Yin Akwatin Alkawari
1 Bezalel ya yi akwati da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kamu ɗaya da rabi.
2 Ya dalaye shi da zinariya tsantsa ciki da waje, ya kuma yi masa dajiya da zinariya kewaye da shi.
3 Ya sa masa ƙawanya huɗu na zinariya a kan kusurwoyinsa huɗu, ƙawane biyu a wannan gefe, biyu kuma a wancan gefe.
4 Ya kuma yi sandunan da itacen ƙirya, ya dalaye su da zinariya.
5 Sai ya zura sandunan cikin ƙawanen da suke a gyaffan akwatin don ɗaukarsa.
6 Ya yi murfin da zinariya tsantsa, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuma kamu ɗaya da rabi.
7 Ya kuma ƙera siffofin kerubobi biyu da zinariya, ya maƙala su a gefe biyu na murfin.
8 Kerub ɗaya a wannan gefe, ɗaya kuma a wancan gefe. Ya yi su a haɗe da murfin a gefe biyu na murfin.
9 Kerubobin suka buɗe fikafikansu sama, suka inuwantar da murfin da fikafikansu. Fuskokinsu kuma na duban juna, suna kuma fuskantar murfin.
Yin Tebur
10 Sai kuma ya yi tebur da itacen ƙirya, tsawsonsa kamu biyu, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kamu ɗaya da rabi.
11 Ya dalaye shi da zinariya tsantsa, ya yi masa dajiya da zinariya.
12 Ya yi masa dajiya mai fāɗin tafin hannu kewaye da shi, ya kuma yi wata dajiya da zinariya kewaye da ita.
13 Ya yi wa tebur ɗin ƙawane huɗu na zinariya, ya manna ƙawane a kusurwoyi huɗu na ƙafafunsa.
14 Ƙawanen suna kusa da dajiyar inda za a zura sanduna na ɗaukar teburin.
15 Ya yi sanduna da itacen ƙirya don ɗaukar teburin. Sa’an nan ya dalaye su da zinariya.
16 Ya yi kayan teburin da zinariya tsantsa, wato farantansa, da kwanonin tuya, da kwanoninsa, da butoci domin yin hadaya ta sha.
Yin Alkuki
17 Ya yi alkuki da zinariya tsantsa. An yi gindinsa da gorar jikinsa da ƙerarriyar zinariya. Ƙoƙunan alkukin da mahaɗansa, da furanninsa, a haɗe aka yi su da alkukin.
18 Akwai rassan fitila guda shida, uku a wannan gefe, uku kuma a wancan.
19 A kowane reshe na alkukin akwai ƙoƙuna uku masu kamar tohon almond, akwai kuma mahaɗai da furanni.
20 A bisa alkukin kuma akwai ƙoƙuna guda huɗu da aka yi su kamar tohon almond, da mahaɗai, da furanni.
21 Akwai mahaɗi kuma a ƙarƙashin kowane reshe biyu biyu na dukan rassan guda shida, a miƙe daga alkukin.
22 An ƙera mahaɗai da rassan alkuki a haɗe. Da ƙerarriyar zinariya aka yi alkukin da dukan kome nasa a haɗe.
23 Da zinariya tsantsa ya yi fitilu bakwai, da hantsuka da farantansa.
24 Da zinariya tsantsa na talanti ɗaya ya yi alkukin da kayayyakinsa duka.
Yin Bagaden Ƙona Turare
25 Ya yi bagaden ƙona turare da itacen ƙirya, tsawonsa kamu ɗaya, fāɗinsa kamu ɗaya, shi murabba’i ne, tsayinsa kuma kamu biyu ne, zankayensa kuwa a haɗe suke da shi.
26 Ya dalaye shi da zinariya tsantsa, da bisansa, da kewayen gyaffansa, da zankayensa. Ya kewaye shi kuma da dajiya ta zinariya.
27 Ya sa masa ƙawane biyu na zinariya a gyaffansa a ƙarkashin dajiya daura da juna don a zura sandunan ɗaukarsa.
28 Ya kuma yi sanduna biyu da itacen ƙirya, sa’an nan ya dalaye su da zinariya.
Yin Man Keɓewa da Turare
29 Ya yi tsattsarkan mai na keɓewa da kuma turare mai ƙanshi yadda mai yin turare yakan yi.