Adalci da Aikata Gaskiya
1 Kada ku baza rahoton ƙarya. Kada wani ya haɗa baki da mugu ya zama munafukin mashaidi.
2 Kada ku yi mugunta domin galibin mutane na yi, kada kuwa ku yi shaidar zur a gaban shari’a don ku faranta zuciyar yawancin mutane, domin kada ku sa a kauce wa adalci.
3 Kada ku yi wa matalauci sonkai a gaban shari’a.
4 “Idan wani ya iske san maƙiyinsa ko jakinsa ya ɓace, sai ya komar masa da shi.
5 Idan wani ya ga kaya ya danne jakin maƙiyinsa kada ya tafi ya bar shi da shi, sai ya taimaka a ɗaga masa.
6 “Kada ku rasa yin adalci ga matalauci a wurin shari’a.
7 Ku yi nesa da ƙage. Kada ku kashe marar laifi da kuma adali, gama ba zan baratar da mugu ba.
8 Kada ku ci hanci, gama cin hanci yakan makantar da masu mulki, yakan kuma karkatar da manufar masu gaskiya.
9 “Kada ku wulakanta baƙo, kun dai san halin baƙunci, gama dā ku baƙi ne a ƙasar Masar.”
Shekara ta Bakwai da Rana ta Bakwai
10 “Za ku nomi gonakinku shekara shida, kuna tattara amfaninsu.
11 Amma a shekara ta bakwai, ku bar su su huta kurum, ba za ku girbi kome daga ciki ba, domin mutanenku matalauta su ci abin da ya ragu, namomin jeji kuma su ci. Haka kuma za ku yi da gonakinku na inabi da na zaitun.
12 “Cikin kwana shida za ku yi aikinku, amma a kan rana ta bakwai sai ku huta, don shanunku da jakunanku su kuma su huta, don bayinku da baƙinku su wartsake.
13 Ku kula da dukan abin da na faɗa muku. Kada a ji bakinku na roƙon kome ga waɗansu alloli.”
Ƙayyadaddun Idodi Uku
14 “Sau uku a shekara za ku yi mini idi.
15 Wajibi ne ku yi idin abinci marar yisti, kamar yadda na umarce ku. Za ku ci abinci marar yisti kwana bakwai lokacin da aka ayyana a watan Abib, gama a wannan wata ne kuka fito daga Masar. Kada wani ya zo wurina hannu wofi.
16 Ku kuma yi idin nunan fari na amfanin gonakinku da kaka. Sa’an nan kuma za ku yi idin gama tattara amfanin gonakinku a ƙarshen shekara.
17 Sau uku a shekara mazaje za su gabatar da kansu a gaban Ubangiji.
18 “Kada ku miƙa jinin hadayata tare da abinci mai yisti. Kada kuma ku ajiye kitsen abin da aka yanka a lokacin idina, ya kwana.
19 “Wajibi ne ku kawo mafi kyau daga cikin nunan fari na amfanin gonakinku a gidan Ubangiji Allahnku.
“Kada ku dafa ɗan akuya cikin madarar uwarsa.”
Mala’ikan Ubangiji zai Bi da Isra’ilawa
20 “Ni da kaina zan aiki mala’ika a gabanku don ya kiyaye ku a sa’ad da kuke tafiya, ya kuma kai ku inda na shirya muku.
21 Ku nuna masa bangirma, ku kasa kunne ga maganarsa. Kada ku tayar masa, gama ba zai gafarta muku laifofinku ba, gama shi wakilina ne.
22 Idan kun kasa kunne a hankali ga maganarsa, kuka aikata dukan abin da na faɗa, sai in zama maƙiyin maƙiyanku da magabcin magabtanku.
23 Mala’ikana zai wuce gabanku, ya bi da ku inda Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Kan’aniyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa suke, zan kuma hallakar da su ƙaƙaf.
24 Ba za ku rusuna wa allolinsu ba, balle fa ku bauta musu, kada ku yi yadda suke yi. Sai ku hallaka allolinsu ɗungum, ku farfashe keɓaɓɓun duwatsunsu.
25 Za ku bauta wa Ubangiji Allahnku, ni kuwa zan yalwata abincinku da ruwan shanku, in kuma kawar muku da ciwo.
26 A ƙasarku, mace ba za ta yi ɓari ba, ba kuma za a sami marar haihuwa ba. Zan ba ku tsawon rai.
27 “Zan aiki razanata a gabanku, in sa mutanen da za ku gamu da su su ruɗe. Zan sa maƙiyanku duka su ba ku baya, su sheƙa a guje.
28 Zan aiki zirnako a gabanku, su kore muku Hiwiyawa, da Kan’aniyawa, da Hittiyawa.
29 Ba a shekara guda zan kore muku su ba, don kada ƙasar ta zama kufai har namomin jeji su fi ƙarfinku.
30 Da kaɗan da kaɗan zan kore muku su, har yawanku ya kai yadda za ku mallaki ƙasar.
31 Zan yanka muku kan iyaka daga Bahar Maliya zuwa tekun Filistiyawa, daga jeji kuma zuwa Kogin Yufiretis. Gama zan ba da mazaunan ƙasar a hannunku, za ku kore su daga gabanku.
32 Kada ku ƙulla alkawari da su, ko da allolinsu.
33 Kada su zauna cikin ƙasarku domin kada su sa ku ku yi mini zunubi, ku bauta wa allolinsu, har abin kuwa ya zamar muku tarko.”