Addu’ar Neman Hamɓare Mugaye
1 Ya Ubangiji, me ya sa kake can nesa?
Me ya sa ka ɓoye kanka a lokacin wahala?
2 Mugaye suna fāriya, suna kuma tsananta wa matalauta,
Ɗana tarkon da suka yi yă kama su.
3 Mugun mutum yana fāriya da mugayen manufofinsa,
Mai haɗama yakan zagi Ubangiji ya kuma ƙi shi.
4 Mugun mutum da girmankansa yana cewa, “Ba Allah!”
Wannan ne abin da mugu yake tunani.
5 Yakan yi nasara a dukan abin da yake yi.
Ba zai fahimci hukuncin Allah ba,
Yana yi wa abokan gābansa duban raini.
6 Yana ce wa kansa “Ba zan taɓa fāɗuwa ba,
Ba zan taɓa shan wahala ba.”
7 Maganganunsa suna cike da zage-zage, da ƙarairayi, da barazana,
Yana da saurin faɗar maganganun ƙiyayya da na mugunta.
8 Yakan ɓuya cikin ƙauyuka,
Yă jira a can har yă kashe marasa laifi.
Yakan yi sanɗa, ya kama kāsassu,
9 Yakan jira a inda ya ɓuya kamar zaki.
Yakan kwanta yana fakon wanda zai kama,
Har ya kama shi da tarkonsa ya tafi da shi!
10 Yakan ragargaza kāsasshe,
Yă gwada masa ƙarfi, yă ci nasara a kansa.
11 Mugun mutum yakan ce wa kansa, “Allah bai kula ba!
Ya rufe idonsa, ba zai taɓa ganina ba.”
12 Ya Ubangiji, ka zo ka cece ni!
Kada ka manta da waɗanda ake zaluntarsu, ya Allah!
13 Yaya mugun zai riƙa raina Allah,
Har yă riƙa ce wa kansa, “Ba zai hukunta ni ba”?
14 Amma kana gani, kana kuma lura da masu shan wuya, da masu ɓacin rai,
Koyaushe kuma a shirye kake ka yi taimako.
Mutum wanda ba shi da mai taimako yakan danka kansa gare ka,
Gama kullum kakan taimaki masu bukata.
15 Ka karya ikon mugaye, masu mugunta,
Ka hukunta su saboda muguntarsu,
Har hukuncinsu ya cika sarai.
16 Ubangiji sarki ne har abada abadin,
Arna kuma za su ɓace daga ƙasarsa.
17 Za ka saurara ga addu’o’in masu kaɗaici, ya Ubangiji,
Za ka ba su ƙarfin hali.
18 Za ka ji koke-koken waɗanda ake zalunta da na marayu,
Ka yi shari’ar da za su ji daɗi,
Domin kada ‘yan adam su ƙara haddasa wata razana.