Ranar Kafara
1 Sai Ubangiji ya yi magana da Musa bayan rasuwar ‘ya’yan Haruna, maza biyu, sa’ad da suka hura wuta marar tsarki a gaban Ubangiji, suka mutu.
2 Ubangiji kuma ya ce wa Musa, “Faɗa wa ɗan’uwanka Haruna kada ya riƙa shiga Wuri Mafi Tsarki bayan labule ko yaushe, wato, a gaban murfi wanda yake bisa akwatin alkawari, domin kada ya mutu, gama zan bayyana a cikin girgije a kan murfin.
3 Amma sai Haruna ya shiga Wuri Mafi Tsarki bayan da ya kawo ɗan bijimi domin yin hadaya don zunubi, da rago don yin hadaya ta ƙonawa.”
4 Sa’an nan Ubangiji ya ba Musa ka’idodin nan. Sai Haruna ya sa zilaika ta lilin tsattsarka, ya ɗaura mukuru na lilin, ya yi ɗamara da abin ɗamara na lilin, ya naɗa rawani na lilin, waɗannan su ne tsattsarkar sutura. Zai yi wanka da ruwa, sa’an nan ya sa su.
5 Zai karɓi bunsuru biyu daga taron jama’ar Isra’ila domin yin hadaya don zunubi, da rago ɗaya don yin hadaya ta ƙonawa.
6 Haruna zai miƙa bijimi na yin hadaya don zunubi saboda kansa. Zai yi kafara don kansa da gidansa.
7 Zai kuma kawo bunsuran nan biyu a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada.
8 Sa’an nan ya jefa kuri’a kan bunsuran nan biyu. Kuri’a ɗaya don Ubangiji, ɗaya kuma domin Azazel.
9 A wanda kuri’ar Ubangiji ta faɗa a kansa, sai Haruna ya miƙa shi hadaya don zunubi ga Ubangiji.
10 Amma a wanda kuri’ar Azazel ta faɗa a kansa, sai a miƙa shi da rai a gaban Ubangiji, a yi kafara da shi, a kora shi can cikin jeji domin Azazel.
11 Haruna kuma zai miƙa bijimi na yin hadaya don zunubin kansa, ya yi kafara don kansa da gidansa. Zai yanka bijimi na yin hadaya don zunubin kansa.
12 Zai ɗauki faranti cike da garwashin wuta daga bagaden da yake a gaban Ubangiji, ya kuma cika hannunsa biyu da turare mai ƙanshi, ya shigar da shi bayan labulen.
13 Zai zuba turaren a wuta a gaban Ubangiji, domin hayaƙi ya tunnuke ya rufe murfi wanda yake a kan akwatin alkawari, don kada ya mutu.
14 Sai ya ɗibi jinin bijimin, ya yayyafa da yatsansa a gefen gabas na murfin, zai kuma yayyafa jinin a gaban murfin sau bakwai.
15 Sai kuma ya yanka bunsuru na yin hadaya don zunubin jama’ar ya shigar da jinin bayan labulen. Zai sa jinin kamar yadda ya yi da jinin bijimin, ya yayyafa shi a kan murfin, da gaban murfin.
16 Da haka zai yi kafara domin Wuri Mai Tsarki saboda ƙazantar mutanen Isra’ila, da laifofinsu, da dukan zunubansu. Haka kuma zai yi wa alfarwa ta sujada, wadda take a wurinsu, a tsakiyar ƙazantarsu.
17 Kada kowa ya kasance cikin alfarwar sujada lokacin da Haruna ya shiga Wuri Mafi Tsarki domin ya yi kafara don kansa, da gidansa, da dukan taron jama’ar Isra’ila, sai lokacin da ya fita.
18 Sa’an nan zai fita ya tafi wurin bagade wanda yake gaban Ubangiji don ya yi kafara dominsa. Zai ɗibi jinin bijimin da na bunsurun, ya shafa wa zankayen bagaden a kewaye.
19 Zai kuma yayyafa jinin da yatsansa har sau bakwai a kan bagaden, ya tsabtace shi, ya tsarkake shi daga ƙazantar jama’ar Isra’ila.
20 A sa’ad da ya gama yin kafara don Wuri Mai Tsarki, da alfarwa ta sujada, da bagaden, sai ya miƙa bunsuru ɗin mai rai.
21 Haruna zai ɗibiya hannuwansa duka biyu a kan kan bunsurun mai rai, ya hurta muguntar Isra’ilawa duka a bisa bunsurun, da dukan laifofinsu, da dukan zunubansu. Zai ɗibiya su a kan kan bunsurun, ya kora shi cikin jeji ta hannun wanda aka shirya zai kora shi.
22 Bunsurun zai ɗauki muguntarsu duka a kansa zuwa jeji. Mutumin kuwa zai sake shi can a jeji.
23 Sa’an nan Haruna zai shiga alfarwa ta sujada, ya tuɓe tufafinsa na lilin waɗanda ya sa sa’ad da ya shiga Wuri Mafi Tsarki, ya ajiye su a nan.
24 Zai kuma yi wanka da ruwa a wuri mai tsarki, sa’an nan ya sa tufafinsa, ya je, ya miƙa hadayarsa ta ƙonawa, da hadaya ta ƙonawa don jama’a, domin ya yi kafara don kansa da jama’a.
25 Zai ƙone kitsen hadaya don zunubi a bisa bagaden.
26 Shi wanda ya kore bunsurun Azazel, sai ya wanke tufafinsa ya yi wanka da ruwa, bayan haka yana iya komawa cikin zango.
27 Bijimin da bunsurun da aka yi hadaya don zunubi da su, waɗanda aka yi kafara da jininsu a Wuri Mafi Tsarki, sai a kai su bayan zangon, a ƙone fatunsu, da namansu, da tarosonsu.
28 Shi wanda ya ƙone su, zai wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, bayan haka ya iya komawa zangon.
29 Waɗannan za su zama farillai a gare su har abada. A rana ta goma ga watan bakwai za su ƙasƙantar da kansu, ba za su yi kowane irin aiki ba, ko ɗan ƙasa, ko baƙon da yake cikinsu.
30 Gama a wannan rana za a yi kafara dominsu, domin a tsarkake su daga dukan zunubansu, su zama tsarkakakku a gaban Ubangiji.
31 Wannan rana muhimmiya ce don hutawa a gare su. Za su ƙasƙantar da kansu, wannan farilla ce har abada.
32 Firist kuma da aka naɗa ya zama firist a madadin mahaifinsa, zai yi kafara yana saye da tufafin lilin masu tsarki.
33 Zai yi kafara domin Wuri Mai Tsarki, da alfarwa ta sujada, da bagaden. Sa’an nan kuma ya yi kafara domin firistocin, da dukan taron jama’ar.
34 Wannan zai zama dawwamammiyar farilla a gare su. Za a riƙa yin kafara domin jama’ar Isra’ila saboda zunubansu duka sau ɗaya a shekara.
Sai Musa ya aikata kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.