Yusufu Ya Fassara Mafarkan ‘Yan Kurkuku
1 Bayan waɗannan al’amura, sai mai shayarwa da mai tuya na Sarkin Masar suka yi wa maigidansu Sarkin Masar laifi.
2 Fir’auna ya yi fushi da ma’aikatan nan nasa biyu, wato shugaban masu shayarwa da shugaban masu tuya.
3 Ya ba da su a sa su kurkuku, cikin gidan shugaban masu tsaron fāda, wato kurkuku inda Yusufu yake a tsare.
4 Shugaban ‘yan tsaron ya danƙa su ga Yusufu don ya hidimta musu, sun kuwa jima a kurkukun har an daɗe.
5 Suka yi mafarki, su biyu ɗin, a dare ɗaya, da shi mai shayarwar da mai tuyar na gidan Sarkin Masar, waɗanda aka sa a kurkuku, kowanne kuwa da nasa mafarkin da kuma tasa irin fassarar mafarkin.
6 Da Yusufu ya zo wurinsu da safe, ya ga sun damu.
7 Sai ya tambaye su ya ce, “Me ya sa fuskokinku suke a yamutse yau?”
8 Suka ce masa, “Mafarkai muka yi, ba kuma wanda zai fassara mana su.”
Sai Yusufu ya ce musu, “Ashe, ba a wurin Allah fassarori suke ba? Ku faɗa mini su, ina roƙonku.”
9 Saboda haka, shugaban masu shayarwa ya faɗa wa Yusufu mafarkinsa, ya ce masa, “A mafarkina ga kurangar inabi a gabana.
10 A kurangar akwai rassa uku. Sai ta yi toho, ta huda nan da nan, ta kuma yi nonna, har suka nuna suka zama inabi.
11 Finjalin Fir’auna na hannuna, sai na ɗauki ‘ya’yan inabi na matse su cikin finjalin Fir’auna, na sa finjalin a hannun Fir’auna.”
12 Yusufu ya ce masa, “Wannan ita ce fassararsa, rassan nan uku, kwana uku ne,
13 bayan kwana uku Fir’auna zai ɗaukaka ka, ya komar da kai matsayinka, za ka kuma sa finjalin Fir’auna a hannunsa kamar dā lokacin da kake mai hidimar shayarwarsa.
14 Amma ka tuna da ni sa’ad da abin ya tabbata gare ka, sai ka yi mini alheri, ka ambace ni a wurin Fir’auna, har da za a fisshe ni daga wannan gida.
15 Gama ni, hakika sato ni aka yi daga ƙasar Ibraniyawa. A nan kuma ban yi wani abin da zai isa a sa ni a kurkuku ba.”
16 Sa’ad da shugaban masu tuya ya ga fassarar tana da kyau, sai ya ce wa Yusufu, “Ni ma cikin nawa mafarki, na ga kwanduna uku na waina a bisa kaina.
17 A kwandon da yake bisa ɗin akwai toye-toye iri iri domin Fir’auna, amma ga tsuntsaye suna ta ci daga cikin kwandon da yake bisa duka, wato wanda yake bisa kaina ɗin.”
18 Yusufu ya amsa, “Wannan ita ce fassararsa, kwandunan uku, kwana uku ne,
19 bayan kwana uku Fir’auna zai falle kanka ya rataye ka a bisa itace, tsuntsaye kuwa za su ci naman jikinka.”
20 A rana ta uku, wadda take ranar haihuwar Fir’auna, Fir’auna ya yi wa dukan bayinsa biki, sai ya kawo shugaban masu shayarwa da shugaban masu tuya a gaban fādawansa.
21 Ya komar da shugaban masu shayarwa a matsayinsa na shayarwa, ya kuwa miƙa finjali a hannun Fir’auna,
22 amma ya rataye shugaban masu tuya kamar yadda Yusufu ya fassara musu.
23 Duk da haka shugaban masu shayarwar bai tuna da Yusufu ba, amma ya manta da shi.