Yakubu da Iyalinsa suka Tafi Masar
1 Isra’ila ya kama tafiyarsa da dukan abin da yake da shi. Ya zo Biyer-sheba, ya kuwa ba da hadayu ga Allah na mahaifinsa Ishaku.
2 Sai Allah ya yi magana cikin wahayin dare, ya ce, “Yakubu.”
Ya amsa ya ce, “Na’am.”
3 Sai ya ce, “Ni ne Allah, Allah na mahaifinka, kada ka ji tsoron zuwa Masar, gama a can zan maishe ka babbar al’umma.
4 Ni kuwa zan gangara tare da kai zuwa Masar, ni kuma zan sāke haurowa tare da kai. Lokacin mutuwarka za ka mutu a hannun Yusufu.”
5 Sai Yakubu ya tashi daga Biyer-sheba, ‘ya’yan Isra’ila maza kuwa suka ɗauki mahaifinsu Yakubu, da ‘yan ƙananansu da matansu a cikin kekunan shanun da Fir’auna ya aika a ɗauko su.
6 Suka kuma kora shanunsu, suka ɗauki kayayyakinsu waɗanda suka samu a ƙasar Kan’ana, suka iso Masar, Yakubu da zuriyarsa duka,
7 ‘ya’yansa maza da jikokinsa maza tare da shi, ‘ya’yansa mata, da jikokinsa mata, ya kawo zuriyarsa dukka zuwa ƙasar Masar.
8 Waɗannan su ne sunayen ‘ya’ya maza na Isra’ila, wato Yakubu, waɗanda suka iso Masar. Ra’ubainu, ɗan farin Yakubu.
9 ‘Ya’yan Ra’ubainu, maza kuwa, su ne Hanok, da Fallu, da Hesruna, da Karmi.
10 ‘Ya’yan Saminu, maza, su ne Yemuwel, da Yamin, da Ohad, da Yakin, da Zohar, da Shawul ɗan wata Bakan’aniya.
11 ‘Ya’yan Lawi, maza, su ne Gershon, da Kohat, da Merari.
12 ‘Ya’yan Yahuza, maza, su ne Er, da Onan, da Shela, da Feresa, da Zera, (amma Er da Onan suka rasu a ƙasar Kan’ana). ‘Ya’yan Feresa, maza kuwa, su ne Hesruna da Hamul.
13 ‘Ya’yan Issaka, maza, su ne Tola, da Fuwa, da Yashub, da Shimron.
14 ‘Ya’yan Zabaluna, maza, su ne Sered, da Elon, da Yaleyel,
15 (waɗannan su ne ‘ya’yan Lai’atu, maza, waɗanda ta haifa wa Yakubu cikin Fadan-aram, da ‘ya tasa kuma Dinatu, ‘ya’yansa mata da maza duka, mutum talatin da uku ne).
16 ‘Ya’yan Gad, maza, su ne Zifiyon, da Haggi, da Shuni, da Ezbon, da Eri, da Arodi, da Areli.
17 ‘Ya’yan Ashiru, maza, su ne Yimna, da Yishuwa, da Yishwi, da Beriya, da Sera, ‘yar’uwarsu. ‘Ya’yan Beriya, maza kuma, su ne Eber da Malkiyel.
18 Waɗannan su goma sha shida, su ne zuriyar Yakubu, maza, na wajen Zilfa, wadda Laban ya bai wa Lai’atu, ‘yarsa.
19 ‘Ya’ya maza, na Rahila, matar Yakubu, su ne Yusufu da Biliyaminu.
20 Asenat ‘yar Fotifera, firist na On, ta haifa wa Yusufu Manassa da Ifraimu a ƙasar Masar.
21 ‘Ya’yan Biliyaminu, maza, su ne Bela, da Beker, da Ashbel, da Gera, da Na’aman, da Ahiram, da Rosh, da Muffim, da Huffim, da Adar.
22 Waɗannan su goma sha huɗu su ne zuriyar Yakubu, maza, na wajen Rahila.
23 Hushim shi ne ɗan Dan.
24 ‘Ya’yan Naftali, maza, su ne Yazeyel, da Guni, da Yezer, da Shallum.
25 Waɗannan su bakwai, su ne zuriyar Yakubu, maza, na wajen Bilha, wadda Laban ya bai wa ‘yarsa Rahila.
26 Mutanen Yakubu dukka da suka shiga Masar, waɗanda suke zuriyarsa ne, banda matan ‘ya’yansa, su mutum sittin da shida ne.
27 ‘Ya’yan Yusufu, maza, waɗanda aka haifa masa a Masar su biyu ne. Dukkan mutane na gidan Yakubu da suka zo Masar su saba’in.
Yakubu da Iyalinsa a Masar
28 Isra’ila kuwa ya aiki Yahuza ya yi gaba zuwa wurin Yusufu ya faɗa masa ya sadu da shi a nuna masa Goshen. Da suka zo ƙasar Goshen,
29 sai Yusufu ya kintsa karusarsa ya haura zuwa Goshen don ya taryi Isra’ila, mahaifinsa. Nan da nan da isowarsa wurinsa, ya rungume shi, ya jima yana ta kuka a kafaɗarsa.
30 Isra’ila ya ce wa Yusufu, “To, bari in mutu yanzu, tun da na ga fuskarka na sani kuma kana da rai har yanzu.”
31 Yusufu ya ce wa ‘yan’uwansa da iyalin gidan mahaifinsa, “Zan tafi in faɗa wa Fir’auna, in ce masa, ‘’yan’uwana da iyalin gidan mahaifina, waɗanda dā yake a ƙasar Kan’ana, sun zo wurina,)
32 mutanen kuwa makiyaya ne, sun kuwa zo da garkunansu na awaki da na tumaki, da garkunansu na shanu, da dukkan abin da suke da shi.’
33 To, sa’ad da Fir’auna zai kira ku, ya tambaye ku, ‘Mece ce sana’arku?’
34 Sai ku ce, ‘Ranka ya daɗe, mu makiyayan shanu ne tun muna ‘yan yara har zuwa yau, da mu da kakanninmu,’ don ku sami wurin zama a ƙasar Goshen, gama kowane makiyayi abin ƙyama ne ga Masarawa.”