanakin Ishaku shekara ce ɗari da tamanin.
29 Sai Ishaku ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya rasu, aka kuwa kai shi ga jama’arsa waɗanda suka riga shi, da kyakkyawan tsufa cike da kwanaki, ‘ya’yansa Isuwa da Yakubu suka binne shi.