Bagaden Ƙona Turare
1 “Za ku yi bagaden ƙona turare. Za ku yi shi da itacen ƙirya.
2 Tsawonsa da fāɗinsa kamu guda guda ne, zai zama murabba’i, amma tsayinsa ya zama kamu biyu. Za a haɗa zankayensa su zama ɗaya da shi.
3 Za ku dalaye shi, da bisansa, da gyaffansa, da zankayensa da zinariya tsantsa. Ku kuma yi masa dajiyar zinariya.
4 Za ku yi masa ƙawanya biyu na zinariya a ƙarƙashin dajiyar gefe da gefe, daura da juna. Ƙawanen za su zama inda za a zura sandunan ɗaukarsa.
5 Za ku yi sandunan da itacen ƙirya, ku dalaye su da zinariya.
6 Sai ku ajiye bagaden a gaban labulen akwatin alkawari da murfin akwati inda zan sadu da kai.
7 Haruna kuwa zai ƙona turare mai ƙanshi a bisansa kowace safiya lokacin da yake gyarta fitilun.
8 Zai kuma ƙona turaren sa’ad da ya kunna fitilun da almuru. Za a riƙa ƙona turare kullum a gaban Ubangiji dukan zamananku.
9 Ba za a ƙona wani irin turare dabam ba a bisansa, ba kuma za a miƙa hadaya ta ƙonawa, ko ta gari, ko ta sha, a bisansa ba.
10 Sau ɗaya a shekara Haruna zai yi kafara a bisa zankayensa. Zai yi kafara a bisansa da jinin hadaya don zunubi ta yin kafara. Za a riƙa yin wannan dukan zamananku, gama bagaden mai tsarki ne ga Ubangiji.”
Kuɗin Haikali
11 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa,
12 “A sa’ad da za ku ƙidaya Isra’ilawa, sai ko wannensu ya biya fansar kansa ga Ubangiji domin kada annoba ta buge su lokacin da za ku ƙidaya su.
13 Dukan wanda aka lasafta shi cikin ƙidayar kuwa zai biya kuɗi bisa ga ma’aunin kuɗin da ake aiki da shi. Tilas kowanne ya biya wannan, gama sadaka ce ga Ubangiji.
14 Duk wanda aka lasafta shi cikin ƙidayar tun daga mai shekara ashirin ko fi, zai ba da wannan sadaka ga Ubangiji.
15 Lokacin da kuke ba da wannan sadaka ga Ubangiji saboda kafarar rayukanku, mai samu ba zai zarce ba, matalauci kuma ba zai ba da abin da ya gaza abin da aka ƙayyade ba.
16 Za ku karɓi kuɗin nan na kafara daga wurin Isra’ilawa, ku ajiye shi domin aiki a alfarwa ta sujada. Zai zama abin tunawa ga Isra’ilawa a gaban Ubangiji, don su yi kafarar kansu.”
Daron Tagulla na Wanke Hannu
17 Ubangiji ya kuma ce wa Musa,
18 “Sai ku yi daro da tagulla don wanka. Ku yi masa gammo da tagulla, ku ajiye shi tsakanin alfarwa ta sujada da bagaden, ku zuba ruwa a ciki.
19 A wurin ne Haruna da ‘ya’yansa maza za su wanke hannuwansu da ƙafafunsu.
20 Sa’ad da suke shiga cikin alfarwa ta sujada ko sa’ad da suke kusatar bagade don su miƙa hadaya ta ƙonawa da wuta ga Ubangiji, sai su yi wanka don kada a kashe su.
21 Su wanke hannuwansu da ƙafafunsu don kada su mutu. Yin wannan zai zama musu da zuriyarsu farilla dukan zamanansu.”
Man Keɓewa da Turare
22 Ubangiji kuma ya ce wa Musa,
23 “Ɗauki kayan yaji masu kyan gaske, ruwan mur na shekel ɗari biyar, da kirfa mai daɗin ƙanshi na shekel ɗari biyu da hamsin, da turaren wuta mai ƙanshi na shekel ɗari biyu da hamsin,
24 da kashiya na shekel ɗari biyar bisa ga ma’aunin kuɗin da ake aiki da shi, da moɗa ɗaya na man zaitun.
25 Da waɗannan za ku yi man keɓewa mai tsarki yadda mai yin turare yake yi, zai zama man keɓewa mai tsarki.
26 Za a shafa wa alfarwa ta sujada da akwatin alkawari wannan mai.
27 A kuma shafa wa teburin da kayayyakinsa, da alkukin da kayayyakinsa, da bagaden ƙona turare,
28 da bagaden hadaya ta ƙonawa da kayayyakinsa, da daron da gammonsa.
29 Ta haka za a tsarkake su domin su zama masu tsarki sosai. Duk abin da ya taɓa su zai tsarkaka.
30 Za ka zuba wa Haruna da ya’yansa maza mai, ka keɓe su domin su zama firistocina masu yi mini aiki.
31 Sai ka faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘Wannan mai, mai tsarki ne a gare ni domin keɓewa a dukan zamananku.
32 Ba za a shafa wa kowa ba, ba kuma za a yi wani mai irinsa ba, gama man tsattsarka ne, saboda haka zai kasance tsattsarka a gare ku.
33 Duk wanda ya yi wani irinsa ko kuwa ya shafa wa wani, za a raba shi da jama’arsa.”’
34 Ubangiji ya ce wa Musa, “Ɗauki kayan yaji masu ƙanshi, su stakte, da onika, da galbanum tare da lubban. Su zama daidai wa daida.
35 Da waɗannan za a yi turare yadda mai yin turare yake yi, a sa masa gishiri, ya zama tsabtatacce, tsarkakakke.
36 A ɗauki kaɗan daga ciki, a niƙa, sa’an nan a ɗiba daga ciki, a ajiye a gaban akwatin alkawari a cikin alfarwa ta sujada a inda zan sadu da kai. Wannan turare zai zama muku mafi tsarki.
37 Irin turaren nan da za ku yi, ba za ku yi wa kanku irinsa ba. Zai zama abu mai tsarki a gare ku, gama na Ubangiji ne.
38 Duk wanda ya yi irin turaren nan don amfanin kansa, za a raba shi da jama’arsa.”