Yin Tufafin Firistoci
1 An yi wa firistoci tufafi masu kyau na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, domin yin aiki a Wuri Mai Tsarki. Suka yi wa Haruna tsarkakan tufafi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
2 Ya yi falmaran da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan lilin.
3 An kuma buga zinariya fake-fake, suka yanyanka ta zare-zare don su yi saƙa da ita tare da zane na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, da na lallausan lilin, aikin gwani mai fasaha.
4 Suka yi wa falmaran kafaɗu, sa’an nan suka haɗa su a gefenta biyu na sama.
5 Gwanin masaƙi ya saƙa abin ɗamarar falmaran. Da irin kayan da aka saƙa falmaran ne aka saƙa abin ɗamarar, wato da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da zaren lallausan lilin kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
6 Sai aka gyaggyarta duwatsu masu daraja aka jera su cikin tsaiko na zinariya. Aka zana sunayen ‘ya’yan Isra’ila a kan duwatsun kamar yadda akan yi hatimi.
7 Aka sa su a kan kafaɗun falmaran don su zama duwatsun tunawa da Isra’ila kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
8 Aka kuma yi ƙyallen maƙalawa a ƙirji da gwaninta kamar yadda aka yi wa falmaran aiki da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan lilin.
9 Ƙyallen maƙalawa a ƙirji murabba’i ne, aka ninka shi biyu, tsawonsa da fāɗinsa kamu ɗaya ɗaya ne.
10 Sai suka sa jeri huɗu na duwatsu masu daraja a bisansa. A jeri na fari aka sa yakutu, da tofaz, da zumurrudu.
11 A jeri na biyu aka sa turkos, da saffir, da daimon.
12 A jeri na uku aka sa yakinta, da idon mage, da ametis.
13 A jeri na huɗu aka sa beril, da onis, da yasfa. Aka sa su cikin tsaiko na zinariya.
14 An zana sunayen ‘ya’yan Isra’ila goma sha biyu a kan duwatsu masu daraja kamar yadda akan yi hatimi.
15 Sai suka yi tukakkun sarƙoƙi na zinariya tsantsa a kan ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
16 Suka yi tsaiko biyu na zinariya da ƙawane biyu na zinariya. Sai suka sa ƙawanen nan biyu a gefe biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
17 Suka kuma zura sarƙoƙin nan biyu na zinariya a ƙawanen nan biyu na zinariya na gyaffan ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
18 Sai suka maƙala waɗancan bakin sarƙoƙin zinariya a tsaikon nan biyu, sa’an nan suka rataya su a kafaɗun falmaran daga gaba.
19 Suka kuma yi ƙawane biyu na zinariya, suka sa su a gefe biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji daga ciki kusa da falmaran.
20 Suka yi waɗansu ƙawane biyu na zinariya, suka maƙala su daga ƙasa a gaban kafaɗu biyu na falmaran kusa da mahaɗin a bisa abin ɗamarar falmaran.
21 Sai suka ɗaure ƙawanen ƙyallen maƙalawa a ƙirjin a ƙawanen falmaran da shuɗiyar igiya don ƙyallen maƙalawa a ƙirji ya kwanta lif a bisa kan abin ɗamarar falmaran don kada ya kwance daga falmaran, sun yi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
22 Ya kuma saƙa taguwa ta falmaran da shuɗi duka.
23 An yi wa taguwar wuyan wundi kamar sulke, aka daje wuyan don kada ya kece.
24 A karbun taguwar, suka yi fasalin ‘ya’yan rumman da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan lilin.
25 Suka kuma yi ƙararrawa da zinariya tsantsa, suka sa su a tsakankanin fasalin ‘ya’yan rumman kewaye da karbun taguwa.
26 An jera su bi da bi, wato fasalin rumman yana biye da ƙararrawa. Haka aka jera su kewaye da karbun taguwar yin aiki, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
27 Suka saƙa zilaika da lallausan zaren lilin don Haruna da ‘ya’yansa.
28 Suka kuma yi rawani, da huluna, da mukurai da lallausan lilin.
29 Sun kuma yi abin ɗamara da lallausan lilin mai launin shuɗi, da shunayya, da mulufi. Aka yi mata ɗinkin ado kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
30 Suka yi allo tsattsarka da zinariya tsantsa suka zāna rubutu irin na hatimi a kansa haka, “MAI TSARKI GA UBANGIJI.”
31 Suka ɗaura shi da shuɗiyar igiya a gaban rawanin kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
Ƙarewar Aikin
32 Haka kuwa aka gama dukan aiki na alfarwa ta sujada. Isra’ilawa suka yi shi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
33 Sai suka kawo wa Musa alfarwa da dukan kayayyakinta, wato da maratayanta, da katakanta, da sandunanta, da dirkokinta, da kwasfanta,
34 da murfi na fatun raguna da na awaki, da labulen,
35 da akwatin alkawari da sandunansa, da murfinsa,
36 da tebur, da kayayyakinsa duka, da gurasar ajiyewa,
37 da alkuki na zinariya tsantsa da fitilunsa da dukan kayayyakinsa, da man fitila,
38 da bagade na zinariya, da man keɓewa, da turare mai ƙanshi, da labulen ƙofar alfarwar,
39 da bagade na tagulla da ragarsa ta tagulla, da sandunansa da dukan kayayyakinsa, da daro da gammonsa,
40 da labulen farfajiya da dirkokinta, da kwasfanta, da labulen ƙofarta, da igiyoyinta, da turakunta, da dukan kayayyakin yin aiki a alfarwa ta sujada,
41 da tufafin ado na aiki a Wuri Mai Tsarki, wato tsarkakan tufafin Haruna firist, da tufafin ‘ya’yansa maza don su yi aikin firistoci.
42 Isra’ilawa sun yi dukan aiki kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
43 Da Musa ya duba dukan aikin, ga shi kuwa, sun yi shi daidai, kamar yadda Ubangiji ya umarta, sai Musa ya sa musu albarka.