Yusufu Ya Fassara wa Fir’auna Mafarkansa
1 Bayan shekaru biyu cif, Fir’auna ma ya yi mafarki, ga shi, yana tsaye a bakin kogin Nilu,
2 sai ga shanu bakwai masu ƙiba mulmul suka fito daga Nilu, suka yi kiwo cikin iwa.
3 Ga kuma waɗansu shanu bakwai munana ramammu suka fito daga cikin Nilu a bayansu, suka tsaya kusa da waɗancan shanu a bakin Nilu.
4 Sai shanun nan munana ramammu suka cinye shanun nan bakwai masu sheƙi, masu ƙibar. Sai Fir’auna ya farka.
5 Barci kuma ya kwashe shi, ya sāke yin mafarki a karo na biyu, sai zangarku bakwai masu kauri kyawawa suna girma a kara gudu.
6 Ga shi kuma, a bayansu waɗansu zangarku bakwai suka fito sirara waɗanda iskar gabas ta ƙeƙasar.
7 Sai siraran zangarkun suka haɗiye zangarkun nan bakwai masu kauri kyawawa. Sai Fir’auna ya farka, ashe, mafarki ne.
8 Saboda haka da safe, hankalinsa ya tashi, sai ya aika aka kirawo dukan bokayen Masar da dukan masu hikimar Masar, Fir’auna kuwa ya faɗa musu mafarkansa, amma ba wanda ya iya fassara masa su.
9 Sai shugaban masu shayarwa ya ce wa Fir’auna, “Yau, na tuna da laifofina.
10 Sa’ad da ka yi fushi da barorinka, ka sa ni da shugaban masu tuya cikin kurkukun da yake a cikin gidan shugaban masu tsaron fāda,
11 muka yi mafarki dare ɗaya, ni da shi, kowane mutum da irin tasa fassarar mafarkin.
12 Akwai wani Ba’ibrane, ɗan saurayi, tare da mu, bawan shugaban masu tsaron fāda, sa’ad da muka faɗa masa sai ya fassara mana mafarkanmu, ya yi wa kowannenmu fassara bisa kan mafarkinsa.
13 Yadda ya fassara mana haka kuwa ya zama, aka komar da ni matsayina, mai tuya kuwa aka rataye shi.”
14 Sai Fir’auna ya aika a kirawo Yusufu, da gaggawa suka fito da shi daga cikin kurkuku. Da Yusufu ya yi aski, ya sāke tufafinsa ya zo gaban Fir’auna.
15 Fir’auna kuwa ya ce wa Yusufu, “Na yi mafarkin da ba wanda ya san fassararsa, amma na ji an ce, wai kai, in ka ji mafarkin kana iya fassara shi.”
16 Yusufu ya amsa wa Fir’auna ya ce, “Ba a gare ni ba, Allah zai amsa wa Fir’auna da kyakkyawar amsa.”
17 Fir’auna ya ce wa Yusufu, “Ga shi, a cikin mafarkina ina tsaye a bakin Kogin Nilu,
18 ga shanu bakwai, masu sheƙi masu ƙiba suka fito daga cikin Nilu suna kiwo cikin iwa.
19 Sai waɗansu shanu bakwai ƙanjamammu, munana, ramammu, irin waɗanda ban taɓa ganinsu a ƙasar Masar ba, suka fito bayansu.
20 Sai ramammun, munanan shanun suka cinye shanun nan bakwai masu ƙiba na farko,
21 amma da suka haɗiye su, ba wanda zai iya sani sun haɗiye su, gama suna nan a ramammunsu kamar yadda suke a dā. Sai na farka.
22 Har yanzu kuma, a cikin mafarkina ga zangarku masu kauri kyawawa guda bakwai, suna girma a kara guda,
23 zangarku bakwai kuma busassu sirara waɗanda iskar gabas ta ƙeƙasar, suka fito a bayansu.
24 Siraran zangarkun kuwa suka haɗiye zangarkun nan bakwai kyawawa masu kauri. Na faɗa wa bokaye, amma ba wanda ya iya yi mini fassararsa.”
25 Yusufu ya ce wa Fir’auna, “Mafarkin Fir’auna ɗaya ne, Allah ya bayyana wa Fir’auna abin da yake shirin aikatawa.
26 Waɗannan shanu bakwai, shekaru bakwai ne, kyawawan zangarkun nan bakwai kuma shekaru bakwai ne, mafarkin ɗaya ne.
27 Ramammun shanun nan bakwai da suka fito a bayansu shekaru bakwai ne, busassun zangarkun nan bakwai waɗanda iskar gabas ta ƙeƙasar kuwa, shekaru bakwai ne na yunwa.
28 Haka yake kamar yadda na faɗa wa Fir’auna, Allah ya nuna wa Fir’auna abin da yake shirin aikatawa.
29 Za a yi shekara bakwai cike da ƙoshi a ƙasar Masar duka,
30 amma a bayansu za a yi shekara bakwai na yunwa, amma za a manta da dukan ƙoshin nan a ƙasar Masar, yunwar kuwa za ta game dukan ƙasar.
31 Zai kuwa zama kamar ba a taɓa yin ƙoshi a ƙasar ba, saboda tsananin yunwar.
32 Maimaitawar mafarkin nan na Fir’auna kuwa, ya nuna cewa Allah ya riga ya ƙaddara al’amarin, hakika kuwa Allah zai tabbatar da shi ba da jimawa ba.
33 “Yanzu fa bari Fir’auna ya zaɓi mutum mai basira, mai hikima, ya sa shi bisa ƙasar Masar.
34 Bari Fir’auna ya ci gaba da naɗa shugabanni bisa ƙasa, don su tattara humushin amfanin ƙasar Masar na shekarun nan bakwai na ƙoshi.
35 Bari kuma su tattara dukan abinci a shekarun nan bakwai masu zuwa na albarka, su tsiba a ƙarƙashin ikon Fir’auna saboda abinci cikin birane, su kuma lura da shi.
36 Wannan abinci zai zama ajiya domin ƙasar, kariyar shekaru bakwai na yunwa, waɗanda za a yi cikin ƙasar Masar, domin kada ƙasar ta ƙare saboda yunwar.”
An Naɗa Yusufu Mai Mulki a Masar
37 Fir’auna da fādawansa duka sun yarda da wannan shawara.
38 Sai Fir’auna ya ce wa fādawansa, “Mā iya samun mutum irin wannan, wanda Ruhun Allah yake cikinsa?”
39 Domin haka Fir’auna ya ce wa Yusufu, “Tun da yake Allah ya nuna maka waɗannan abu duka, ba wani mai basira da hikima kamarka,
40 za ka shugabanci gidana, bisa ga cewarka za a mallaki jama’ata, sai dai da sarauta kaɗai nake gaba da kai.”
41 Fir’auna ya ce wa Yusufu, “Ga shi, na sa ka bisa dukan ƙasar Masar.”
42 Sai Fir’auna ya cire zobensa mai hatimi daga hannunsa ya sa a hannun Yusufu, ya sa masa rigunan lilin masu kyau, ya rataya masa sarƙar zinariya a wuya,
43 ya kuma sa shi ya hau karusarsa ta biyu, suka yi ta shela a gabansa, “Ku ba da hanya.” Ta haka fa ya sa ya zama mai mulki bisa dukan ƙasar Masar.
44 Har yanzu dai Fir’auna ya ce wa Yusufu, “Ni ne Fir’auna, ba mutumin da zai ɗaga hannu ko ƙafa cikin dukan ƙasar Masar idan ba da izninka ba.”
45 Fir’auna kuwa ya sa wa Yusufu suna, Zafenat-faneya. Ya kuma aurar masa da Asenat ‘yar Fotifera, firist na On. Yusufu kuwa ya fita rangadin ƙasar Masar.
46 Yusufu yana da shekara talatin lokacin da ya kama aiki a wurin Fir’auna, Sarkin Masar. Yusufu kuwa ya fita daga gaban Fir’auna ya ratsa dukan ƙasar Masar.
47 A cikin shekaru bakwai ɗin nan na ƙoshi, ƙasa ta ba da amfani mai yawan gaske,
48 sai ya tattara dukan abinci na shekarun nan bakwai da aka yi na ƙoshi a ƙasar Masar, ya kuwa tanada abinci cikin birane, a kowane birni ya tanada abinci daga karkarar da take kewaye da shi.
49 Sai Yusufu ya tsiba tsaba kamar yashin teku, har ya daina aunawa domin ba ta aunuwa saboda yawa.
50 Kafin kuwa shekarun nan na yunwa, an haifa wa Yusufu ‘ya’ya biyu maza, waɗanda Asenat ‘yar Fotifera, firist na On ta haifa masa.
51 Yusufu ya raɗa wa ɗan farin suna, Manassa, yana cewa, “Gama Allah ya sa ni in manta da dukan wahalata da dukan gidan mahaifina.”
52 Na biyun kuma ya raɗa masa suna, Ifraimu, yana cewa, “Gama Allah ya wadata ni a cikin ƙasar wulakancina.”
53 Shekarun nan bakwai na ƙoshi da aka yi cikin ƙasar Masar sun cika,
54 aka fara shekaru bakwai na yunwa kamar yadda Yusufu ya faɗa. Sai aka yi yunwa cikin sauran ƙasashe duka, amma a ƙasar Masar akwai abinci.
55 Sa’ad da yunwa ta game dukan ƙasar, mutanen suka yi wa Fir’auna kuka domin abinci, sai Fir’auna ya faɗa wa Masarawa duka, ya ce, “Ku tafi wurin Yusufu, abin da duk ya faɗa muku, sai ku yi.”
56 Domin haka sa’ad da yunwar ta bazu ko’ina a ƙasar, Yusufu ya buɗe taskokin ajiya, ya yi ta sayar wa Masarawa, gama yunwa ta tsananta a ƙasar.
57 Duniya duka kuwa ta zo Masar wurin Yusufu, ta sayi hatsi saboda yunwa ta tsananta a duniya duka.