Tsarkakewar Mata bayan Haihuwa
1 Ubangiji ya ba Musa ka’idodin nan domin jama’ar Isra’ila.
2 Idan mace ta yi ciki, ta haifi ɗa namiji, to, za ta zama marar tsarki har kwana bakwai, kamar cikin kwanakin hailarta.
3 A kan rana ta takwas za a yi wa jaririn kaciya.
4 Sa’an nan kuma sai ta ci gaba da zama cikin jinin har kwana talatin da uku. A lokacin ba za ta taɓa kowane tsattsarkan abu ba, ba za ta shiga wurin yin sujada ba, har kwanakin tsarkakewarta su cika.
5 Amma idan ‘ya mace ce ta haifa, za ta zama marar tsarki mako biyu kamar a kwanakin hailarta. Za ta ci gaba da zama cikin jinin har kwana sittin da shida.
6 Sa’ad da kwanakin tsarkakewarta na haihuwar ɗa ko ‘ya suka cika, sai ta kai wa firist ɗan rago bana ɗaya, a ƙofar alfarwa ta sujada don hadaya ta ƙonawa, da ɗan tattabara, ko kurciya na yin hadaya don zunubi.
7 Sai ya miƙa ga Ubangiji, ya yi kafara dominta, za ta kuwa tsarkaka. Wannan shi ne abin da ya wajaba ga wanda ta haifi ɗa ko ‘ya.
8 Amma idan ɗan rago ya fi ƙarfinta, sai ta kawo kurciyoyi biyu, ko ‘yan tattabarai biyu, ɗaya don hadaya ta ƙonawa, ɗayan kuwa don yin hadaya don zunubi. Firist kuwa zai yi kafara dominta, za ta kuwa tsarkaka.