Dokoki a kan Kuturta
1 Ubangiji ya ba Musa da Haruna waɗannan ka’idodi.
2 Idan mutum yana da kumburi a fatar jikinsa, ko ɓamɓaroki ko tabo, har ya zama kamar cutar kuturta, sai a kai shi wurin Haruna, firist, ko ɗaya daga cikin zuriyarsa, firistoci.
3 Firist ɗin zai dudduba cutar da take a fatar jikin mutumin. Idan gashin da yake wurin cutar ya rikiɗa ya zama fari, zurfin cutar kuma ya zarce fatar jikinsa, wannan cuta kuturta ce. Firist ɗin da ya dudduba shi zai hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne.
4 Amma idan tabon fari ne, zurfinsa kuwa bai zarce fatar ba, gashin kuma da yake cikinsa bai rikiɗa ya zama fari ba, sai firist ya kulle mai ciwon har kwana bakwai.
5 A rana ta bakwai firist zai ƙara dudduba shi, in ya ga cutar ba ta yaɗu a fatar jikin mutumin ba, sai ya sāke kulle shi waɗansu kwana bakwai kuma.
6 A rana ta bakwai sai firist ya sāke dubansa, idan ciwon ya dushe, cutar kuma ba ta yaɗuwa a fatar jikin mutumin, firist zai hurta, cewa, mutumin tsattsarka ne, ɓamɓaroki ne kawai, sai ya wanke tufafinsa.
7 Amma idan ɓamɓaroki ya yaɗu a cikin fatar jikin mutumin bayan da ya nuna kansa ga firist don tsarkakewa, sai ya sāke zuwa gaban firist.
8 Firist zai duba shi, idan ɓamɓaroki ya yaɗu a fatar, sai firist ya hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne, ba ɓamɓaroki ba ne, kuturta ce.
9 Sa’ad da cutar kuturta ta kama mutum, sai a kai shi wurin firist.
10 Firist kuwa ya dudduba shi, in akwai kumburi a fatar jikin mutum wanda ya rikiɗar da gashin wurin ya zama fari, in kuma akwai sabon miki a kumburin,
11 to, kuturta ce da ta daɗe a fatar jikinsa. Firist kuwa zai hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne, ba za a kulle shi ba, gama ya tabbata marar tsarki ne.
12 Idan kuturtar ta faso a fatar jikin mutum har ta rufe fatar jikin mutumin daga kai zuwa ƙafa a iyakar ganin firist,
13 firist ɗin zai duba shi, in kuturtar ta rufe jikin duka, zai hurta, cewa, mutumin tsarkakakke ne daga cutar, gama kuturtar ta rikiɗa, ta yi fari fat, don haka ya tsarkaka.
14 Amma a ranar da aka ga sabon miki a jikinsa zai zama marar tsarki.
15 Sai firist ya dudduba sabon mikin ya hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne, sabon miki fa marar tsarki ne, gama kuturta ce.
16 Idan kuma sabon mikin ya juya, ya rikiɗa ya zama fari, zai tafi wurin firist.
17 Firist ɗin zai dudduba shi, idan cutar ta rikiɗa ta zama fara, sai firist ya hurta, cewa, mutumin tsarkakakke ne, gama ya tsarkaka.
18 Amma idan akwai wanda yake da ƙurjin da ya warke,
19 idan kuma akwai tabo jaja-jaja, da fari-farin tabo, sai a nuna wa firist.
20 Firist zai dudduba shi, idan zurfin kumburin ko tabon rikiɗa fari, sai firist ya hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne, cutar kuturta ce ta faso a ƙurjin.
21 Amma idan firist ya dudduba shi ya ga gashin wurin bai yi fari ba, zurfin ƙurjin kuma bai zarce fatar ba, amma ya dushe, sai firist ɗin ya kulle shi kwana bakwai.
22 Amma idan ƙurjin ya bazu a fatar jikin, sai firist ya hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, kuturta ce.
23 Amma idan tabon ya tsaya wuri ɗaya, bai bazu ba, tabon miki ke nan, sai firist ya hurta, cewa, shi mutumin tsarkakakke ne.
24 Ko kuma idan mutum ya ƙuna a fatar jiki, naman wurin ƙunar kuwa ya yi tabo jaja-jaja, da fari-fari, ko fari,
25 sai firist ya dudduba shi, in gashin wurin tabo ya zarce fatar, to, kuturta ce ta faso a cikin ƙunar, sai firist ya hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, cutar kuturta ce.
26 Amma idan firist ya dudduba tabon, ya ga gashin tabon bai zama fari ba, zurfin tabon kuma bai zarce fatar ba, amma ya dushe, firist zai kulle shi kwana bakwai.
27 A kan rana ta bakwai, zai sāke dubansa, idan tabon yana bazuwa cikin fatar, sai firist ya hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, kuturta ce.
28 Amma idan tabon ya tsaya a wuri ɗaya, bai bazu a fatar jikin ba, ya kuma dushe, to, kumburi ne na ƙunar, firist zai hurta, cewa, shi mutumin tsarkakakke ne, gama tabon ƙuna ne.
29 Sa’ad da mace ko namiji na da cuta a kai, ko a gemu,
30 sai firist ya dudduba cutar, in ya ga zurfin cutar ya zarce fatar, gashin kuma da yake wurin ya zama rawaya, siriri kuma, firist zai hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, miki ne, ciwon da za a iya ɗauka ne.
31 Amma idan firist ya duba mikin, ya ga zurfinsa bai zarce fatar ba, ba kuma baƙin gashi a ciki, sai firist ya kulle mai miki har kwana bakwai.
32 A rana ta bakwai kuma firist zai duba cutar, idan mikin bai bazu ba, babu kuma rawayan gashi a cikinsa, zurfin mikin kuwa bai zarce fatar ba,
33 zai aske kansa, amma ba zai aske mikin ba, sai firist ya sāke kulle mai mikin har waɗansu kwana bakwai.
34 A rana ta bakwai firist zai dudduba mikin, idan mikin bai bazu ba, zurfinsa kuma bai zarce fatar ba, sai firist ya hurta, cewa, shi mutumin tsarkakakke ne, sai mutumin ya wanke tufafinsa, ya tsarkaka ke nan.
35 Amma idan mikin ya bazu bayan tsarkakewarsa,
36 sai firist ya dudduba shi, idan mikin ya bazu a fatar, ba lalle ne ya nemi rawayan gashi ba, shi mutumin marar tsarki ne.
37 Amma idan a ganinsa mikin bai yaɗu ba, baƙin gashi ya tsiro ya kuma yi tsawo a wurin, mikin ya warke ke nan, mutumin ya tsarkaka, firist kuwa zai hurta, cewa, shi mutumin tsarkakakke ne.
38 Idan a fatar jikin mace ko namiji akwai fararen tabbai,
39 sai firist ya dudduba, idan tabban toka-toka ne, mawanki ne ya faso a fatar, shi tsarkakakke ne.
40 Idan gashin kan mutum ya zube, ya zama mai sanƙo ke nan, amma shi tsattsarka ne.
41 Idan gashin goshin mutum ya zube, ya yi sanƙo ke nan, amma shi tsattsarka ne.
42 Idan a sanƙon ko a gaban goshi akwai tabon cuta jaja-jaja da fari-fari, to, kuturta ce ta faso a sanƙonsa ko gaban goshinsa.
43 Firist kuwa zai dudduba shi, idan an ga kumburin jaja-jaja da fari-fari ne a sanƙon kansa, ko a gabansa kamar alamar kuturta a fata jikinsa,
44 to, kuturu ne shi, marar tsarki. Firist zai hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, cutar kuturta tana kansa.
45 Mai kuturta zai sa yagaggun tufafinsa, ya bar gashin kansa ba gyara, sa’an nan ya rufe leɓensa na sama, ya ta da murya, ya riƙa cewa, “Marar tsarki, marar tsarki.”
46 Muddin yana da cutar, zai zama marar tsarki. Zai zauna shi kaɗai a bayan zango.
47 Idan ana tsammani akwai cutar kuturta a rigar ulu ko ta lilin,
48 ko a tariyar zaren, ko a waɗari, ko a lilin, ko a ulu, ko a cikin fata, ko cikin kowane abu da aka yi da fata,
49 idan cutar ta zama kore-kore, ko jaja-jaja a rigar, ko a fatar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko a kan abin da aka yi da fata, wannan cuta kuturta ce, sai a nuna wa firist.
50 Firist zai dudduba cutar, ya ajiye abin da yake da cutar har kwana bakwai.
51 A rana ta bakwai ɗin zai sāke dudduba cutar, idan cutar ta yaɗu a rigar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko a fatar, komene ne za a yi da fata, wannan cuta muguwar kuturta ce, abin zai zama marar tsarki.
52 Zai ƙone rigar, ko tariyar zaren, ko waɗari na ulu ko na lilin, ko abin da dai aka yi da fata wanda yake da cutar, gama muguwar kuturta ce.
53 Amma idan firist ya dudduba ya ga cutar ba ta yaɗu a rigar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko a abin da aka yi da fata ba,
54 sai firist ya umarta a wanke abin da yake da cutar, ya sāke ajiye shi har kwana bakwai kuma.
55 Firist kuma zai sāke duban abin da yake da cutar bayan da aka wanke shi, idan ya ga launin cutar bai sāke ba, ko da cutar ba ta yaɗu ba, abin ya zama marar tsarki ne nan, sai a ƙone shi da wuta, ko tabon cutar yana cikin abin ne, ko a waje.
56 Amma idan firist ɗin ya duba ya ga tabon ya dushe bayan da aka wanke shi, sai ya kece wurin daga fatar, ko tariyar zaren, ko waɗarin.
57 Idan tabon ya sāke bayyana kuma a rigar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko a kan abin da aka yi da fata, ya yaɗu, sai a ƙone abin da yake da kuturtar.
58 Amma da rigar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko kowane abin da aka yi da fata, wanda cutar ta wanku daga shi sa’ad da aka wanke, sai a sāke wanke shi, ya kuwa zama tsarkakakke ke nan.
59 Wannan ita ce dokar da za a bi a kan cutar kuturtar rigar ulu ko ta lilin, ko cutar kuturta ta tariyar zaren, ko ta waɗarin, ko kuma ta kan kowane abu da aka yi da fata, don a tabbatar tsattsarka ne, ko marar tsarki ne.