1 “Da Bezalel da Oholiyab, da kowane mutum mai hikima, waɗanda Ubangiji ya ba su hikima da basira na sanin yin kowane irin aiki, za su shirya Wuri Mai Tsarki kamar yadda Ubangiji ya umarta.”
Jama’a Sun Kawo Sadaka Mai Yawa
2 Sai Musa ya kirayi Bezalel, da Oholiyab, da kowane mutum mai hikima wanda Ubangiji ya ba shi hikima a zuciya, da duk wanda zuciyarsa ta iza shi ya zo, ya yi aikin.
3 Su kuwa suka karɓa daga wurin Musa dukan sadaka ta yardar rai da Isra’ilawa suka kawo don yin aikin alfarwa ta sujada. Jama’a suka yi ta kawo masa sadaka ta yardar rai kowace safiya.
4 Sai masu hikiman da suke yin aiki na alfarwa ta sujada suka ɗan dakatar da aiki suka tafi wurin Musa.
5 Suka ce masa, “Jama’a suna ta kawo sadaka fiye da abin da ake bukata domin aikin da Ubangiji ya umarta a yi.”
6 Sai Musa ya umarce su su yi shela a zango cewa, “Kada wata mace ko wani namiji ya sāke kawo sadaka don aikin alfarwa ta sujada.” Sai jama’a suka daina kawowa.
7 Gama abin da aka kawo ya isa yin aikin, har da ragi.
Yin Alfarwa ta Sujada
8 Sai dukan mutane masu gwaninta daga cikin ma’aikatan, suka yi alfarwa da labule goma. An yi labulen da lallausan zaren lilin na shuɗi, da shunayya, da mulufi. Aka yi wa labulen zānen kerubobi na gwaninta.
9 Tsawon kowane labule kamu ashirin da takwas, fāɗinsa kuma kamu huɗu ne. Dukan labulen girmansu ɗaya ne.
10 Ya ɗinɗinke labule biyar a harhaɗe, haka kuma ya yi da sauran labule biyar.
11 Sai ya sa shuɗɗan hantuna a karbun labule na fari da na biyu.
12 Ya sa hantuna hamsin a karbun labule na fari, haka kuma ya sa na biyun. Dukan hantunan suna daura da juna.
13 Ya kuma yi maɗauri hamsin na zinariya, ya harhaɗa labule da juna da maɗauran domin alfarwa ta zama ɗaya.
14 Ya kuma yi labule goma sha ɗaya da gashin awaki domin ya rufe alfarwa.
15 Tsawon kowane labule kamu talatin, fāɗinsa kuma kamu huɗu ne. Labule goma sha ɗayan nan girmansu ɗaya ne.
16 Ya harhaɗa labule biyar wuri ɗaya, shida kuma ya harhaɗa su wuri ɗaya.
17 Sai ya yi hantuna hamsin, ya sa a karbu na bisa na labule na farin, haka kuma ya sa hantuna hamsin a karbun sama na labule na biyu.
18 Ya kuma yi maɗaurai da tagulla waɗanda zai harhaɗa hantuna da su don alfarwa ta zama ɗaya.
19 Ya yi wa alfarwa murfi da fatun raguna da aka rina ja, ya kuma yi wani abin rufewa da fatuna da aka jeme.
20 Ya kuma yi katakan alfarwa da itacen ƙirya.
21 Tsawon kowane katako kamu goma ne, kaurinsa kuma kamu ɗaya da rabi ne.
22 Kowane katako an fiƙe bakinsa biyu don a harhaɗa su tare, haka ya yi da dukan katakan alfarwa.
23 Yadda ya yi da katakan alfarwa ke nan, ya kafa katakai ashirin a fuskar kudu.
24 Sai ya yi kwasfa arba’in da azurfa domin katakai ashirin. Kowane katako yana da kwasfa biyu saboda bakinsa biyu da aka fiƙe.
25 A fuska ta biyu ta wajen arewa ta alfarwa, ya kafa katakai ashirin.
26 Ya kuma yi kwasfa arba’in na azurfa. Kowane katako yana da kwasfa biyu.
27 Ya yi katakai shida a bayan alfarwa a fuskar yamma.
28 Ya kuma yi katakai biyu don kusurwar baya ta alfarwa.
29 Aka haɗa katakai daga ƙasa har zuwa sama inda aka haɗa su a ƙawanya ta fari, haka ya yi da su a kusurwoyin nan biyu.
30 Akwai katako takwas da kwasfansu na azurfa guda goma sha shida. Kowane katako yana da kwasfa biyu.
31 Sai ya yi sanduna na itacen ƙirya, sanduna biyar domin katakan gefe ɗaya na alfarwa,
32 sanduna biyar kuma domin katakan ɗaya gefen na alfarwa, biyar kuma domin katakan da yake baya na alfarwa wajen yamma.
33 Ya sa sandan da yake a tsakiya ya wuce daga wannan gefe zuwa wancan gefe.
34 Ya dalaye katakai da zinariya. Ya yi musu ƙawane na zinariya inda za a sarƙafa sandunan. Ya kuma dalaye sandunan da zinariya.
35 Ya kuma yi labule da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin, ya kuma yi wa labulen zānen kerubobi na gwaninta.
36 Ya yi wa labulen dirkoki huɗu da itacen ƙirya. Sai ya dalaye su da zinariya. Ya kuma yi musu maratayai da zinariya. Ya yi wa dirkokin nan kwasfa huɗu da azurfa.
37 Ya yi wa ƙofar alfarwa labulen da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin. Ya yi wa labulen ado.
38 Ya haɗa labulen da dirkokinsa biyar, da maratayansu. Ya dalaye kawunansu da maɗauransu da zinariya, amma ya dalaye kwasfansu guda biyar da tagulla.