Waɗanda za su Yi alfarwa ta Sujada
1 Ubangiji kuma ya ce wa Musa,
2 “Ga shi, na zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuza.
3 Na cika shi da Ruhuna, da hikima, da basira, da ilimi, da fasaha,
4 don ya yi fasalin abubuwa na zinariya, da azurfa, da tagulla,
5 da yankan duwatsu masu tamani na jerawa, da sassaƙa itace, da kowane irin aikin fasaha.
6 Ga shi kuma, ni da kaina, na sa Oholiyab ɗan Ahisamak na kabilar Dan tare da shi, na kuma sa hikima a zukatan masu hikima, don su yi dukan abin da na umarce ka
7 a kan alfarwar ta sujada da akwatin alkawari, da murfin da yake bisansa, da dukan kayayyakin da yake cikin alfarwar,
8 da teburin da kayayyakinsa, da alkuki na zinariya tsantsa tare da dukan kayayyakinsa, da bagaden ƙona turare,
9 da bagaden hadaya ta ƙonawa da dukan kayayyakinsa, da daron da gammonsa,
10 da saƙaƙƙun tufafi, wato da tsarkakakkun tufafin Haruna da na ‘ya’yansa maza domin aikin firistoci,
11 da man keɓewa, da turaren nan mai ƙanshi domin Wuri Mai Tsarki. Za su yi su duka kamar yadda na umarce ka.”
Ranar Hutawa
12 Ubangiji kuma ya ce wa Musa,
13 “Faɗa wa Isra’ilawa, ‘Sai ku kiyaye Asabar domin shaida tsakanina da ku da zuriyarku har abada, domin ku sani ni ne Ubangiji wanda ya keɓe ku.
14 Ku kiyaye ranar Asabar gama tsattsarkar rana ce a gare ku. Duk wanda ya tozarta ta, za a kashe shi, duk wanda ya yi aiki kuma a cikinta za a raba shi da jama’arsa.
15 A kwana shida za a yi aiki, amma rana ta bakwai ranar hutawa ce tsattsarka ta saduda ga Ubangiji, don haka duk wanda ya yi kowane irin aiki a cikinta za a kashe shi.
16 Domin wannan fa Isra’ilawa za su kiyaye ranar Asabar, su kiyaye ta dukan zamanansu, gama madawwamin alkawari ne.
17 Ranar za ta zama dawwamammiyar shaida tsakanina da Isra’ilawa, cewa a kwana shida ni Ubangiji na yi sama da ƙasa, amma a rana ta bakwai na ajiye aiki, na huta.”’
18 Sa’ad da ya gama magana da Musa a kan Dutsen Sina’i, sai ya ba shi alluna biyu na shaida, allunan duwatsu rubatattu da yatsan Allah.