Wahalar Isra’ilawa a Masar
1 Waɗannan su ne sunayen ‘ya’ya maza na Isra’ila, waɗanda suka tafi Masar tare da Yakubu, kowanne da iyalinsa.
2 Su ne Ra’ubainu, da Saminu, da Lawi, da Yahuza,
3 da Issaka, da Zabaluna, da Biliyaminu,
4 da Dan, da Naftali, da Gad, da Ashiru.
5 Zuriyar Yakubu duka mutum saba’in ne, Yusufu kuwa, an riga an kai shi Masar.
6 Ana nan sai Yusufu ya rasu, shi da dukan ‘yan’uwansa na wannan tsara.
7 Amma ‘ya’yan Isra’ila suka hayayyafa, suka ƙaru ƙwarai, suka riɓaɓɓanya, suka ƙasaita ƙwarai da gaske, har suka cika ƙasar.
8 A wannan lokaci kuwa aka yi wani sabon sarki a Masar wanda bai san Yusufu ba.
9 Sai ya ce wa mutanensa, “Duba, jama’ar Isra’ila sun cika yawa sun fi ƙarfinmu.
10 Zo, mu san irin dabarar da za mu yi musu, don kada su riɓaɓɓanya, domin in aka faɗa mana da yaƙi, kada su haɗa kai da maƙiyanmu, su yaƙe mu, su tsere daga ƙasar.”
11 Suka kuwa naɗa musu shugabannin aikin gandu domin su wahalshe su da mawuyacin aiki. Aka sa su su gina wa Fir’auna biranen ajiya, wato Fitom da Ramases.
12 Amma ko da yake Masarawa sun ƙara tsananta musu, duk da haka sai suka ƙara ƙaruwa, suna ta yaɗuwa. Masarawa kuwa suka tsorata saboda Isra’ilawa.
13 Suka kuma tilasta wa Isra’ilawa su yi ta aiki mai tsanani.
14 Suka baƙanta musu rai da aiki mai tsanani na kwaɓa, da yin tubali, da kowane irin aiki a saura. A cikin ayyukansu duka suka tsananta musu.
15 Sarkin Masar ya ce wa ungozomar Ibraniyawa, Shifra da Fu’a,
16 “Sa’ad da kuke yi wa matan Ibraniyawa hidimarku ta ungozomai, in kuka gan su durƙushe, in jariri ne suka haifa, sai ku yi masa sanadin mutuwa, in kuma jaririya ce, ku bar ta da rai.”
17 Amma da yake ungozomar masu tsoron Allah ne, ba su yi yadda Sarkin Masar ya umarce su ba, amma suka bar ‘ya’ya maza da rai.
18 Don haka Sarkin Masar ya kirawo ungozomar, ya ce musu, “Me ya sa kuka bar ‘ya’ya maza da rai?”
19 Ungozomar suka ce wa Fir’auna, “Domin matan Ibraniyawa ba kamar matan Masarawa ba ne, gama su masu ƙwazo ne, sukan haihu tun ungozomar ba su kai wurinsu ba.”
20 Allah kuwa ya yi wa ungozoman nan alheri. Mutanen suka riɓanya, suka ƙasaita ƙwarai.
21 Allah kuma ya ba ungozoman nan zuriya domin sun ji tsoronsa.
22 Fir’auna kuwa ya umarci dukan mutanensa ya ce, “Duk jaririn da aka haifa wa Ibraniyawa, sai ku jefa shi cikin Kogin Nilu, amma idan jaririya ce, ku bar ta da rai.”