Hadaya ta Salama
1 Idan mutum zai kawo hadayarsa ta salama daga garken shanu, sai ya kawo mace ko namiji marar lahani ga Ubangiji.
2 Zai ɗibiya hannunsa a kan kan hadayarsa, ya yanka a bakin ƙofar alfarwa ta sujada. ‘Ya’yan Haruna maza kuwa, firistoci, za su yayyafa wa bagaden jinin kewaye da shi.
3 Daga hadaya ta salama sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji, wato, kitsen da yake rufe da kayan ciki, da wanda yake bisansa,
4 da ƙoda biyu, da kitsen da yake bisansu a wajen kwiɓi, da matsarmamar da zai cire tare ƙodojin.
5 ‘Ya’yan Haruna, maza kuwa, za su ƙone su tare da hadayar ƙonawa da take bisa itacen da yake cikin wutar bagade, hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
6 Idan kuwa hadayarsa ta salama ga Ubangiji daga garken tumaki, ko na awaki ce, sai ya ba da dabbar, mace ko namiji, marar lahani.
7 Idan ɗan rago ne ya bayar don hadaya, sai ya miƙa shi a gaban Ubangiji.
8 Zai ɗibiya hannunsa a kan kan hadayarsa, ya yanka a gaban alfarwa ta sujada. ‘Ya’yan Haruna, maza kuwa, za su yayyafa wa bagaden jinin kewaye da shi.
9 Daga cikin hadaya ta salama sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji, wato, kitsensa da wutsiyarsa duka mai kitse. Zai yanke ta gab da ƙashin gadon baya, da kitsen da ya rufe kayan ciki kuwa, da wanda yake bisansa,
10 da ƙoda biyu, da kitsen da yake bisansu a wajen kwiɓi, da matsarmamar da zai cire tare da ƙodojin.
11 Firist kuwa zai ƙone su a bisa bagaden kamar hadayar abincin da akan ƙone da wuta ga Ubangiji.
12 Idan ya kawo akuya don hadayarsa, sai ya miƙa ta a gaban Ubangiji.
13 Zai ɗibiya hannunsa a bisa kanta, ya yanka ta a gaban alfarwa ta sujada. ‘Ya’yan Haruna, maza, za su yayyafa wa bagaden jinin kewaye da shi.
14 Sa’an nan mai hadayar zai ba da kitsen da yake rufe da kayan cikin, da wanda yake bisansa,
15 da ƙodoji biyu, da kitsen da yake bisansu wajen kwiɓi, da matsarmama don a miƙa su hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.
16 Firist kuwa zai ƙone su a bisa bagaden kamar hadayar abincin da akan ƙone don ya yi ƙanshi mai daɗi. Dukan kitse na Ubangiji ne.
17 Ba za a ci kitse ko jinin ba a wuraren zamanku. Wannan doka madawwamiya ce.