Kayinu da Habila
1 Adamu kuwa ya san matarsa Hawwa’u, ta kuwa yi ciki, ta haifi Kayinu. Sai ta ce, “Na sami ɗa namiji da iznin Ubangiji.”
2 Ta kuma haifi ɗan’uwansa Habila. Habila makiyayin tumaki ne, Kayinu kuwa manomi ne.
3 Wata rana, sai Kayinu ya kawo sadaka ga Ubangiji daga amfanin gona.
4 Habila kuwa ya kawo nasa ƙosassu daga cikin ‘ya’yan fari na garkensa. Ubangiji kuwa ya kula da Habila da sadakarsa,
5 amma Kayinu da sadakarsa, bai kula da su ba. Saboda haka Kayinu ya husata ƙwarai, har tsikar jikinsa ta tashi.
6 Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Me ya sa ka husata, me kuma ya sa har tsikar jikinka ta tashi?
7 In da ka yi daidai, ai, da ka yi murmushi. Amma tun da ka yi mugunta, to, zunubi zai yi fakonka don ya rinjaye ka kamar naman jeji. Yana so ya mallake ka, amma tilas ne ka rinjaye shi.”
8 Kayinu ya ce wa ɗan’uwansa Habila, “Mu tafi cikin saura.” A lokacin da suke cikin saura, sai Kayinu ya tasar wa ɗan’uwansa Habila, har ya kashe shi.
9 Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Ina Habila ɗan’uwanka?”
Ya ce, “Ban sani ba, ni makiyayin ɗan’uwana ne?”
10 Sai Ubangiji ya ce, “Me ke nan ka yi? Muryar jinin ɗan’uwanka tana yi mini kuka daga ƙasa.
11 Yanzu fa, kai la’ananne ne daga cikin ƙasar da ta buɗe baki, ta karɓi jinin ɗan’uwanka daga hannunka.
12 In ka yi noma, ƙasar ba za ta ƙara ba ka cikakken amfaninta ba, za ka zama mai yawo barkatai, mai kai da kawowa a duniya.”
13 Kayinu ya ce wa Ubangiji, “Hukuncina ya fi ƙarfina.
14 Ga shi, yanzu ka kore ni a guje daga fuskar ƙasar, zan zama a ɓoye daga fuskarka, zan kuma zama mai yawo barkatai, mai kai da kawowa a duniya, duk wanda ya same ni kuwa zai kashe ni.”
15 Sai Ubangiji ya ce masa, “Ba haka ba ne! Wanda duk ya kashe Kayinu, za a rama masa har sau bakwai.” Ubangiji kuma ya sa wa Kayinu tabo, domin duk wanda ya iske shi kada ya kashe shi.
16 Kayinu ya yi tafiyarsa ya rabu da Ubangiji, ya zauna a ƙasar Nod, gabashin Aidan.
Zuriyar Kayinu
17 Kayinu ya san matarsa, ta kuwa yi ciki ta haifi Anuhu, ya kuwa gina birni ya sa wa birnin sunan ɗansa, Anuhu.
18 An haifa wa Anuhu ɗa, wato Airad. Airad ya haifi Mehuyayel, Mehuyayel kuwa ya haifi Metushayel, Metushayel kuma ya haifi Lamek.
19 Lamek ya auri mata biyu, sunan ɗayar Ada, ta biyun kuwa Zulai.
20 Ada ta haifi Yabal, shi ne ya zama uban mazaunan alfarwa, makiyayan dabbobi.
21 Sunan ɗan’uwansa Yubal, wanda ya zama uban makaɗan garaya da mabusan sarewa.
22 Zulai kuwa ta haifi Tubal-kayinu, shi ne asalin maƙeran dukan kayayyakin tagulla da na baƙin ƙarfe. Sunan ‘yar’uwar Tubalkayinu Na’ama ne.
23 Lamek kuwa ya ce wa matansa, “Ada da Zulai, ku ji muryata, ku matan Lamek ku ji abin da nake cewa na kashe mutum domin ya yi mini rauni, saurayi kuma don ya buge ni.
24 Idan an rama wa Kayinu sau bakwai, hakika na Lamek, sai sau saba’in da bakwai.”
Zuriyar Shitu
25 Sai kuma Adamu ya san matarsa, ta kuwa haifi ɗa, ta raɗa masa suna Shitu, gama ta ce, “Allah ya arzuta ni da ɗa maimakon Habila wanda Kayinu ya kashe.”
26 Ga Shitu kuma aka haifi ɗa, ya kuwa raɗa masa suna Enosh. A wannan lokaci ne mutane suka fara kira bisa sunan Ubangiji.