NEH 1

Addu’ar Nehemiya domin Urushalima

1 Labarin Nehemiya ɗan Hakaliya ke nan. Ya zama fa a watan Kisle a shekara ta ashirin, sa’ad da ni Nehemiya nake a fādar Shushan, wato alkarya,

2 sai Hanani, ɗaya daga cikin ‘yan’uwana, ya zo tare da waɗansu mutanen Yahuza. Na kuwa tambaye shi labarin Yahudawan da suka tsira, suka koma daga zaman talala, da labarin Urushalima.

3 Sai suka ce mini, “Waɗanda suka tsira, suka koma daga zaman talala, da suke can lardin, suna cikin wahala ƙwarai, suna kuma shan kunya. Garun Urushalima kuma ya rushe, ƙofofi sun ƙone.”

4 Da na ji wannan labari, sai na zauna, na yi kuka. Na yi kwanaki ina baƙin ciki, na yi ta azumi da addu’a a gaban Allah na Sama.

5 Na ce, “Ya Ubangiji Allah na Sama, Allah mai girma, mai banrazana, mai cika alkawari, mai nuna madawwamiyar ƙauna ga waɗanda suke ƙaunarka, wato masu kiyaye umarnanka,

6 ina roƙonka ka kasa kunne, ka kuma buɗe idanunka, ka ji addu’ar bawanka, wadda nake yi a gabanka dare da rana saboda bayinka, mutanen Isra’ila. Ina hurta zunubanmu, mu mutanen Isra’ila, da muka yi maka. Ni da gidan ubana mun yi zunubi.

7 Mun kangare maka, ba mu kiyaye umarnai, da dokoki, da ka’idodi waɗanda ka ba bawanka Musa ba.

8 Ka tuna da maganar da ka umarci bawanka Musa cewa, ‘Idan kun yi rashin aminci, zan warwatsa ku cikin al’ummai.

9 Amma idan kun juyo wurina, kun kiyaye umarnaina, kun aikata su, ko da yake an warsatsar da ku can nesa, zan tattaro ku, in kawo ku wurin da na zaɓa domin in sa sunana ya kahu a wurin.’

10 “Su bayinka ne, mutanenka ne kuma, waɗanda ka fansa da ikonka.

11 Ya Ubangiji, ka kasa kunne ga addu’ar bawanka, da addu’o’in bayinka, waɗanda suke jin daɗin girmama sunanka. Ka ba bawanka nasara yau ka sa ya sami tagomashi a gaban mutumin nan.”