Waƙar Musa
1 Musa da jama’ar Isra’ila suka raira wannan waƙa ga Ubangiji suka ce,
“Zan raira waƙa ga Ubangiji, gama ya ci gawurtacciyar nasara,
Dawakai da mahayansu ya jefar cikin bahar.
2 Ubangiji ne ƙarfina da mafakata,
Shi ne wanda ya cece ni.
Wannan ne Allahna, zan yabe shi,
Allah na kakana, zan ɗaukaka shi.
3 Ubangiji mayaƙi ne,
Yahweh ne sunansa.
4 “Karusan Fir’auna da rundunarsa, ya jefar cikin bahar,
Zaɓaɓɓun jarumawansa ya nutsar da su cikin Bahar Maliya.
5 Rigyawa ta rufe su,
Suka nutse cikin zurfi kamar dutse.
6 Ya Ubangiji dantsen damanka, mai iko ne,
Ya Ubangiji, dantsen damanka ya ragargaza magabta.
7 Cikin girman ɗaukakarka, ka kā da maƙiyanka, ka aika da hasalarka,
Ka cinye su kamar ciyawa.
8 Da hucin numfashin hancinka ruwa ya tattaru,
Rigyawa ta tsaya kamar tudu,
Zurfafan ruwa suka daskare a tsakiyar bahar.
9 Magabcin ya ce, ‘Zan bi, in kama su, in raba ganima,
Muradina a kansu zai biya, zan zare takobina, hannuna zai hallaka su.’
10 Ka hura iskarka, bahar ta rufe su, suka nutse kamar darma cikin manyan ruwaye.
11 “Ya Ubangiji, wane ne kamarka a cikin alloli?
Wa yake kamarka a cikin ɗaukaka da tsarki?
Mai banrazana cikin mafifitan ayyuka, mai aikata mu’ujizai.
12 Ka miƙa dantsen damanka, ƙasa ta haɗiye su.
13 Da tabbatacciyar ƙaunarka, ka bi da jama’arka da ka fansa,
Ka bi da su da ƙarfinka zuwa tsattsarkan mazauninka.
14 Al’ummai suka ji suka yi rawar jiki,
Tsoro ya kama mazaunan Filistiya.
15 Sarakunan Edom suka tsorata,
Shugabannin Mowab suna rawar jiki,
Dukan mazaunan Kan’ana sun narke.
16 Tsoro da razana sun aukar musu,
Ta wurin ikonka suka tsaya cik kamar dutse,
Har jama’arka, ya Ubangiji, suka haye,
I, jama’arka, ya Ubangiji, suka haye,
17 Za ka kawo su, ka dasa su a kan dutsen nan naka,
Wurin, ya Ubangiji, da ka maishe shi tsattsarkan mazauninka,
Tsattsarkan wurinka, ya Ubangiji, wanda ka kafa da ikonka.
18 Ubangiji zai yi mulki har abada abadin.”
19 Gama sa’ad da dawakan Fir’auna, da karusansa, da mahayan dawakansa suka shiga bahar, Ubangiji ya komar da ruwan bahar a bisansu, amma Isra’ilawa suka yi tafiya a busassiyar ƙasa ta tsakiyar bahar.
20 Sai Maryamu, annabiya, ‘yar’uwar Haruna, ta ɗauki kuru cikin hannunta. Mata duka suka fita, suka bi ta da kuwaru suna ta rawa.
21 Maryamu tana raira musu waƙa tana cewa,
“Raira waƙa ga Ubangiji, gama ya ci gawurtacciyar nasara,
Doki da mahayinsa, ya jefar cikin bahar.”
Maɓuɓɓugan Ruwan Ɗaci
22 Musa kuwa ya bi da Isra’ilawa daga Bahar Maliya, suka shiga jejin Sur. Suka yi tafiya kwana uku cikin jejin, ba su sami ruwa ba.
23 Sa’ad da suka zo Mara, sun kasa shan ruwan Mara saboda ɗacinsa, don haka aka sa masa suna Mara.
24 Sai mutanen suka yi wa Musa gunaguni suna cewa, “Me za mu sha?”
25 Musa ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya nuna masa wani itace. Sa’an nan Musa ya karyi itacen, ya jefa cikin ruwa, ruwan kuwa ya zama mai daɗi.
A nan ne Ubangiji ya kafa musu dokoki da ka’idodi, a nan ne kuma ya gwada su.
26 Ya ce, “In za ku himmantu ku yi biyayya da ni, ni da nake Ubangiji Allahnku, sai ku aikata abin da yake daidai a gare ni, ku kuma kiyaye umarnaina da dokokina duka, to, ba zan sa muku cuce-cuce irin waɗanda na sa wa Masarawa ba, gama ni ne Ubangiji da nake warkar da ku.”
27 Daga nan suka je Elim inda akwai maɓuɓɓugan ruwa goma sha biyu, da itatuwan giginya saba’in. A nan suka yi zango a bakin ruwa.