FAR 5

Zuriyar Adamu

1 Wannan shi ne littafin asalin Adamu. A sa’ad da Allah ya halicci mutum, ya yi shi cikin siffar Allah.

2 Namiji da ta mace ya halicce su, ya sa musu albarka, ya sa musu suna, Mutum, sa’ad da aka halicce su.

3 Da Adamu ya yi shekara ɗari da talatin, ya haifi ɗa cikin kamanninsa da cikin siffarsa, ya kuwa sa masa suna Shitu.

4 Bayan da Adamu ya haifi ɗansa Shitu, ya yi shekara ɗari takwas, sa’an nan ya haifi ‘ya’ya mata da maza.

5 Haka nan kuwa dukan kwanakin Adamu shekara ce ɗari tara da talatin, ya rasu.

6 Da Shitu ya yi shekara ɗari da biyar, ya haifi Enosh.

7 Bayan da Shitu ya haifi Enosh ya rayu shekara ɗari takwas da bakwai, ya haifi ‘ya’ya mata da maza.

8 Haka nan kuwa dukan kwanakin Shitu shekara ce ɗari tara da goma sha biyu, ya rasu.

9 Da Enosh ya yi shekara tasa’in, ya haifi Kenan.

10 Bayan Enosh ya haifi Kenan ya rayu shekara ɗari takwas da goma sha biyar, ya kuma haifi ‘ya’ya mata da maza.

11 Haka nan kuwa dukan kwanakin Enosh shekara ce ɗari tara da biyar, ya rasu.

12 Sa’ad da Kenan ya yi shekara saba’in, ya haifi Mahalalel.

13 Bayan da Kenan ya haifi Mahalalel ya yi shekara ɗari takwas da arba’in, ya kuma haifi ‘ya’ya mata da maza.

14 Haka nan kuwa dukan kwanakin Kenan shekara ce ɗari tara da goma, ya rasu.

15 Sa’ad da Mahalalel ya yi shekara sittin da biyar ya haifi Yared.

16 Bayan da Mahalalel ya haifi Yared, ya yi shekara ɗari takwas da talatin, ya kuma haifi ‘ya’ya mata da maza.

17 Haka nan kuwa dukan kwanakin Mahalalel shekara ce ɗari takwas da tasa’in da biyar, ya rasu.

18 Sa’ad da Yared ya yi shekara ɗari da sittin da biyu, ya haifi Anuhu.

19 Bayan da Yared ya haifi Anuhu ya yi shekara ɗari takwas ya haifi ‘ya’ya mata da maza.

20 Haka nan kuwa dukan kwanakin Yared shekara ce ɗari tara da sittin da biyu, ya rasu.

21 Sa’ad da Anuhu ya yi shekara sittin da biyar, ya haifi Metusela.

22 Bayan da Anuhu ya haifi Metusela, ya yi tafiya tare da Allah shekara ɗari uku ya haifi ‘ya’ya mata da maza.

23 Haka nan kuwa dukan kwanakin Anuhu shekara ce ɗari uku da sittin da biyar.

24 Anuhu ya yi tafiya tare da Allah, Allah kuwa ya ɗauke shi, ba a ƙara ganinsa ba.

25 Sa’ad da Metusela ya yi shekara ɗari da tamanin da bakwai, ya haifi Lamek.

26 Bayan da Metusela ya haifi Lamek ya yi shekara ɗari bakwai da tamanin da biyu, ya haifi ‘ya’ya mata da maza.

27 Haka nan kuwa dukan kwanakin Metusela shekara ce ɗari tara da sittin da tara, ya rasu.

28 Sa’ad da Lamek ya yi shekara ɗari da tamanin da biyu, ya haifi ɗa,

29 ya sa masa suna Nuhu, yana cewa, “Daga gare shi za mu sami sauƙin aikinmu da wahalar hannuwanmu a ƙasar da Ubangiji ya la’anta.”

30 Bayan da Lamek ya haifi Nuhu ya yi shekara ɗari biyar da tasa’in da biyar, ya haifi ‘ya’ya mata da maza.

31 Haka nan kuwa dukan kwanakin Lamek shekara ce ɗari bakwai da saba’in da bakwai, ya rasu.

32 Sa’ad da Nuhu ya yi shekara ɗari biyar, ya haifi Shem, da Ham, da Yafet.